Chapter 19
Chapter 19
kwalliya abind ya gigita Kabir mashi shi Kam zai iya cewa gara da akayi da haka Anwar yayi sallama ya shigo ya zube Yana gaishe da Kabir mashi don ya sanshi sosai Yana ganinshi agidan nasu sai dai har ga Allah Bai zaci shine uban yarinyar da tayi mishi gatsali ba. Mr President ya tambayeshi "Su waye kasa aka kulle a station? Ya fada mishi duk yadda abin ya faro har zuwan izzatu da irin tozarcin da tayi mishi duk ya fada musu inda Mr President yayi murmushi "To kanwar ka da uwarka kasa aka kulle don iyalan Kabir ne sai kaje maza kasa asake su............ Yazube gaban Kabir Yana bashi hakuri "Kayi hakuri Abba ban sani ba ne ka gafarce Ni yanzu ne zansa akansu har gida............. [5/19, 4:36 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 27* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Abinn tausayi abin kuka da zubar hawaye ciwon dungo duk me tsoron Allah Dole yaji zuciyar shi ta raunan bisa Dole ta aje raino don Bata iyawa ciwo yaci karfinta Makotan ta malam Ali da Jamila sun Mata karah matuka gaya inda malam Ali ke tur da Allah wadai da Kabir da duniyar dake Rudin shi Jamila Bata San dungon nada wani da da har ya shahara ba kallon da take Mata Bata taba haihuwa ba Amma da dungon ta fada Mata tana da Da Yana zaune garin Abuja...... "Kuma ke Kika haifeshi dungo? Kwarai kuwa Jamila baya son dai rabata Koko Yana ganin ya wuce akalli fakiriya Irina ace nice na haifeshiba? Oho "Amma gaskiya kiyi hakuri dungo indai ke Kika haife shi gaskiya Bai maida biki ba Kuma Bai zamo da abin alfahari ba tunda Bai damu da damuwar ki ba shi kuwa me yake nema cikin duniya da har take Rudin shi yake Miki hakan? Allah ya shirye shi yasa ya Gane Amma fa Yana da tarin kalubale gaban shi Wanda alhakin kadai zai iya tadeshi Shi kuwa malam Ali da ya shigo yaga dungon cikin halin ciwo ya tausaya Mata Ya dubeta "Dungo kabiru kuwa yasan Baki da lafiya haka? "Ya sani malam Ali tunda har gida na taka naje na sanar dashi "Ya Zama Dole akirashi yanzu don Dole Dole ce. Ya a karbi wayar ta ya lalubo lambar shi ya kirashi Wayar ta shiga tayi ta burari kamar ba zai daga ba sai da aka jera mishi Kira kusan bakwai kafin ya daga Kuma Yana gani ya kuma san me lambar Yana ganin dai idan ya dauka aiki zata Sara mishi shiyasa ya watsar da Kiran sai da yaga ba za a hakura da Kiran ba ne ya dauka akule "Kabiru kana lafiya? Cewar malam Ali ya amsa da lafiya "Dama don in sanar dakai tsohuwa fa ba lafiya har ana bukatar ganin ka da gaggawa in ma Babu wani uzuri me nauyi akanka to ko zuwa gobe ne sai ka Zo. 'to Babu matsala ya fada Yana aje wayar ba tare da yajira sallamar malam Ali ba Washe gari kuwa sai gashi ya iso da safe inda ya iske dungon cikin halin ciwo ta rame ta Kare abin tausayi ga me raunannar zuciya ma sai ya koka Amma dayake akwai karfin hali sai kwarara kanta take. Ya zube Yana gaishe ta Yana Mata sannu da jiki ta amsa tana tambayar shi iyali ya amsa da kowa lafiya Malam Ali ya shigo suka gaisa inda yake mishi bayanin ciwon da ya ke damun tsohuwar tashi Ya kadu ba kadan ba Jin Wai ciwon Koda ne matsalar ta Ya sauke ajiyar zuciya "Aikin gaskiya babba ne kudi ake kashewa ba kadan ba yayin dashen Koda Kuma Ni gaskiya yanzu bani da kudin da Zan iya biyan aikin. Sai dai ko a saurara zuwa gaba....... "Haba kabiru irin wannan halin da take ciki kake maganar a saurara? Idan har baka da kudin biyan aikin sai kuje a ciri taka a dasa Mata don duk Wanda zaiyi hakan bayanka yake "Nima fa ba lafiyar Nan gareni ba malam Ali a dai saurara din har zuwa gaba shi ciwo shi ke shiga da garaje Amma lafiya sai ahankali. Malam Ali ya bishi da kallon takaici da hasara da dai haihuwar irin wannan yaron gara abarar dashi a zauna Babu haihuwa don haihuwar irinsu in ba damuwa da bakin ciki ba Babu abinda suke gadarwa Kabir ya zura hannu acikin aljihun shi ya debo kudi dubu goma ya dire agabanta "Gashi inna a rike wannan Zan dawo bayan kwana biyu inga yadda jikin ya zamo......... "A a kabiru kaje da kudinka na gode Amma Zan so ka tsaya in FASA MAKA wani KWAI don kaji idan na cancanci irin wannan sakayyar a gareka......... "Inna yanzu sauri nake don akwai wata kwangila da aka bani yau Zan soma ta ki aje duk wata magana gefe sai na dawo..... Wayar shi ta dauki tsuwwa inda ya ga sunan alh uba Dan yaro ya dauka da sauri inda ake sanar dashi ana neman shi Kan kwangilar da zai Fara Da sauri ya fice daga gidan Basuyi cikakkiyar sallama da uwar tashi ba bare Mal Ali Hawaye ya zubowa malam Ali ya share Yana duban dungo "Anya kuwa ke Kika haifi kabiru dungo? "Uhum Ni na haife shi Mal Ali...... To ki tuna indai har a Asibiti Kika haife shi sauya Miki shi akayi Baba zaton Dan halak zaiyi abinda yayi Miki, mu da muka hada makotaka kawai dake muna Jin tausayin ki Amma ace da ya kasa Jin Kan uwar da ta wahalta maka? Dungo ta Mike cikin layi da jigatar ciwo ta hankado kar Kashin gadonta ta jawo wata katuwar mantimoti ta jawo wani kunshi kulle cikin tsumma ta kuma jawo wata tsohuwar takarda ta nufo malam Ali dake kallon ta da mamakin abinda take nema. Ta zube kunshin da takardar agaban shi "Malam Ali Bari yau in fada maka wata magana da ta zamo sirrina saboda Kai din ka zamo Dan uwana Kuma wannan sakon Ina so ka isar dashi ga kabiru don inaji ajikina ba zai dawo ya riske Ni da Rai ba don nasan zai wuce shekara Bai dawo ba..................... [5/19, 4:36 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 28* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ...........Malam Ali ya bita da kallo inda ta kwance kunshin tsumman sai ga kudi dumus Yan naira dubu dubu sabbi gal a daure da takardar banki malam Ali mamaki ya kashe shi daga zaune har dai yayi kokarin tankawa "Kina da kudin Nan dungo Amma Kika zauna da ciwo har Kika Sha wahala haka? ........ "Ba kudi na bane malam Ali wannan kudin kabiru ne na abinda ya gada kuma shine KWAN da nake cewa dashi ya tsaya in fasa mishi ya ki don haka ga Amana Nan dukiyar maraya ce ka isar gareshi dukiyar da mahaifin shi ya mutu ya bar mishi ce ba Zan taba mishi abinshi ba saboda Nima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31