Chapter 21
Chapter 21
siyar Miki da humairar zanyi da ban bibiye ki don haka ladar aikina har in mutu ba Zan Daina karbarta daga gareki ba don haka dauko min kudi in Kama gabana idan Kuma Zaki iya siyenta ayanzu to muyi ciniki ki bani milyon dari in bar Miki ita har abada idan Kuma ba Zaki iya ba to Zan Rika zuwa ina karbar Yar milyon biyu ko uku idan bukatar hakan ta taso.......... Tasss! Ta dauke meron da mari.... Mero ta dubeta cikin mamaki na karfin halin marinta "Kika mare Ni izzatu?...... "So ma nake kice Zaki Rama Marin kiga yadda ake hawa hanyar lahira "Uhum bama Zan Rama ba saboda ke din jakata ce ko ince asusuna don haka dauko min in wuce milyon biyu da dubu dari biyar nake so yau don Ina Jin tausayin ki da uku zance ki bani...... Karar motar fulani da izzatu ta jiyo Wanda ya alamta Mata dawowar ta yasa taga Bari kawai ta sallami izzatu don Bata son ta fahimci komai don haka ta rubuta wa sister mero cek ta Bata Wanda yayi daidai da shigowar fulanin wadda ko kallon mero batayi ba inda meron ke Mata kallon tayi saurin girma "Momy na dawo cewar fulani dake Hawa Kan bene saboda taga momy tayi bakuwa . "To sannu da dawowa. "Sai ki tashi ki tafi Allah Ubangiji yasa tsautsayi ko kaddara su sake dawo dake Nan gidan inda Zaki Gane kinyi kuskuren shigowa duniya arashin dace Mero ta Mike tana murmushi "To na gode uwar dakina a huta lafiya ta fice daga gidan inda izzatu ta rakota da wata matsiyaciyar harara A kofar fitowa gidan sister mero taga hamshakiyar motar me daukar hankali tabita da kallo inda shi Kuma na cikin motar ya fito Yana tsaida sister mero ta tsaya suka gaisa inda yake sanar da ita wata yarinya ya biyo wadda ta shiga gidan yanzu . Atake mero ta Gane humaira yake magana "Allah sarki ai ya ta ce ince dai ba wani Abu tayi maka ba? "A no Babu abinda tayi min kawai na biyota ne don Allah ya jarabeni da kaunar ta ya fada Yana rusunawa don yaji tace itace uwarta "Karka damu Alh sai dai ka Kara hakuri don Bata tsayawa da samari Kuma ma ubanta ya ce ba yanzu zaiyi Mata aure ba Amma tunda Allah Ubangiji ya kawoka bani lambar ka sai muyi magana don Nan din ba gidan mu bane munzo wata hidima ne da an Kare zamu koma gida in yaso sai muyi magana "Ok to mama Babu matsala ya bude motar ya dauko Mata compliment card din shi ya Bata inda mero ta ga suna shi honorable bello Rimaye Bata tsinke da lamarin ba Sai da taga kyautar gieman da yayi Mata suka Rabu akan zasuyi waya ya tafi Yana Jin lallai yayi sa a Mero tayi murmushi "Kai lallai abar Allah da lamarin sa wannan yarinya uwarta ta iya haihuwa Ni Kuma na karbi haihuwar ta a sa a yanzune wasan mu da izzatu zai dauko sabon salon da zai kayatar da me kallo da saurare................ [5/21, 5:47 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 30* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Tunda Kabir yayi kwangilar Nan har yau ba a Kuma kiranshi an bashi wata kwangilar ba inda akayi ta cin burin kwangilar hako Sola da akace za ayi a kauyuka biyar da yake zaton zaiyi har Yana cin buri hatta izzatu ma ta ci nata burin inda Yar lele humaira fulani ma ta shigar da tata bukatar ta son asauya Mata mota wadda ta gani a tashar MBC fitowar shekarar 2019 inda Kuma akayi Mata alkawarin da anyi kwangilar an gama za a yi Mata oder ta sai dai me? Shiru ta bashi Labari inda ya Gane lallai an maida shi aljihun baya koma angama dashi A fusace ya zaro wayar shi zai Kira eng AK inda izzatu ta dakatar dashi 'zuwa ya kamata kayi ba Kiran waya ba na lura wannan mutumin so yake yaga bayan mu Kabir idan ba sako gambo mafiyas atafiyar nayi ba ba zai saurara Mana ba. Da sauri ya tashi mota ya nufi gidan eng AK don suyita ta Kare Eng ya kwashi iyalanshi suka fice country Moll inda suke ta jidar abinda ya kawo su duk da silar zuwan ummita ce wadda tacewa abbanta tana son zuwa don siyo biscuits da kayan makulashe inda shi Kuma ya kwaso su duka suka wuce don gaskiyar magana yanzu duniyar nayi dashi Ummita da Mubarak da Ahmed da Fatima suka nufi wurin kayan kwalam suna ta jidar abinda suke so cikin sa a ya shigo don siyen makilin da wayar iPhone kawai sai idon shi ya fada kanta wani Abu ya daki zuciyar shi ya zuba Mata ido Yana kallon ta har Bai San lokacin da kafar shi ta taka ta Isa inda suke ba ya Kai hannu Kan abin takai hannu suka dire hannu alokaci daya inda tayi saurin duban shi shima ya dubeta sukayi kallon kuda atare inda yayi saurin Miko Mata abida ta Kai hannu tayi saurin Jan hannun kannenta suka bar shi rike da biscuits din Yana musu rakiya da ido inda ya saki baki Yana kallon su har suka fice inda yake tambayar kanshi Anya kuwa yayiwa kanshi adalci ace Yana amsa sunan kirista yace musulma yake so? Gambo mafiyas da yaji shirun shi tayi yawa ya kwado mishi Kira inda ya dauko abinda ya kawo shi ya fito Yana waiwayen ummita har dai gambo mafiyas ya kula da kallon da yakewa ummita ya faske keyar shi "Lover boy kayo kamu ko kake zuba Mata ido? Wilson yayi murmushi Bai tanka ba suka bar wurin Lokacin da suka iso gida eng ya hango motar Kabir mashi afake inda ya Gane wurin shi yazo Don haka ya cewa iyalan shi su shigs ciki zaiga bakon shi ya budewa Kabir falon da yake karbar Baki ya karrama shi da ruwa da lemu Yana mishi sannu da zuwa "Ba ruwa ya kawoni Sha ba AK Jan kunnen ka nazoyi don na Gane Kaine ka ke kokarin gurgun Tani tun kafin ka Fara kwangila nake yi ba Kuma Zan yarda zuwan ka yasa ka kassara niba don haka ka janye jikinka in ko kaki ji to ba zaka ki gani ba AK ya dubeshi Yana karanto hasbunallahu wa Ni imal wakil don yasan wannan mutum yadda ya fito Yana fada mishi hska to Babu abinda ba zai iya yi ba "Kayi hakuri me gida Wallahi bani da laifi akan duk abinda kake zaton Ni nayi maka Wallahi ban da hannu Abu daya na sani ana fada Akan aikinka to Zan baka shawara ka gyara don ana fadin kana bada rata shiyasa aikin Babu nagarta wannan shi na sani Kuma me gida nifa kanenka ne komai ya samu bawa da sanin Allah Ni da Kai Babu Wanda yasan gobe sai Allah Ni ban Isa na tare Rabon ka ba duk inda ka shiga sai ka samoshi......... "Bance kayi min wa azi ba so nake kawai kace ka Daina aikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31