Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

share shekara Bai lekota ba bare ya agaza Mata duk kudin shi da shaharar shi Bai bada Kai ga lamarin mahaifiyar shi ba inda Ni Kam gidan iko nace anyi asara kuwa indai haka ne........... [5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 12* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Ta faka motar me kololuwar daraja a farfajiyar Asibitin national hospital dake babban birnin tarayya Abuja inda ta fito fuskarta sanye da Derk spes ta soma takawa sannu ahankali tamkar me tausayin kasa hannunta sabe da jakar LV kafar ta sanye da takalmin LV mahadin jakar sai wani matsiyacin leshe Wanda ya lashe kudi ba kadan ba kamshin turaren ta ya bulale wurin ta kara daukar kanta yayin da ta ga wasu manyan Mata suna binta da kallo don gaskiyar magana shigarta Babu karya don ta samu Kabir mashi yadda take so Kuma ya rike Mata Kan macijin inda har take Jin kanta ame jinin arziki Ta iso ofis din sister mero wadda aiki yayiwa sauki suka gaisa inda meron ke kallon ta cikin Sha awa "Jiya kin Kira bana Asibiti naje gwarunfa duba wata abokiyar aikina da bataji Dadi ba Ina fatan dai ba kwayar pills din da Kika Saba karba Zaki karba don gaskiya lokaci yayi da ya kamata ace kin haihu ai kin Sha Miya haka Nan, "Uhum mero ai ba Zan kuma yarda insha wani Abu yanzu da sunan Hana daukar ciki don nayi nadama ba kadan ba...... "Gara dai Kam don abin in ya kazanta Babu kyau. To yanzu me za ayi Miki? Ta sauke ajiyar zuciya "Mero na rabu da mijina sanadin Rashin haihuwa inda ayanzu nayi wani auren Wanda bana fatan sake gamuwa da wani tarnakin irin na gidan AK shine nake son samun mafita daga gareki..... Mero ta tareta "Kin samu matsala ne halan? "Na samu matsala kuwa gagaruma wadda silar Shan maganin Hana daukar ciki ya haifar min har na samu bakin sakamakon ba Zan haihu ba shine nake gudun haduwa da irin waccan matsalar ta gidan AK shine nake so ki taimakeni da mafita. Sister mero ta sauke ajiyar zuciya "Gaskiya izzatu Babu wani taimakon da Zan iya yi Miki illa ki rungumi kaddara Kuma hakan ya zamo izna da Jan kunne gareki da masu irin abinda kikayi Shi Allah ba ayi mishi Dole ana yin tsari Amma sai an fara haihuwa anga yadda haihuwar ta faro misali yinta Kai da Kai ko Kuma inke da mijinki zaku iya haifar me cutar sikila idan kunyi tsari ba laifi bane don ku hutar da yaran daga wahala Amma da yawan ku Kuna SHIGA hurumin Ubangiji da son kuci gyaran wahayi........ "Kinga mero ban baro gida don inzo kiyi min wa azi ba in wa azi nake sonji zanje ne in siyi kaset ko in bude Sunnah TV ban kumayo wanka don inzo ki shaki kamshin turarena ba, A a nayo kwalliya ne don ina so ta biyani kudin sabulu...... "To naji hajiya izzatu me kike so nayi Miki yanzu? "Shine abinda ya kamata kiyi ba Wai ki saki baki kina neman shiga rigar malunta ba. "Ina so ne na mallaki Da ko Diya ta yadda Zan fita daga matsalar bana haihuwa shine kawai nake so ki taimakeni "Wannan me sauki ne inaga gidan marayu kawai ya kamata kije ki darzo duk kalar Wanda yayi Miki mace ko namiji sai kin zaba.... "Idan naje gidan marayu na dauko ai kowa yasan ba nawa bane Kuma bana son na gidan marayu gaskiya Kuma ai kowa zai kalle shi da sanin asalin sa, "To yanzu ya kike so ayi ? "Mijina na yanzu baisan bana haihuwa ba shiyasa nake so yin kauda bara da hankalin shi abinda nake so mero ke Nike so muyi magana ta fahimta don Zan biyaki kudi tundaga naira milyan daya zuwa goma akan bukatata idan har Zaki iya shiyasa ma na taho gareki don nasan aikin da Zan Baki akwai mutane fin dubu da in na Kai musu da gudu zasuyi min Sister mero da taji yawan kudin da izzatu ta ambato zata Bata akan aikin da bataji komeye ba sai ta rude ta kidime har take Jin ita ko ma Arayuwar ta ta taba Kama milyon guda ahannun ta? Yau sai ace za ta samu goma me take jira?.............. [5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 14* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Matar ta shigo da buhun bakco Wanda ta zubo kayan kadi dangin su kukar Miya daddawar kalwa da kubewa da karkashi ta shigo da sallama inda izzatu ke kwance akan kujera tree seater a Dole laulayi take Ta amsawa matar aciki ta zauna tana kallon ta ganin kamar Bata da lafiya "Babu lafiya ne halan? "Eh wallahi dungo cikine ke ta bani wahala , ta fada tana gatsina fuska tamkar dai ace cikin ne na gaske "Allah ya Raba lafiya ai haka laulayi yake Dole ne ake jinjinawa uwa akan wahalar samuwar danta Allah kayi Rahama ga iyayen mu ke kuma ya Raba ku lafiya ke da duk wata me dauke da Kaya irin naki. Ta amsa kamar ana Mata Dole. Amma abin mamaki ko ruwa ba ayi karar bawa ladidi ba me amsa sunan dungo ita da gidan danta bare abincin tarba Amma dayake Allah ya zuba Mata ruwan hakuri Bata damu ba daga karshe ma izzatu Nan ta barta yashe afalo ita Kuma ta shige daki tabi gado Wai ita me ciki Sai biyar na yamma me gidan ya shigo inda yayi arba da uwarshi yashe a falo ya zube suna gaisawa inda yake tambayar Wai lafiya tazo? "Eh lafiya Amma ba Lau ba ruwan da akayi kwana uku da ya wuce bango na ya Fadi Allah ya kiyaye Babu abinda ya taba sai Yar akuyata itama ba sosai taji jiki ba don na barota ma tana yawon ta. "To Allah ya kiyaye gaba zansa agyara shi ko zuwa Nan da wata me kamawa in Sha Allah. "To Allah ya bada iko Kuna lafiya dai ko? Nazo na samu izzatu ba lafiya inda take sanar Dani cikine Allah ya Raba lafiya Ya amsa Yana murmushi don shi kanshi Yana muradin yaran Kishin ruwa ya isheta har ta kauda alkunya ta tambaya ya dauko gorar ruwan ya Bata ya Kuma lariya ta kawo Mata abinci Amma tace ta koshi inda ta Miko mishi kayan kadin dai dai da fitowar izzatu tana shake hanci Wai wani wari wari take ji inda ya nuna Mata kayan da babar ta kawo inda ta toshe hanci "Haba Ashe buhunki ne baba yake wannan doyin don Allah jeki dasu zasu sakani amai bana ma amfani da irin su Wani Abu marar Dadi ya daki zuciyar dattijuwar Amma ta matse inda ta amsa da fadin ba komai Bata San basa amfani da su bane ta Mike da Shirin tahowa inda takewa izzatu fatan samun lafiya abin takaici Wai dubu biyu tayi

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});