Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

son ganinka.... "An gama hajiya dama Babu komai ahannu na.......... "To maza garzayo kasamu kudi yanzu Minti Sha biyar ya iso inda take fada mishi abinda take so yayi Mata "Ka Gane ko gambo wata ce nake so ka bi min bayanta zuwa first Bank zata fiddo wasu manyan kudi shine nake son ka karbo min su ka dawo min dasu zaka ganta cikin mota 206 jar kala me lambar katsina yi maza gambo ka karbo min kudin Nan kar ka yarda asamu akasi ko sabani......... "Babu kuskure acikin aikina hajiya Ina me tabbatar Miki da awa uku tayi yawa kisaka Ranki inuwa kudin ki sun dawo Miki sun gama Ya fice Yana fiyto izzatu ta zauna tana dariyar mugunta "Uhum mero kenan yaro yaro ne yaro Bai San wuta ba sai ya taka mero kinci karya kin kwana da yunwa Gambo mafiyas ya iso bakin ya labe a gefe Yana kallon mutane me SHIGA da me fita ba inda ya hango motar sister mero wadda aka kwatanta mishi Sai ya soma dakon jiran fitowar mero Mero da ta gabatar da cek din da zata fitar su kansu sun girgiza Anna da suka duba asusun izzatu sai Basuyi mamaki ba atake suka Bata takardar da zata cike ta cike aka fitar Mata da kudin duka sai ta raba su ta saka milyon biyar cikin asusun ta ta fito da milyon biyar don taje ta biya bashi sau Kuma ta aje don bukatu Ta SHIGA motar ta ta nufi gida don ta Kira me mota yazo gida ya amshi kudin shi saboda zai fi sirri Sai dai wani Al amari dake Shirin faruwa ya gigita sister mero inda wata mota ta Sha gabanta cikin azama ta taka burki don kadan ya rage ta banki motar da ta Sha gabanta Atake gambo mafiyas ya fito ya na bude motar mero Yana kanga Mata bindiga agoshi Yana tambayar ta kudi Bataja ba ta jawo buhun kudin ta Miko mishi ya amsa ya koma motar sukaja motar aguje suka bacewa ganinta inda mero take sauke ajiyar zuciya ta iso gida tana tunanin waye ya San zataje banki? Babu ko shakka izzatu na da hannu akan wannan abin da akayi Mata koma ita ta turo Mata bakaken mabiya sai Kuma ta tuna da yadda izzatun taso yi Mata dungu akan kudinta sai kawai ta gano mugun kulli ne izzatu ta kullo Mata inda Kuma wata zuciya ke Bata shawarar tashi kije kuyi ta ta Kare Babu Wanda yasan zakije banki sai ita to komai zai iya faruwa Aikuwa ta fice zuwa gidan izzatu inda ta badda sawu da saka nikabi ta tari napep ya kawota kofar gidan izzatu inda Kuma cikin sa a ta ga motar da tayi Mata fashi ta faka har katon basamuden da ya yi Mata atakin da bindiga ya fito Yana rike da buhun kudinta inda ta tabbatar dai izzatu ce me alhakin yi Mata hakan, to yanzu meye abin yi? Anya kuwa idan tace SHIGA zatayi gidan izzatu ba zata saka katon ya illatata ba????............ [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *page 18* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Wata zuciyar tace Mata shiga kawai ki karbo hakkin ki tunda ma gashi kin gani ya kawowa wadda ta sakashi Har ta cire kafa zata tunkari kofar shiga gidan sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta Akul Kika SHIGA gidan can yadda Dan ta addar can ya nuna Miki bindiga komai zai iya faruwa gara dai ki koma gida ki sako sabon lale Amma SHIGA gidan can ayanzu akwai matsala Sai Kuma ta karbi wannan shawarar da fuskar fahimta ta juya gida Gambo mafiyas ya direwa izzatu kudin a gabanta inda inda ta Gane kudin ba duka bane Amma dai an rage ta Zaria rafar dubu dari ta bashi ya karba Yana godiya inda yace da wani aikin ya samu ta kirashi Da haka ya fice Yana zukar tabar iblis din shi Abinda izzatu bats sani ba shine shima gambo mafiyas sai da ya wari wasu kudin ya boye don harkar duka Babu Amana Amma izzatu Bata Gane ba ta dauki kudin ta mayar daki Komawar sister mero gida ta doko wa izzatu waya inda tana ganin Kiran meron gabanta ya Sara dass ! Amma sai ta maze ta daga da salon bagararwa "Sister mero ya kike ya aikine? "Lafiya Amma abinda Zan fada Miki izzatu karki yarda kice irin wannan wasan zamuyi dake don na rantse Miki da Allah sai na kaiki kasa warwas.......... "Me akayi Kuma mero?....... . "Karki yaudare Ni don Ni ba yarinyar goye bace idan kudin ki kike so ai ba sai kin turo min babbakun mabiya ba sai in maido Miki in karbi Yar mutane......... "Nifa bangane Abinda kike nufi ba mero wani Abu ya faru ne? "Kin fini sanin abinda ya faru saboda Babu Wanda ya San zanje banki karbar kudi sai ke to Akan me Zaki turo min Dan fashi bayan Ni da ke taimakon juna mukayi? Kuma magana Kare nazo dazu na tarar da shi Wanda Kika sa yayi min fashin ya Zo gidan ki da buhun kudina to saurareni da kyau na rantse Miki da sarkin da ya huran numfashi da tassarufin lamurana sai kin biyani kudina Baki Nan da awa ashirin da hudu ki turo min kudina ga lambar asusuna Nan Zan turo Miki idan Kuma kina bukatar sauran kudinki Zan maido Miki in karbi Yar mutane duk shawarar da Kika yanke Ina jiran kiranki......... Dit ta yanke wayar tabar izzatu da kyalkyala dariya "Uhum mero kenan na kula in ba kwanji na na motsa ba Zaki zame min kadangaren bakin tulu to duk Zan hada in kashe da tulun da kadangaren don Banga amfanin su ba Akarshe dai ta yanke shawarar turawa sister mero kudinta don suna game wayar sakon lambar account din ta shigo wayar izzatu a take kuma tayi Mata transfer ta wsyar kudinta suka SHIGA inda sister mero tayi murmushi "Uhum izzatu kenan tunda wannan turbar kike son mubi to Zan nuna Miki Ni har gobe takadarci Yana min Rana Baki sanni bane Amma Zan nuna Miki kece karamar Yar iskace Nasha gabanki har abada ke gaba da abada ma na wuce da iyawar ki Zan Kuma waiwaye ki don wasan mu Bai ma fara ba karamar marar kunya dake bileja Itama izzatu anata bangaren Tasha mugun Alwashin akan mero saboda ta kula itace zata zamo Mata matsala to su zuba shege NE zai fasa Bata santa bane nata iskancin kawai ta sani Bata San nata ba Allah yasa tsautsayi ko azal ya sa mero Kiran wayarta ko ma zuwa gidanta taga yadda ake kera Rashin mutunci Tom Bari muga yadda Za ayi haduwa ta gaba da sister mero da izzatu waye zai FASA KWAI............. [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 19* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Wata irin Rashin lafiya ta Kama dungo uwar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});