Chapter 29
Chapter 29
sa zuciya ta bugawa ba.......... "A a malam Bari nazo na nuna maka yarinyar da nake fada maka na samu don ka ganta sai dai fa ban taba yi Mata magana ba saboda kwarjini da tayi min na dai binciko ance min Yar gidan eng AK ce na Kuma San baba ya sanshi shine kawai na fada mishi ina sonta yace in Bari zaiyi mishi magana Amma har yanzu na kasa yi Mata magana sai dai kawai na Zo inda Zan hango ta na kalleta na more....... "Amma dai ka kusa bada maza badamasi duk barikin ka ace tsoron mace kake? Ko dayake wata Kil kamila ce shiyasa kake shayinta kaga banbancin matar kwarai da ta banza inda abariki ne Babu wani kwarjinin da Matan bariki kewa Yan bariki tara ce ke dukan goma........... 'ban Yi maka gardama ba abokina muje in nuna maka ita... Haka suka fito har zuwa kuki cafee inda Kuma cikin sa a ta fito ta soma takawa domin komawa gida inda Kuma agefe guda Wilson shima yake lafe yana Kare Mata kallo inda Kuma gaban Anwar ya buga da karfi yarinyar da ta saci zuciyar shi itace masoyiyar badamasi? Lallai akwai hayaniya a gaba duk surutun da badamasi keyi domin Koda ummita Anwar baya cikin hayyacin shi da haka sukayi sallama ya taho Kai tsaye ya tunkari Mr President cewar yanzu ne ya samu matar aure idan zasu yarda ya auri Mata uku to ahada mishi da ita idan kuwa ba zasu yarda ba to abar auren duka Mr President yayi murmushi "Yar gidan waye ita wannan din ? Yar gidan eng AK ce ya bashi amsa "To kaje zanyi mishi magana ko ta hudu ka Kara hangowa kayi magana Zan cike maka su hudu dai dai ai Kai din Dan gata ne, Anwar ya tashi Yana murmushi yayiwa Mr President sallama ya wuce abinshi.................. [5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 40* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Alh uba Dan yaro yazo har gida ya samu eng AK Akan Dan wurin shi badamasi yaga yarshi Yana so har ma suna rokon iri don hada ZURIA Eng yayi shiru don har ga Allah baya son yiwa ummita auren da ba itace ta kawo Wanda take so ba Kuma hasalima Yana da tarihin Rayuwar badamasi da yadda yake son sheke Aya da Matan bariki shi da kanshi ba zai yarda da auren badamasi ba don haka Bai boyewa Alh uba Dan yaro ba. "To alh na gode da kauna don me son hada ZURIA da Kai ya gama maka Dukkan kauna sai dai gaskiya alh bana son matsa Mata akan aure don yaran yanzu kana so ina so ma ya aka Kare bare anyi basa so? "Zan sanar da ita zancen badamasi ka Kuma turoshi yau ko gobe don su gana idan yayi Mata shikenan idan kuwa baiyi Mata alh sai yaro yayi hakuri...... "Kar ka damu abdulkarim koni ba zanso kayiwa yarka Dole a aure ba don wannan zamanin ba irin Wanda ake Dole a zauna lafiya bane Ina fatan alkhairi agaresu idan Kuma baiyi Mata ba sai ya nema agaba da haka sukayi sallama inda ya dire mishi kudi masu kauri akan Wai ya bawa Yar shi ta siyi kayan kwalliya sukayi sallama ya tafi Bai boyewa lubabatu ba dake ta Shan sharafinta da daukewa ak Kai ya zayyane Mata yadda sukayi da alh uba Dan yaro Amma ke da ke can in kin tanka ta tanka mishi don tana ganin awannan halin za ayiwa ummita aure cikin halin Babu? Bai bi ta kanta ba ya kira ummita dakin shi ya sanar da ita abinda ke faruwa na game da badamasi da ubanshi ya Zo neman aurenta ya Kuma nemi Jin Ra ayin ta Ta sunkuyar da kanta kasa tanajin kunya tana Kuma nazari............... "Kar ki kwari kanki ummita ba Zan taba yi Miki AUREN Dole ba Wanda kike so shi Zan Baki don haka idan kinji ranki Bai dauka ba Babu kunya tsakanina dake Zan Baki damar ki. "Abba na baka zabi wallahi zanyi maka biyayya muddin ka hango cancanta da dacewa akan shi zanyi maraba in Kuma roki Allah ya zaba min abinda yafi ALHERI Ya sauke ajiyar zuciya Yana godewa Allah da ya bashi ya me biyayya "Allah yayi Miki albarka ummita na gode da karrama Ni da kikayi Amma ki Bari zuwa yau ko gobe badamasi zaizo ku gana yadda Kika ganshi ko kikaji shi aranki kar ki boye min ta haka ne Zan yanke hukunci na adalci amatsayina na mahaifin ki Ta amsa ta fito Washe gari kuwa sai ga badamasi ya iso cikin shiga ta Alfarma da son ya siyo zuciyar ummita Amma Rashin sa ar da yayi kallo daya tayi mishi taji yayi Mata Kama da Yan duniya ita Kam Bata muradin auren irin su don wayewar su tayi yawa Sukayi fira ta Yan Mintoci duk yadda yaso ya yaudari zuciyar ta hakan Bata yuwu ba haka sukayi sallama Yana Bata kudi Amma Taki karba tayi godiya inda yake Jin lallai irinta yake so wace macece ke kin kudi a wannan duniyar? Sai yaji ta Kara burgeshi da haka ya taho Yana santin aurenta "Yaya Kika ga badamasi ummita? Shin yayi miki Koko akwai matsala? Tayi shiru kafin ta dubi abban nata "Kayi hakuri Abba ka gafarce Ni gaskiya Bai yi min ba wayewar shi tayi min yawa............ "Nima da kin zabi badamasi ummita to da Zan fada Miki aibin auren shi don Nima tarbiyar shi batayi min ba Amma tunda Ra ayin mu yazo Daya shikenan sai abashi hakuri dama ban rufeshi ba ke Kuma Ubangiji ya Baki miji na gari ta amsa ta fito Haka kuwa akayi ya iske alh uba Dan yaro ya sanar dashi yadda sukayi da yarinya ya Basu hakuri ya dawo gida Kwana biyu Wilson na kwance Babu lafiya abinda ya tabbatar ciwon son ummita ne ya kayar dashi inda ya hadiyi magani da allurai Amma duk abanza Babu wani sauki sai radadin zuciya Tamkar Wanda ya amsa umarni ya zaro key din mota ya fice zuwa kuki inda yayi nasarar ganin shigarta ya zauna zaman jiran fitowar ta Sai yamma ta fito inda ya shigo mota ya karaso inda take tafe akasa ya danno Mata horn Ta juyo Inda idonta ya hasko Mata shi sai tayi maza ta daure fuska yayin da shi Kuma yajefota da wani murmushi ya fito Yana fadin "Kice yau da kafar dama Kika fito gashi mun hade don hanyar gidan naku zanbi Ta sassauta fuskar ta "Ayya yau Kuma inajin Kaine baka fito da kafar damar ba don yau ba inda kasani zani ba......... "Sa ar takice take da yawa har nayi nufin kaiki duk inda zakije Ta dubeshi "Na taba fada maka duhu da haske basa tarayya a wuri Daya me kake nufi da SHIGA cikin Rayuwata? Ya shafi sumar kanshi Yana murmushi "Nagode da wannan damar da Kika bani manufata itace muyi musayar zuciya....... "A hakan zamuyi musayar zuciya kana a duhu? "Kasancewar mu mutane jinsi Daya shine kawai alakar mu ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31