Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kama mun hadu shima ma gaisa don ba Zan yaudari kaina cewa zaka zo gidana sada zumunci ba Toni a wa? Da haka malam Ali ya fice ya bar Kabir da hada hudu da ukun da zasu bashi takwas Izzatu da taji batun itama taji Babu Dadi Amma sai tace addua kawai zasuyi itace mafita Yayinda humaira fulani taji ya kakar tata ta Bata kuka take tamkar dai izzatu ce ta Bata abinda ya Bata ran izzatu ta shiga zazzaga Mata masifa Kwana biyu Kabir ya watsar da batun dungo inda yace duk ma inda ta SHIGA zata fito idan Kuma tayi haka ne don ta tada mishi hankali to ta tada mishi Bai samu zarafin duba kunshin da takardar ba ya kwashe su ya watsa ciki kabit din ajiyar takardun shi Kwana biyu ummita na zuwa kuki cafee kasa saboda Babu kudin da zatayi transport din zuwa gashi saura wata biyu ta Ida ta karbi sakamakon Tana tafe anatse inda kamar daga sama Wilson ya hangota zata ketare titin da zai sadata da kuki cafee inda ya zuba Mata ido a yau ji yake tamkar idan baiyi Mata magana ba zaiyi Rashi na zuciyar shi sai dai kafin ya faka motar ya fito har ta shige Ya kasa tsaye da zaune zuciyar shi na kawo mishi shawarwari akan kawai ya jira ta fito in yaso ko mayar da its gidane sai yayi Aiko ya dasa zaman jira har uku na maraice ta fito ta soma tafiya inda ya kula tamkar Bata da lafiya Ta gota shi kadan ya ga ta dafe bishiya ta rike kanta Wanda alamu suka nuna ciwo yake Mata inda dabara ta fado mishi ya tashi motar ya karaso gareta Yana fitowa Ya tunkaro ta ta zuba mishi ido kallo daya ta Gane shine Wanda ya tsura Mata idon Nan a country mall Yayi Mata sallama cikin hausar shi da Bata fita Bata amsa ba ta dai dubeshi "Sannu fa Naga kamar kina neman taimako na?...... Tayi saurin Kada mishi kanta "No nagode zaka iya tafiya. "Kiyi hakuri nasan inda zakije akwai nisa kizo na kaiki Naga kamar kina headache ne ...... "Nagode sosai Zan iya komawa ba damuwa........... "Kiyi min alfarma ko ta kaiki gida ne tunda har Baki da lafiya.......... "Idan aka ganni a motarka nace me? "Ka ganka kuwa ? "Taimako wani abune da addinin mu ya koyar damu ga mabiyan sa shin kana daga mabiyan ne da zaka taimakeni? "To duhu da haske basa tarayya a wuri Daya Dole daya ke bawa Daya wuri idan haske ya bayyana to duhu yayewa yake don haka na gode da taimakon ka gareni "Na sani amma haka Nan naji Ina son taimakon ki tunda muma namu addinin ya koyar damu taimakon Kuma Bai saka kiyayya ga sauran addinan ba indai ba naku adfinin ya saka muku kiyayyar sauran addinan ba. Kiyi hakuri ki shigo na saukeki nayi Miki alkawarin Babu cuta tsakanin mu haka kawai nake son taimakon ki Azahiri ita kanta tana bukatar taimakon don Jin kanta take tamkar zai tarwatse Dole ma ta nemi abinda zai kaita gida don Bata sababa ga kuma yunwa da takeji wadda idan akasa tace zata tafi to ko shakka Babu sai dai akwashe ta amika gidan don haka ta sallama ta shiga motar yaja suka iso gida ya sauketa ya Miko Mata fakitin maganin ciwon Kai me tsadar gaske ta karba tana godiya Tun daga wannan Rana Bai Kara shiga cikin lamarin ta ba sai dai zai labe ya kalleta ya more ya koma gida inda kusan kullum sai yazo kuki internet cafee ya ganta batare da ya Bari ta ganshi ba Hajiya sabuwa first lady matar Mr President take sanar da Mr President din maganar da ta taba fada mishi ta samowa Anwar auren diyar kawarta matar soja wato kudusiyya ta taso don haka atura mutane su nema mishi auren Ya dubeta Yana murmushi "Kice auren gata za ayiwa Anwar ba na fada Miki Yar gidan Kabir mashi Nima na nema mishi ba? Ta kwabe Baki da zaka yarda sai ince ka bar maganar Yar gidan Kabir mashi kudusiyya macece daya tamkar da goma......... "Ba zanyi magana biyu ba tunda dai kema kin samo mishi wata sai ahada mishi biyu don haka itama Yar gidan Kabir mashi din sai muyi magana kawai Wannan abin ya Bata ran haj sabuwa don tasan idan matar soja taji haka ba zata yarda ba Amma kome kenan zasu San yadda sukayi suka lalata Shirin Yar gidan Kabir din don kudusiyya kawai suke son tayi Rayuwa a gidan Anwar din baza ta tabs Zama da kishiya ba bare har ta Zama Bora Sai dai da Anwar din ya shigo hajiya sabuwa ke mishi maganar kudusiyya da zaba mishi ita da tayi a matsayyin matar aure yayi saurin tareta..... "Bana son ta hajiya ku barni na zabo matar da Nike so da kaina tunda Kuma zabar kanku kukayi ke da dady ba hada ku akayi ba....... "Kayi karya ka bani kunya Wallahi Anwar Dole ne ka auri kudusiyya..... 'to shikenan haj duk abinda ya samu Yar mutane kar kiyi kuka da kowa...... Ya fice ya barta sake da Baki............... [5/24, 7:50 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 38* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Anwar ya fito sukayi kicibus da mahaifin shi ya zube Yana rattaba mishi abinda hajiya sabuwa ta fada mishi akan Wai ta yi mishi Mata da kudusiyya wadda shi atsarin shi kudusiyya batayi mishi ba. Mr President yayi murmushi "In Banda abinka Anwar meye na damuwa don ta zabo maka matar girma ? Nima fa nayi nufin Yi maka gata kanaji? "Eh inaji dady. Yauwa ai kasan gidan Alh Kabir mashi ko? Eh gaskiya kamar na sani Amma dai akwatanta min . Yayi mishi kwatance ya Kuma Gane inda ya bashi rafar dubu hamsin hamsin guda biyu ta dubu dari yace idan sun gama magana ya bada amatsayin kyauta Ya dubi uban cikin Rashin Gane abinda yake nufi har dai ya tambaya "Dady wa za a ba wannan kudin shi alh Kabir mashi din? "A a kaje Zan kirashi zamuyi magana bashi zaka bawa ba ita wadda zaku yi maganar da ita zaka bawa amatsayin kyautar ka. Ba don ya Gane ba ya taho don har ga Allah shi Bai kawo komai aranshi ba yayi nasarar Gane gidan ya Kuma tura me gadin yayi mishi sallama da alh Kabir Atare suka iso inda Kabir kewa Anwar sannu da zuwa ya sauke shi a wurin da yake karbar Baki suka gaisa inda Anwar din yake sanar dashi dady ne ya turo shi "Eh ai ya kirani bayan ka taho Bari in turo maka ita. Ya Mike ya bar Anwar sake da Baki Yana maimaita kalmar Bari in turo maka ita, to itawa za a turo mishi? Sai ya zuba ido kowacece itan Fulani na zaune cikin ado da kwalliya tamkar me shiri fita party ta zubawa TV ido tana kallon India Wanda take son sanar da dadyn ta tana izuwa India don garin na burgeta sai Kuma gashi ya shigo

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});