Chapter 10
Chapter 10
ahalina babu abinda bazanyi ba,kowa Cike da mamaki take dubana sukuwa samarin tsoro na ne yashigesu. Tambaya na shugaban garejin yayi ruwan nawane?nace jakar leda uku CE. Nan kuwa yaciro dari biyar ya bani,sannan yace bread na nawa sukaci?bashi amsa nayi da cewa da bread din hamsin da rabi sannan ai ba yau sukafara mata haka. Karshe dai Sai da mukabar gareji da Naira dubu Daya da dari uku,sannan nace"Babu Wanda ya Isa yahanamu kawo talla garejin. Daukar bucket Dina nayi muka tafi,a ranar dai nayi dambe Yafi a kirga,Kuma duk akan bread da ruwa,masu yima Aunty Saudah rainin wayo sai da na Rama Mata. Abin mamaki mun siye bread din nan tass Babu ko lankare, murna sosai Aunty Saudah tayi. Haka kuwa muka nufi hanyar gida muna Cike da farin ciki,a hanya muka hadu da wani wan baban mu akan mashin dinsa Sabo fil,harara yabimu dashi Yana cewa shegu 'yayan Allah shirya masu kama da almajirai,Baku da aiki sai gantalin talla. Juyowa nayi nace"Kaine dai babban almajiri Mai yawon maula,Kuma ai da sauki mu gumummu muke ci,wasu kuwa gumin haramun suke ci. Ashe ramawar Nan danayi ya Sosa masa rai Aiko Nan yafara tsiya,kome yafada na bashi martani a karshe dai tsaki naja mai tare da tofar da miyau muka wuce. Ni ban Sani ba Ashe hakan ya bata masa Rai sosai. Aunty Saudah kuwa tsiya tadinga mun a hanya akan nadena rashin kunya,dukar da kai nayi kamar gaske nace toh Aunty Saudah nadena. Tayi farin ciki sosai da amsar da nabata,wato nadena. Gida muka Shiga Cike da farin ciki na fada jikin Ammi da Abba nace"Ammi Abba yau munyi ciniki Sosai,domin gabadaya aka cinye,murna sukayi sosai kamar su goyamu,tuwon dawar da Ammi tayi da miyar kukan da ko isashshen magi baiji ba muka fara ci Cike dajin yunwa. Ammi kuwa tasamu tayi tana kallon mu tana Murmushi Cike da kaunar mu a ranta,shikuwa Abba daki yashiga. Langa-langar kofan mu aka bugo da karfi Wanda yasamu zabura gabadaya,baba Ayuba ne yashigo Yana masifa,ganina yasashi yowa inda nake direct. Nikuwa ganin haka yasa na Miki nayi hanyar bayin mu,ai kuwa baba tsalha ya biyo baya na shima a gunen , da yake wajen da santsi sai na zille nayi gefe guda. Yana kuwa karisowa wajen santsin jiake timmmm baba tsalha yafadi,Kara yasaka tare da fadin"wayyo Allah na kunguru na. Nikuwa mezanyi Banda dariya,dariya nake sosai harda rike Cike,Cike da bacin Rai yadago Yana dubana. Abba ne yakariso cikin Sauri Yana fadin "Subhanallah yaya Ayuba meyasa Meka?cikin Sauri Abba ya kamashi ya dagashi,Nuno ni da yatsa yayi yace"wancan tsinanniyar yarinyar taka Mai Kama da aljanu nan yashiga bawa Abba labarin komai. Cike da bacin Rai Abba yadago Yana duba na yace"Mama haka kayi? Girgiza Kai nayi cikin Sauri nace"A'ah Abba kawai don ya tsaneni ne shiyasa zaice haka,gaishe kawai nayi yahau zagina don yaga bankula shi ba shine yabiyo ta nan. Gabadaya bude mouth baba Ayuba ya bude Yana kallo na,Yana mamakin wani irin hatsabibanci ne dani haka? Shiru yayi batare da yayi magana ba ya fita daga gidan,karyayyen langa-langar mu yabuga yafita, Abba ne yadawo da dubanshi kaina yace"zonan mamana,tsakanin ki da Allah meyafaru?Jin ta tambayi tsakani na da Allah yasa nafadi gasky,Nan ko Abba ya Shiga yimun fada inda yake Shiga banan yake fita ba,Ammi ma haka Bayan sun gama suka dasa nasiha akan narage tsiwa da rashin kunya. Amsa kawai na Basu da toh sannan na nemi yafiyarsu,Sam banson bacin ran iyayena a gefe guda kuwa ta shiga tanan ne tafita ta can tabi iskaaaaa. Washe gari kuwa muka sake daukar tallan bread din duk idan muka fita sai mun siye tasss,dalilin haka kuwa Allah ya albarkaci Dan ribar dubu dayan da muke samu,ganin haka yasa Abba yasamu a islamiya,ajinmu Daya da Aunty Saudah tunda inada kokari sosai,kwana na biyu a islamiyar sunana ya zagaya makarantar,a dalilin na fasa ma wani yaro kai yakawomun wargi,kullum sai iyayen yara sunkawo karana wajen headmaster,ganin haka yasa headmaster ya sanar ma da Abba,wanna Karan fushi Abba ya dauka sosai a kaina domin har zaneni yayi yace Kuma zai cire ni a makarantar. Hakuri Nashiga bashi,sannan nayi mai alkawarin bazan Kara ba,tsaki yaja yace"keda Kika Saba da dama tuban mazuru. Ita dai Ammi ko me akayi sai dai Ido. ~After 3 month~ Mun cigaba da zuwa islamiya Alhamdulillah Allah nata rufa Mana asiri,sannan a gefe guda bamu dena zuwa tallah ba. Ranar sati na shirya ni kadai na tafi islamiya da yake Aunty Saudah bataman tabi kanwar Ammi Agadez domin Ammi 'yar agadez ne can wani kauye,namanta sunan shi,ita Kuma tana aure a cikin garin nijar. Latti nayi,da yake malam shafi'u azzalumi ne yasan bansan duka,Aiko nan yamun dukan tsiya,kuka nayi sosai tare da duban hannu na yanda ya fashe.Don haka na dauki alwashi da ramuwa da *daukan fansa* a dalilin dukan wallahi sai na Rama. Washe gari kuwa Bayan antashi islamiya na dai-dai ci dai-dai lungun da malam shafi'u ke wucewa na zuzzuba kososhi tunda ga farkon lungun har tsakiya,sannan nasu wani waje na boye,hannu na da katon icce. Aiko bayan antashi malam shafi'u ya shigo lungun,kunnensa sanye da earpeace bai ankare ba yaji mashin tafara selow slow slow alamun Babu iska,sauka yayi tare da Jan tsaki,Yana duban tayar mashin dinsa Bai ankare ba yaji saukan sanda a bayansa say kwala masa,wani irin ihu yasake tare da gantsarewa,cikin bacin Rai ya juyo Cike da mamaki da takai ci yake duba na,nikuwa hade rai nayi kamar wata babba ku Kuma wani sa'a na nace"ai dama ramuwar gayya tafi ta gayya zafi Ina magana Ina jujjuya sandar da take hannu na. Cikin bacin rai yanufo inda nake,Aiko na hau tsalle tsalle kamar 'yar Cali-cali Allah kuwa yabani nasara nashige ta osin shi,abin fitsarin shi na Kama na murdeeee,duk da a lokacin bansan menene ita ba,kawai hannu na ne yakai kanta. Kyalkyalewa da dariya su Fauzi sukayi,khadee tace"lallai Shakeerah kin bar history a unguwar ku. Murmushi Shakeerah tayi tace"hmmmm ku dai Bari,in takaicemu ku tunda na Kama abin fitsarin shi na murde sai da yayi ihun wahala nasake shi,sannan na dauki icce na kwala ma goshin sa Aiko atake anan yafashe goshin yafara fitar da jini. Nesa dashi nayi sannan na nuna masa hannuna da ya fasa da dorina nace"kaga wannan somun tabu ne,Ina Gama fadar haka na arta a 360 na bar wajen nayi gida. Washegari na dauki tallar pure water da bread dina natafi wajen Sha daya na dawo Bayan nayi ciniki ansaye tasss. Tunda nashigo gidan daga Ammi har Abba babu wanda ya kalleni daka gansuu kasan ransu a bace yake,Cike da farin ciki na nufi jikin Ammi na fada kamar yarda na Saba nace Ammi kin.........ko karisawa banyi ba naji saukar Mari,Wanda yasani gigicewa duk da bansan Wanda ya mareni tsakanin Ammi da Abba ba to nafi kyautata zaton Ammi saboda shi Abba mutum ne Mai sanyi kamar yanda Ammi take,babban cinsu Ammi na duka Abba Kuma ba yayi. Ihu nake Ina fadin na Shiga uku,sanda Ammi ta dauko tace"au don ma bandake kiba shine kike kokarin tara mun jama'a?iccen miyar tsanya ta dauko zata zabga mun tana cewa"Bari inmiki Mai dalilin inyaso kyayi kukan da hujja. Zumbur na mike nanufi Bayan Abba ina cewa"A'ah Ammi kuyahakuri wallahi bazan sake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30