Chapter 4
Chapter 4
daba,Jakadiya tace"Amma fulani meyasa baki Kira waya ba anzo ankoya Masa hankali? Fulani Tace kada kidamu ko yanzu wannan yarinyar ai tayi gaba Koda zaiyi zai tuna da abinda yafaru,Jakadiya tace haka ne. Duba na fulani tayi tace 'yammata yaya sunanki? Bata amsa nayi da Maryam Amma anfi kirana da Shakeerah,wow Masha Allah tafada,Cike da mamaki na dago ina kallonta,ba komai yabani mamaki ba illa wow dinda tace nikam da bansan meaning dinshi ba. Tambayata tayi nabata labarina,nan kuwa na zayya ne mata komai,abubuwa da dama dariya take nan tadubi Jakadiya tace taje tacema Sarkin gida a shirye motoci uku xataje unguwa. Ba'a dauki lokaci ba muka shirya nidai Ina rungume da bucket din pure water da farantin bread. Shiga motocin mukayi Wanda najini tamkar nashiga cikin jirgin sama tsaban dadin danaji,a haka nadinga musu kwantace har muka Kai kofar gidan mu,ya wanci 'yan layinmu duk sunfito ganin motoci da manya manya a hankali suka tsaya aka budema fulani murfin motan,nima aka budemun. Tunda akaga amfito Dani daga cikin motar 'yan unguwar mu sukafara gulma kala-kala. Fulani ta dubeni tana tambayata gidan mu,nuna mata gidan nayi,jakadiyar ta da kuyangi uku muka shiga sauran kunyangin da dogarai suka tsaya a waje. Tafe suke da carpet dinsu da Sauri Ammi tatashi ganin antaso keyata gashi daga gani masu kudi ne. Murmushi ne a fuskan fulani,sannu da zuwa Ammi tafara mata sannan tashiga dasu daki don wajen babu wajen fakewa Rana. Dakinmu ta kaita,Wanda yake shimfide da wani tsohon dadduma sai dai tsafta yasa yanajinshi fesss. Carpet Jakadiya tayi kokarin shimfidawa sai fulani ta hanata Zama tayi akasa suka fara gaisawa da Ammi cike da fargaba. Fulani ta dubeta tace"kece mahaifiyar wannan yarinyar Koh?Ammi cike da fargaba Ammi tace"Eah nice! Da fatan dai bawani lefi tayi ba? Girgiza Kai Ammi tayi Nan tasanar da ita duk abinda yafaru sannan tace idan Babu damuwa tana son ganin Abba. Nan Ammi tafita tasamu Dan makota yaje kiransa a wajen bread. Basu dau wani time ba suka shigo shima da kaganshi kasan Cike da mamaki yake a tsakar gida Ammi ta tareshi tace Abban su yau Shakeerah ta nemo Mana magana. Shiru Abba yayi tare da sallama ya Shiga,su Jakadiya fulani ta kalla alamun su bamu waje,fita sukayi tsakar gida,nan suka gaisa cikin mutumci da Abba. Tambayar shi tayi sana'arshi yace mata bread ne,tace to yau yarinyar ku ta temakeni da alamu daga gidan tarbiya tafito tunda har tasan darajar tsoho,ganin haka yasa na biyota don ganin iyayen ta. A tare suka sauke nannauyan ajiyar zuciya. Fulani ta cigaba da cewa idan Babu damuwa,zanso in temaka muku da muhalli sannan Kai nabaka jari mai karfi. Jin kalaman fulani mukayi kamar a mafarki,cikin rawar baki Abba yace Ni...n...I...diin..? Daga Masa kai fulani tayi ai a take anan suka fara godiya saboda tsananin murna. Nan takira ma'ajinta Mai kula da harkan komai tace masa tanaso a dubo mata gida mai kyau Mai 3 bedrooms,Kuma yazama dakwai komai da komai da ake bukata na muhalli. Amsa mata yayi da toh,Aiko cikin awa biyu yakirata yace ansamu,tambayar shi tayi a Ina?yace a kwangila. A lokacin Ammi tagama alqlen gwangwani rai-rai da dakaken yaji tafarnuwa,nan akazuba ma fulani da da kuyanginta da fadawa gaba daya,mukuma ko oho,tsabar yunwa tasa mun manta da yunwa,sosai sukaji dadin alalen. Shakeerah ta dubi su Fauzi tace"In takaice muku fulani itace dalilin arzikinmu. Munje munga sabon gidanmu,gaskiya yayi kyau sosai nida Aunty Saudah a daki guda,daki daya na Ammi dake kallon namu sai daya na Abba da yake da kofa ta waje,duka dakuna biyu Italian bed ne,Daya Kuma Royal shine na dakin Abba,dakuna ne manya² Wanda da safayan 1-1 sitter sai na Abba ne da 1-2 sitter da bangaren dining Falon Kuma kujeru ne hadaddu golden saikace glass Sunyi kyau sosai. Jali tabawa Abba na miliyan Daya sannan ta hadAshi da direban ta suka fara sana'ar sai da motoci. Nan kuwa 'yan uwan Abba suka sake tsanar sa suna yawon cewa yankan Kai yafara,watarana muna zaune da Ammi shi Abba bayanan sun fita da direban fulani sunje kano dauko wata mota. Wani yaro ne yayi sallama ya shigo,amsawa nayi na fita tambayata yayi Wai ance Nan ne gidan wai malam muhammadu? Na'amsa da Eah nan ne wake nemanshi? yaron yacemin wasu maza ne su biyu a waje,cema yaron nayi muje nagansu tare muka fita na bude gate din gidan,Cike da mamaki nake dubansu baba Ayuba ne da baba sani,duk yayyen baban mu ne. Ganina yasasu sakin murmushi gaba dayansu,Nima murmushin naayar musu Ina cewa lahh kune?ku shigo,da to suka amsa ko wanne yana kokarin fara shigowa ganin zasu bangaje ni yasani matsawa suka Shiga,gaba daya bin gidan suke da kallo,wani kolulun bakin ciki baba Ayuba ya hadiye har muka shiga falon,daburcewa sukayi ganin kujerun,Cike da fara'a Ammi ta tarbesu Zama sukayi akan kujerun duk da sunsa ba gani a gidan chairmomin local government,gwanda ma baba sani idan yaso kirki yanayi Zama sukayi,Nikuma nashiga kitchen da kyar na iya bude firij saboda kauyan cina yayi yawa lemu na dauko musu da ruwa na Basu. Nan baba Ayuba ke tambayar Ammi Abba Tace Aiko bayanan,sun tafi kano,wani takaicine ya lullubesu baba sani kuwa har Yana kwarewa yace kano Kuma? Baba Ayuba yace oh rayuwa yanzu muhammadu ne da wannan gidan?harda zuwa kano? Idan natuna sanda yake kwasan masai da bola abin mamaki yake bani. Magana suka gasama Ammi itama Kuma tagani,Murmushi nayi nace wallahi kuwa baba gashi yanzu a dalilin katsalan dan dina muka shiga daukar nan,yaran da ake tsine musu idan ba iyayensu ke tsine musu ba ai abin sai kaga Yana tafiya yanda akeso,yau da hjy 'yar mai goro nanan nasan da zatayi alfahari(wato mahaifiyar Abba) harara baba Ayuba yasakin min yace Mai Hali dai Sam baya canza Hali to yanzu dake nayi magana?Nima hararar na wurga mai nace maganar mahaifina fa kakeyi shiyasa nasa baki. Kwafa baba sani yayi yace ai yanzu Dole muhammadu yayi aure tunda arziki yasamu kaga ni saina samo Mai bazawara. Daka tsalle nayi kamar nice za'ama kishiya nace wallahi bazai yuwuba Kuma Abba bazai dauki shawarar na ba,galala suka saki mouth suna kallo na,Ammi tace Shakeerah tashi kiwuce ciki,da toh na amsa mata na mike Suma mikewar sukayi daganan suka fara Dora ashar,inaso in rama saboda jikina har tsuma yake sai dai Ammi ta hanani. _I need ur comment and sharhi_ Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami🖋️Yafi takobi 🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ *Littafin diamond ladies (Daukar fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari biyu#200 katin waya ta wannan number 08060719719,sannan a nemeni ta wannan number 08060719719 sai nayi adding din mutum a group a group din diamond ladies (Daukar fansa),Wanda suka biya kadai zan zira a ciki......kushiga daga ciki don Jin labari Mai darasi,nishadi,tausayi,fadakarwa,ilimantarwa da jarumta.Nagode.* Bismillahi-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai* Page:7️⃣&8️⃣🖊️ __________Bayan sunje lectures Sai wajen karfe shida suka dawo,sai da suka wuje restaurant sukaci abinci sannan sannan sukayo take away
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30