Chapter 30
Chapter 30
kasanwa mutane Amma akwai banbanci me yawa tamkar nisan sama da kasa don haka kar ka Kuma bibiyata don abinda kazo dashi Kai da kanka kasan ba Mai yuwa bane na gode da taimakon da kataba yi min sai anjima Ta wuce ta barshi inda yake biye da ita Yana nacin ta shigo motar shi ya kaita gida Amma Bata saurare shi ba haka shima Bai fasa binta ba har ta karaso gida shi Kuma yayi zaman awa kusan biyar Yana son ganin fitowar ta Amma shiru har dai ya gaji ya dawo gida sai dai me? Yayiwa ummita tsaye arai bacci ma da ta kwanta mafarkin shi tayi tayi da ta farka ma Babu abinda take bege face ta saka idonta cikin nashi inda Kuma kwana biyu shi Kuma baije kuki ba ta damu matuka gaya har ta soma zubar hawaye ta dafe gurbin zuciyar ta "Kar ki yaudare Ni Mana zuciya? Ta Yaya Zaki sakani son abinda Bai dace Dani ba? Ko kusa haka Kuma ko alama ita kanta lamarin Bai burgeta ba to bare Kuma iyayenta suji Dole ta watsar da wannan gurbatacciyar dake nuna Mata mafarkin ido biyu ...................... [5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 41* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ............Ta taho tana fatan ayau ta ganshi ko daga nesa ne Amma ko burbushin motar shi Bata hango ba har tsayin sati biyu inda ta bawa zuciyar ta magana Amma lamarin yaki yuwa Ta fito don komawa gida kamar ance Mata juyo sai ta hango shi ya zuba Mata ido itama ta zuba mishi nata idon inda take hango tsari da kyan halittar shi Farine tas har ya soma jajaja sumar kanshi baka manyan idanu masu cike da gashin girare baka wuluk sai Dan karamin bakin shi me siraran labba sai sajen dake fuskarshi Wanda Bai Kai kasumba ba a idonta Kam ta Dade Bata ga namiji irin shi ba me yuwa shiyasa ya kasa barin zuciyar ta ganin irin kallon da take mishi yasa ya tako ya karaso gareta "Amma nayi farin cikin ganinki don kwana biyu da ban ganki ba wallahi na rasa natsuwata Allah yasa ban shiga hakkin ki ba idan nace ki shigo mota ta na maida ke gida Bata San lokacin da murmushi ya kubce Mata ba ta dauke kanta "Kar ka yaudare Ni ka Kuma yaudari kanka. Babu hadin tutu da fura Kai da kanka kasan hanyar mu tana da banbanci so ka Daina kusanta kanka Dani don Babu Hadi......... "Ni kuwa a yanzu kusancin nake nema gareki don bana ko shakka munyi musayar zuciya don ko baki fada ba nagani a idonki so karki damu Ni dake zamu zamo Abu guda....... Bata jira ya Kare maganar shi ba ta soma tafiya Yana biye da ita da yaga bazata tsaya ba sai ya fito suka jeru suna tafiya Wai zaiyi Mata rakiya ai kuwa sai gashi ya kawota har gida ta shiga shi kuwa ya dawo tun daga wannan Rana yake biyota su taho tare ya kawota har gida shi Kuma ya juya Ta dawo inda ta samu eng AK yayi Baki Wanda Mubarak ke fada Mata Wai Mr President ne yazo wurin abban su Eng ya karbi bakuncin Mr President Wanda suka gaisa yake tambayar shi Ina ya shige aka Daina Jin duriyar shi ya bashi amsa da ya na Nan yanayin Rayuwa ne "To madallah Zan neme ka Amma kafin Nan wata Alfarma nazo nema idan har Allah yayi lamarin Dama yaron wuri na ne Anwar yaga Yar wurinka yake so shine yace nazo na Yi maka magana idan bakayi Mata miji ba ya shigo cikin masu nema Amma don Allah kar ka kalli girma na ko alfarma ta ka tursasa yarka akan auren Anwar don in har Bata son shi to zai hakura ne ko da kuwa zai mutu don haka kar kace zaka bawa Anwar yarka don Ni ba zanso hakan ba idan ta na sonshi zanyi murna idan kuwa Bata sonshi zanyi musu fatan ALHERI ne kawai don muna da Matan da muka zaba mishi Ni da uwar shi ya Kuma yi Mana biyayya to yanzu ne yaga wadda hankalin shi ya kwanta da ita itace yarka shiyasa zanyi mishi Alfarmar aurenta idan har Allah yayi wannan shine makasudin zuwana. AK yayi shiru kanshi akasa Yana nuna girmama wa ga Mr President inda yaji yayi na am da Anwar ya zamo mijin ummita don tarbiyar shi tana burgeshi tamkar ba Dan wani ba Kuma atsari ma yasan ummita zata so shi don yafi badamasi nesa ba kusa ba .har ga Allah ba don abin duniya yaji Anwar ya kwanta mishi fiye da badamasi ba sai don ya zabawa Yar shi miji na gari Amma ko shi din ummita zatace Bata so zai bawa Mr President din hakuri yaro ya nema agaba Ya dago kanshi Yana duban Mr President "Sir Babu matsala Anwar Nima Dana ne zanso ummita ta karbi auren shi duk da nasan Bata da matsala da nace ta karba zata karba Amma a turo Mata Anwar su gana su Kuma daidaita idan da Rabo Amma daga gareni ma Zan iya cewa na bawa Anwar auren ummita sai fa idan Allah ne Bai kaddaro hakan ba. Mr President yayi murmushi "Nagode sosai abdulkarim da goyon bayan da kabani Zan Kuma turo Anwar yazo su gaisa fatan Ubangiji yasa ALHERI zamu hada Da haka sukayi sallama yayi mishi rakiya har wurin motar shi sai ga kyauta ta girma anyi mishi Amma yace ba zai karba ba inda aka aje mishi motar ta fice ta barshi Baki sake Dole ya karba ya shigo cikin gida Yana fadawa lubabatu yadda sukayi da Mr President Akan son auren ummita Ta dubeshi azabure Cikin wani kallo me bayyana takaici "Shine suka Fara siye imaninka da dukiyar su? Ta fada Yana nuna kudin da hannunta abinda ya kona mishi Rai ba kadan ba ya dubeta cikin mamaki "Nayi Zaton ko wani ya fada Miki haka Zaki karyata lubabatu in siyar da yancin ya ta Akan kudi kike nufi ? "Ba Zan ma karyata ba abdulkarim don nasan talauci Babu abinda baya sawa ba zai zamo abin mamaki ba don ka siyar da mutuncin yarka akan kudi da abin duniya ba..... 'sai dai kasani Nima inada hakki akan ummita don haka ban yarda ba ba Kuma Zan yarda ba. Idan har kaci kudin su saboda aurenta to ka kwana da Shirin biyansu. Yaji wani yaji yaji Yana lullube kwayar idon shi Wai don ya talauce ne lubabatu ke son kece rigar mutuncin shi ne kokuwa akwai abinda yayi Mata Wanda ya fusata ta har take mishi wannan dibar albarkar? Ganin idan yace zai biye Mata Kan batun to rayuka ne kawai zasu baci sai ya fito daga dakin nata hakki dai da take magana nata ya Bata tunda ya sanar da ita Yana Duke Yana faman wankin kayan su Mubarak ummita ta shigo da sauri ta aje takardun ta "Abba da Ranar Nan kake wanki? To kawo na karasa maka Ta fada tana kwabe hijabinta Yayi murmushi "Jeki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31