Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Deejamah Book 1 Complete Hausa Novel 1,284 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dingisa kafa daka ganta bata cikin wahala sai dai daga gani rigimammiya ce,wani ne ya taho da Sauri ya bangaje ta,Aiko tsohuwar nan ta baje a kasa,babu Wanda yamasa magana nan kuwa yafara magana Yana karkata mouth alamu dai Dan daba ne ku tsofaffin nan 'yan iska ne taya Zaki shigo kasuwar mu wallahi kinci darajar ke tsohuwa ce da nayi Miki bakin aiki,cikin tsiwa na taho na dagata ina cewa sannu kaka,amsawa tayi tanamun godiya. Zagina yafara Yana cewa Ni ajawon inace don uwata?banza na masa ganin hakan yasa yajiyo gabana ya dauke ni da mari dafe kunci na nayi Cike da azaba don naji zafi sosai kada kumanta a lokacin 12years gareni bansan sanda nayi kukan kura na dauki bucket din pure water Dina ba na buga masa, dai-dai lokacin wani Dan sanda yazo wucewa Aiko ya kariso Yana tambayar neje faruwa?Nan kuwa tsohuwan nan ta zayyane mai komai tana kuka,albarka yasamun sosai sannan yace nakai tsohuwar gida,tab nida bansanta ba daga haduwa taya zansan gidanta,a gaskiya tacema Dan adai-dai tan da ya daukemu take,tayimai kwantancen layin Aiko nan aka kaimu. Wani dankareren gida mukaje Wanda tunda nake bantaba ganin gida mai kyau da haduwa irin gidan ba don haka nema cikin zumudi nabita gidan,gani nayi ma'aikata kowa na ya duke a kasa Yana kwasan gaisuwa tsoro ne yakamani bansan sanda na diddilo idanuwa waje ba Fadi nake " _innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir-rahmanir-raheem_ yau nakawo kaina mahallaka garin temako,wani falo muka isa babba mai cike da Kayan alatu wallahi kamar ba gidan mutane ba Zama tayi a wani kujeran one sitter tare da dannna wani kararrawa,can sai ga masu aiki sun Kai goma suka taho ajere,kirari suka fara mata tare da zubewa suna kwasan gaisuwa,Murmushi tayi ta dubi daya daga cikinsu tace"Jakadiya!wacce akakira da jakadiyar na kalla babban macece sanna tafi sauran shekaru kayanta daban ne Kuma duk cikansu suna jinsu neat. Murmushi tayi jakadiyar tare da karisowa tana fadin"gaisuwa nake uwar dakina uwar gida sarautar mata gani gareki fulani. Murmushi tsohuwan nan takuma tace"Uhm kuntashi hala baku ganni ba? Eah wallahi fulani tunda banganki ba nace yanzu haka kinje zaga gari ne kamar yanda Kika Saba. Murmushi tayi tace"Aikam nan take Basu labarina tanuna ni sannar ta sanar masu da duk abinda yafaru,duk cikansu kallo na suke Cike da mamaki da yanda nayi fada da Dan daba,Jakadiya tace"Amma fulani meyasa baki Kira waya ba anzo ankoya Masa hankali? Fulani Tace kada kidamu ko yanzu wannan yarinyar ai tayi gaba Koda zaiyi zai tuna da abinda yafaru,Jakadiya tace haka ne. Duba na fulani tayi tace 'yammata yaya sunanki? Bata amsa nayi da Maryam Amma anfi kirana da Shakeerah,wow Masha Allah tafada,Cike da mamaki na dago ina kallonta,ba komai yabani mamaki ba illa wow dinda tace nikam da bansan meaning dinshi ba. Tambayata tayi nabata labarina,nan kuwa na zayya ne mata komai,abubuwa da dama dariya take nan tadubi Jakadiya tace taje tacema Sarkin gida a shirye motoci uku xataje unguwa. Ba'a dauki lokaci ba muka shirya nidai Ina rungume da bucket din pure water da farantin bread. Shiga motocin mukayi Wanda najini tamkar nashiga cikin jirgin sama tsaban dadin danaji,a haka nadinga musu kwantace har muka Kai kofar gidan mu,ya wanci 'yan layinmu duk sunfito ganin motoci da manya manya a hankali suka tsaya aka budema fulani murfin motan,nima aka budemun. Tunda akaga amfito Dani daga cikin motar 'yan unguwar mu sukafara gulma kala-kala. Fulani ta dubeni tana tambayata gidan mu,nuna mata gidan nayi,jakadiyar ta da kuyangi uku muka shiga sauran kunyangin da dogarai suka tsaya a waje. Tafe suke da carpet dinsu da Sauri Ammi tatashi ganin antaso keyata gashi daga gani masu kudi ne. Murmushi ne a fuskan fulani,sannu da zuwa Ammi tafara mata sannan tashiga dasu daki don wajen babu wajen fakewa Rana. Dakinmu ta kaita,Wanda yake shimfide da wani tsohon dadduma sai dai tsafta yasa yanajinshi fesss. Carpet Jakadiya tayi kokarin shimfidawa sai fulani ta hanata Zama tayi akasa suka fara gaisawa da Ammi cike da fargaba. Fulani ta dubeta tace"kece mahaifiyar wannan yarinyar Koh?Ammi cike da fargaba Ammi tace"Eah nice! Da fatan dai bawani lefi tayi ba? Girgiza Kai Ammi tayi Nan tasanar da ita duk abinda yafaru sannan tace idan Babu damuwa tana son ganin Abba. Nan Ammi tafita tasamu Dan makota yaje kiransa a wajen bread. Basu dau wani time ba suka shigo shima da kaganshi kasan Cike da mamaki yake a tsakar gida Ammi ta tareshi tace Abban su yau Shakeerah ta nemo Mana magana. Shiru Abba yayi tare da sallama ya Shiga,su Jakadiya fulani ta kalla alamun su bamu waje,fita sukayi tsakar gida,nan suka gaisa cikin mutumci da Abba. Tambayar shi tayi sana'arshi yace mata bread ne,tace to yau yarinyar ku ta temakeni da alamu daga gidan tarbiya tafito tunda har tasan darajar tsoho,ganin haka yasa na biyota don ganin iyayen ta. A tare suka sauke nannauyan ajiyar zuciya. Fulani ta cigaba da cewa idan Babu damuwa,zanso in temaka muku da muhalli sannan Kai nabaka jari mai karfi. Jin kalaman fulani mukayi kamar a mafarki,cikin rawar baki Abba yace Ni...n...I...diin..? Daga Masa kai fulani tayi ai a take anan suka fara godiya saboda tsananin murna. Nan takira ma'ajinta Mai kula da harkan komai tace masa tanaso a dubo mata gida mai kyau Mai 3 bedrooms,Kuma yazama dakwai komai da komai da ake bukata na muhalli. Amsa mata yayi da toh,Aiko cikin awa biyu yakirata yace ansamu,tambayar shi tayi a Ina?yace a kwangila. A lokacin Ammi tagama alqlen gwangwani rai-rai da dakaken yaji tafarnuwa,nan akazuba ma fulani da da kuyanginta da fadawa gaba daya,mukuma ko oho,tsabar yunwa tasa mun manta da yunwa,sosai sukaji dadin alalen. Shakeerah ta dubi su Fauzi tace"In takaice muku fulani itace dalilin arzikinmu. Munje munga sabon gidanmu,gaskiya yayi kyau sosai nida Aunty Saudah a daki guda,daki daya na Ammi dake kallon namu sai daya na Abba da yake da kofa ta waje,duka dakuna biyu Italian bed ne,Daya Kuma Royal shine na dakin Abba,dakuna ne manya² Wanda da safayan 1-1 sitter sai na Abba ne da 1-2 sitter da bangaren dining Falon Kuma kujeru ne hadaddu golden saikace glass Sunyi kyau sosai. Jali tabawa Abba na miliyan Daya sannan ta hadAshi da direban ta suka fara sana'ar sai da motoci. Nan kuwa 'yan uwan Abba suka sake tsanar sa suna yawon cewa yankan Kai yafara,watarana muna zaune da Ammi shi Abba bayanan sun fita da direban fulani sunje kano dauko wata mota. Wani yaro ne yayi sallama ya shigo,amsawa nayi na fita tambayata yayi Wai ance Nan ne gidan wai malam muhammadu? Na'amsa da Eah nan ne wake nemanshi? yaron yacemin wasu maza ne su biyu a waje,cema yaron nayi muje nagansu tare muka fita na bude gate din gidan,Cike da mamaki nake dubansu baba Ayuba ne da baba sani,duk yayyen baban mu ne. Ganina yasasu sakin murmushi gaba dayansu,Nima murmushin naayar musu Ina cewa lahh kune?ku shigo,da to suka amsa ko wanne yana kokarin fara shigowa ganin zasu bangaje ni yasani matsawa suka Shiga,gaba daya bin gidan suke da kallo,wani kolulun bakin ciki baba Ayuba ya hadiye har muka shiga falon,daburcewa sukayi ganin kujerun,Cike da fara'a Ammi ta tarbesu Zama sukayi akan kujerun duk da sunsa ba gani a gidan chairmomin local government,gwanda ma baba

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});