Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Deejamah Book 1 Complete Hausa Novel 1,271 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dai ta koremu a dakinta,sannan ta dena bamu abinci nida dijee da mahaifinmu,duk wannan abun baba ladi ta bata shawar tace itama bata bashi. Abinda Inna bata sani ba shine baba ladi na Aiko Yaya kaltume da abinci,Kuma duk dare tana zuwa gaishe shi. Maganar kanwata hadasiyya da sauran 'yan uwana yaran baba ladi su uku hassana,usaina,hauwa,su hudun nan sai suka fara harkan karuwanci,domin kuwa maza har cikin gida suke kawowa,suyi iskancin da zasuyi sufita,wannan dalilin yakara haddasa jikin baba yayi zafi. Ya Zama na unguwar mu babu gidan da akewa Allah wadai da tirrr Kaman gidan mal Ali mai icce wato gidanmu. Kunsan Allah daimond ladies sam bamuyi dace iyaye na kwarai ba,domin baba ladi da Inna su suke nuna ma su hadasiyya yanda zasuyima maza suyi iskanci dasu. A kwana a tashi baba ladi ta ragewa Yaya kaltume sanwa,Wanda ake samu taba baba shima ta dena,mu dama tuntuni Inna ta yayemu. Ita burin baba ladi Yaya kaltume ta gujemu tace sam bata yimmu. A hankali muka fara shiga wahala da tagayyarar rayuwa hatta tufafinmu Basu da kyan gani saboda bamu da maraba da almajirai,shawarar Yaya kaltume na nema akan zamu je neman aiki gidajen masu kudi,da kyar ta amince shima sai da taja mana kunne sannan ta amince,ita da kanta ta samammana aiki a gidan wani hamshakin attajiri babban Dan siyasa senator Ahmad shehu tabako. Gidan mutane masu karamci da sanin darajar Dan Adam,Basu da matsalar komai da tawuce ta matan uba,Sam matar shi a maryan Bata da hali. Koda Yaya kaltume taje muka musu bayani ni kadai suka dauka aiki Banda kanwata dijee,munyi kokarin su dauketa Amma abin ya gagara domin sunce tayi karama da yawa a lokacin tana 8years. Haka muka hakura,mub rabu sun daukeni aiki gobe zanfara zuwa wajen bakwai na safe. Bamuyi kasa a gwiwa muka cigaba da bin gidajen masu hannu da shuni don nemawa dijee aiki,cikin yardan Allah muka samu a gidan wani dan siyayasa shima. Alhamdulillah sun dauki dijee,matarshi tana da kirki da fara'a ga son mutane,ta dauki dijee bayan tace itama gone zata fara zuwa,kafin mutafi sai da tayima na ihsanin kudi dubu biyar tace dijee tasai sabulu tayi wanki,sannan ta bamu kayan abinci, taliyace guda biyu da doya hudu. Cike da farin ciki muka dawo gida,duk inda muka wuce zunde a ke Mana da baki,a dalilin 'yan uwan mu da suka fada harkan karuwanci. Bayan munshiga gida Yaya kaltume ta amsa abincin da kudin ta adana mana,makota tashiga gidan wata kawarta ta dafo Mana taliya ta kawo mana mukaci saboda Babu halin girkawa a gidanmu. Wata ranar alhamis da safe usaina ta shigo da kwarton ta sun gama shedan cinsu da masha'a Aiko daganan tsiya ta barke ita dashi,dambe suke sosai tana zazzaginshi. Mari ya kifa mata Yana cewa wallahi kome zakiyi sai dai kiyi bazan aureki ba mezanyi da anawo irinki 'yar titi wacce rijiya ma tafi halittarki daraja. Kukan kura usaina tayi ta cakumo mashi kwalar Riga,gaba daya gida ya hargitse da hayaniya hadda makota sunzo suna saka baki Amma sunki denawa,usaina kuwa anyi anyi ta saki kwarton ta taki. Sake tsinka mata mari yayi Wanda yasata sakin ihu ta kaimasa cizo a kunne,Aiko zafin da yaji ne yasa ya fusgota ya hade kanta da garo. Wani Kara ta saki tare da sulalewa kasa,ko kafin kace me kanta ya fashe sannan ko motsi batayi,da aka dubata aka bincika Allah yamata rasuwa. Domin ko numfashi batayi innalillahi wa inna ilaihirrajiun ranar munga tashin hankali wacce ba'a samata Rana munga iftila'i,kafin kace kwabo 'yan sanda sun zagaye gidammu. Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami πŸ–‹οΈ Yafi takobi πŸ—‘οΈ πŸ’•πŸ’• ❀️ [7/18, 2:05 PM] XahrattyπŸ₯°πŸ˜˜: πŸ’βœ¨ *DIAMOND LADIES* πŸ’βœ¨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* πŸ”±(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž _Jirgin diamond ladies (Daukar Fansa) tana maraba daku,naji korafe korafen ku Akan littafin Nan,masu yabawa nagode,kamar yanda masoya na suka roka na Kuma amince albarkacinsu na maida book din diamond ladies (Daukar Fansa) Naira #100 only Babu damuwa Allah yabar zumunci_πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai*.... Page:9️⃣-1️⃣0οΈβƒ£πŸ–ŠοΈ __________Bayan komai ya lafa na hargitsin gidanmu abinda yafaru da usaina bazamewa iyayenmu darasi ba,dominko a lokacin nema lakafa ya cigaba domin iskancin su hadasiyya gaba yayi,idan kazo gombe kaje unguwarmu duk Wanda kacema gidan mal.Ali mai icce babu Wanda baisan badalar da akeba,ana cikin wannan yanayin na annobar masifa a gidan mu Allah yayiwa baba rasuwa. Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kunsan iftila'i da muka gani? Girgiza Kai su shakeera sukayi. Fauzi tace sallar gawa an rasa Wanda zaiwa baban mu,haka nida Yaya kaltume muke bin gidaje Kiran makota don yimasa sallah,Amma abin yagagara. Da yake ranar juma'ah baba ya rasu,ganin haka yasa nanufi masallacin juma'ar nayuwa limamin masallacin bayanin abinda ke faruwa. Ana kuwa idar da sallah ya sanar cewa zasuje want sallar gawa,don Allah Mutane su taho a tafi. Haka kuwa akayi manya manyan Mutane masu ilimi da kudi suka dungumo gidanmu don yiwa baba sallar gawa. Ganin haka yasa makota Suma suka fito,akayi Masa wanka a ka tada sallah......hmmmm bansan ranar da abin kunya zai gogu a tarihin rayuwa ta ba,domin ana cikin yima baba sallah hauwa tazo wucewa Tasha giya tayi tatillll a cikin maye, ta karisa bakin gawar ta fincike likkafanin da aka rufe baba. Gaba daya sallame sallar Liman yayi,tuni hayaniya ya kaure a wajen dubban jama'ah Fadi suke subhanallah. Wani yaron Liman ne yakariso inda hauwa take ya Dalla mata wani gigitaccen Mari. Tsalle hauwa tayi gefe guda cikin muryan maye tafara duramai wasu arnan zagi,sake kifa mata Mari yayi Wanda yasata kundin bala ta baje a qasa. Janta yayi da karfi ya Shiga da ita zauren gidanmu,sannan aka cigaba da yiwa baba sallah,cikin yardan Allah aka kaishi gidanshi na gaskiya. Bayan sunkai baba suka jiyo gidanmu,Liman da kanshi yafara yiwa su hauwa da hassana da hadasiyya nasiha akan suji tsoron Allah su shiryu tun kafin duniya ta shiryar dasu,su lallabawa rayuwansu su fito da miji suyi aure..... Wani uban tsaki hadasiyya taja Wanda yasa Liman yin Shiru,Cike da mamaki kowa ke kallonta,hassana itakuma ta dauka"kaga malam dakata! Tayi maganar tana daga Masa hannu,idan wa'azi kakejin yi ga masallaci can kuje kuhau munbari kayi,mu yaranka ne da zakazo kana mana wani nasiha na munafurci? Cikin da bacin Rai samarin dake wajen suka Mike sukayi kan hassana. Dakatar dasu Liman yayi,Wanda koni akaran kaina banso haka ba,naso yabari aci uwar kowacce a cikinsu. "Haba shamsu bai kamata ku biye musu na ni domin Allah nake musu nasiha,duniya CE ta ishesu Riga da wando duk Wanda ya dauki duniya don Jin Dadi ya sauke,sannan yajuyo wajen su Inna yace"ko ba'a fada ba nasan kune matan marigayi inaso ku kula da tarbiyyar 'yayanku kada ku manta 'yaya Mata Allah yabaku,meyasa bazaku gyara rayuwarsu ba? Baba ladi tace"kaga malam Liman don Allah katashi katafi mungode da nasiha,dama ba'asan asalin balbela bace sai Tace daga Sudan take,don kawai yanzu an shiryu shine za'ace ga zance ga magana.? Shiru gabadaya wajen akayi,a hankali Liman da tawagarsa suka Mike batare da kowa ya sake magana ba.

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});