Chapter 26
Chapter 26
GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 36* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .......... Lubabatu tamkar wadda aka zuge dare Daya ta sauya sauyi kuwa me yawa abinda ya bawa AK mamaki Amma duk da haka yayi Mata uzuri don aganin shi Dole taji Babu Dadi musamman yadda ta Saba Rayuwa cikin iko da wadata yau Kuma lamarin sai sannu Bata fito fili ta fada mishi ba Amma ya lura da ita da take taken ta Amma duk da haka yayi Mata hanzari don abinda ya nuna mishi kamar tagaji shine kullum cikin bacin Rai take abu kadan Kuma sai ya fusata ta Koda ko ita da yarane sai kaji tana ta antaka musu zagi abinda ta San bayaso bare duka sai ya zamo yanzu duk ta hada tanayiwa yaran sai dai ya kalla ya kauda kanshi Idan Kuma ta hadosu shi da ita zata rufe idonta ta gurza Rashin mutunci son ranta Amma duk da hakan baya biyewa don ya San mafarin lamarin har dai wata Rana ya zaunar da ita Yana mata nasiha "Kiyi hakuri lubabatu komai Kika gani aduniya Yana da farko da Kuma karshe. Kar wannan canjin yasa kiji aranki ko Rahamar ta Kare ko babu sauran wani Jin Dadi Nan gaba . A a yanzu ne ma lamarin zai Fara duk bawan da Kika ga an jarrabeshi matukar ya cinye jarrabawar shi to matakin nasara ne ya hau . Hska Kuma Babu Wanda zaiyi hakuri Bai cimma rabar hakurin shi ba don haka don Allah da manzon sa kiyi hakuri babun da muke ciki in Sha Allah zamu samu kanmu cikin wadata wata Rana matukar dai munyi hakuri domin Allah. Na sani ba kowane zai jurewa Rashi ba to Amma ai bawan da yayi imani yasan Dole ajarabeshi sai mu godewa Allah da ya bamu wannan jarabtar me sauki kiyi hakuri ki Kuma jure ki koma hango baya yadda kika samu Kai sai ki godewa Allah shi Kuma sai ya dubeki ke da lamarin ki. Ta matse hawaye ba tare da tankawa nasihar sa ba inda yaji tausayin ta ya Kara kamashi Da hakan dai ake ta gurgurawa da Dadi ba Dadi kamar dai ta dauka ko ta hakura inda ake cikin Rufin Asirin Allah wani abun mamaki Kuma ba a Kara kiranshi Kan abinda ya shafi harkar kwangila ba shima kuma Bai nemi cusa kanshi ba ya tsaya matsayin shi Yana ta laluben hanyar da Asiri zai rufu inda Allah cikin ikon shi masu zanen taswirar gidaje Kan bashi aikin zanen kasancewar shi eng Wanda ya hada har da sanin makamar zanen inda Kuma kudi ke Dan shigowa Amma ba kamar yadda aka sababa Inda agefe Daya Kuma Kabir yayi wata irin shahara da tunbatsa akan harkar gwangila saboda ayanzu shine ke Kan kadamin shi aiki Kuma Babu nagarta haka za ayi shi agama kafin lokaci kadan ya lalace saboda an saka manuba da ha inci Malam Ali yayi ta Kiran wayar shi Amma kememe yaki dagawa saboda ya San maganar dungo za ayi mishi inda a yau malam Ali ya bugo hanya ya iso garin Abuja duk da Bai San gidan Kabir din ba Amma akace matambayi baya Bata kasancewar shi shahararre Bai Sha wuya wurin gano gidan ba inda ya tsaya Yana karewa gidan kallo Wai gidan dan dungo ne wannan Amma ta Rayu a wani gida da bashi da maraba da kufai saboda ruwan damuna da ya kayar dashi Anna Bata samu arzikin tadawa ba Amma dubi gidan da yazo garin Abuja ya Gina tamkar yayi wurin Zama aduniya Bama wannan ne abin ji ba irin yadda aka kirashi yazo ya samu mahaifiyar shi cikin halin ciwo da neman agaji Amma bawan Allah Nan tunda ya ufa ya tafi Bai Kara waiwayo ta ba bare yayi tunanin duba yadda ta karaji da jiki bare ya kawo Mata dauki ko agaji Yau tsayin watanni shida Babu dungo Babu labarin ta Amma ko dai dai da Rana guda Daya Tak Bai tunawa da uwar shi na cikin neman taimako da agaji bare Kuma ya ruko wani Abu irin na jinkai da ya'yan kwarai masu neman albarka kewa tsaffin su Kai wannan wace irin SHIGA UKU da asara ce? Ubangiji ka shiryi bayinka masu Bata kasa yaran musulmi su zamowa iyayen su sanyi idaniya irin su kabiru Kam da haihuwar su wallahi gara barin su don haihuwar su batayiwa Wanda yayita Rana ba Malam Ali ya share hawayen tausayin dungo yayiwa me gadin magana akan asanar da me gidan yayi bako Aiko sai gashi ya fito cikin shiga ta Wanda ya samu wurin Zama a duniya Kaya masu tsada Wanda kallo daya zakayi mishi ka bashi matsayin minister ko Dan majalissa Ganin malam Ali yasa ya ji wani Abu marar Dadi ya sauki she da ruwa da lemu inda yake tambayar shi "Kabiru baka tambayi me jiki ba bare ka Kira kaji ya ta Kare ji? "To ai lafiya ita ke fakuwa na San dai taji sauki.............. "Amma ko taji sauki ai tana bukatar kulawa mussamman Kai da kake dolen ta "Kabir kayi sannu da kidan da duniya ke maka kana taka rawa Wallahi Babu komai acikin wannan Rayuwar sai rudani Duk nasarar mutum a Rayuwa ya samota ne daga addu ar iyaye don su ke da mabudin kowace irin nasara... "Bama abinda ya kawo Ni wurinka kenan ba don kowa ya gyara ya sani banzo don nayi maka wa azi ba sakone dungo taba Ni ta Kuma ce in isar gareka gashi Kuma Allah ya Taya min na kawo maka sai dai abin tashin hankali da saka zuciya rawa shine mun nemi dungo sama ko kasa mun rasa..................... [5/24, 7:50 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 37* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ...........Arude yake kallon malam Ali Jin yace Wai Babar tashi ta bace an nemeta sama da kasa Babu ita Babu labarin ta............. "Malam Ali ba asan inda take ba kenan? "Abinda yake daurewa mutane Kai kenan don faruwar lamarin tamkar kiftawar ido Wai an nemi dungo Babu ita Babu dalilin ta "Shin wani ne ya sace ta Koko guduwa tayi???.......... "Allah shine mafi sani abinda kawai na kawowa Raina shine dungo tana ganin Bata da kowa sai kanta idan ta faku idanun Al umma batayi laifi ba shiyasa don nafi zargin guduwa tayi don bakin ciki Babu abinda baya sawa........... "Bakin cikin me malam Ali?........ "Bakin cikin ka kabiru me yuwa dungo tana kallon kanta a wadda batayi SA AR haihuwa ba don ban taba ganin Dan halak yayi irin abinda kayiwa mahaifiyar ka ba Kabir Abu Daya Zan fada maka shine ka saurari zuwan musiba don kuwa kajawo Allah fada.... Arikice kabiru ya Mike Yana duban malam Ali da ya fada mishi gaskiya Amma ya kasa abinda zaiyi don ya yarda ya amince lallai ya jawo Allah fada Malam Ali ya Mike Yana fadin "Ni na koma sai Allah ya kaddaro saduwar mu idan kazo inda nake ma gaisa idan kuwa ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31