Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hajiya Amma Nima ba Zan yarda ki fada min maganar da zata dameni ba kija bakin Ni Kuma Zan fassara Miki kowane kalar ciwo Zan fada Miki kalar maganin tunda na kula shekawa jaki shayi aikin banza ne ba iya Sha zaiyi ba.... "Ki Fadi komai damar kice Amma na rantse Miki sai an kawo wata mace agidan Nan wadda zata haifa Mana yara wallahi na gaji da sai dai kici ki kasayar "Ai hajiya Ni tuni na gano kece Baki gano ba kice Rabon a bankado abinda zai saka zuciya tashi Baki taba tambayar ko shi Dan naki ne ke da matasala ba sai dai Ni kuke kallo? To za ayi duk yadda kike so tunda watan da za ayi magana ya Kama wallahi za ayi magana Don haka yanzu sai kiyi hakuri baya gari Yana can kasar waje neman lafiyar da zata bashi Yan dagwai dagwai din da kike magana idan ya dawo sai kizo kuyi maganar kafin lokacin Ni na Dade agidan mu tunda nayi kawaici nayi hakuri ba ku San nayi ba to Ak ya dawo Ni kuma ya sallame Ni Hajiyar tayi shiru tana tauna maganar izzatu kar dai matsalar daga AK din ne na Rashin haihuwar? Karfa allura ta tono garma Kai Bata zaton hakan Kuma ko daga gareshi ne ai akwai magani sai agwada. Da haka hajiyar ta taso inda talai tayi Mata rakiya har wurin motar ta suka tafi ita Kuma ta juyo inda Kuma izzatu tace dawa Allah ya hadata ba da talai ba? "Kinje kun zageni ke da hajiya to in zata burgeni Mata hudu ya kamata ta aurowa ak haihuwa Kuma sun Dade basu haife mishi singa da kasuwar kurmi ba Haka tayi ta sababi tamkar zata aro Baki ta hada da nata talai dai ta wuce daki ta barta Kwana biyu tana cikin takaici da bakin cikin da hajiya Mama ta guma Mata inda take ta jiran zuwan me gidan don ayi ta ta Kare Wai ramamme ya zagi maye Ya Kira wayarta yake sanar da ita kanwar shi asma,u ta haihu har gobe ake suna hajiya Mama ta kirashi ta sanar dashi inda ya bukaci ta dauki kudi dubu hamsin ta kaiwa asmau kudin aski "Gaskiya ba zanje ba ak sai dai na tura talai ko harira Amma Ni dangin ku nayi wuri na aje su gaskiya saboda nagane basa kaunata........ "Babu komai tunda har Kika iya fada min kinyi wuri kin aje dangi na na gode....... Dit ya tsinke wayar inda Kuma taji lallai Bata kyauta ba kamata yayi ta amsa mishi da to in yaso sai ta tura wani kawai don haka sai ta Kira wayar tana bashi hakuri cikin kissa da kisisuna har tana fadin tayi kuskure yayi hakuri da haka suka aje wayar t Washe gari ta nufi gidan Asma u inda ta tabbatar ba zasu kwashe da marar arzikk ba musamman dangin shi dake da burin yada Mata bakar magana to yau Suma zata nuna musu uwar su ma dai dai take da ita bare su kanan shegu Da haka ta fice ta iso gidan sunan Wanda ya ciki ya batse da Yan uwa da abokan arziki ta fito mota tana shakar iska dai dai inda ta hade fuska don kar su Raina ta....... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 3* *___________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *__________________________________* ...Sanye take da leshi me kalar ruwan kasa me cizawa wato coffee brown kafarta sanye da takalmi me tudu Wanda ya Kara Mata tsayi hannunta cike da warwaraye da zabban zinariya yayinda kwalliya ta taimakamata afuskar ta don in baccin kwalliyar to da ba zata kallu ba ahalayya Kam taci sunan ta izzatu don izgili da dagawa ba a magana hakama Bata Faye shiga mutane ba saboda tana ganin ta zarce hada kafada da mutane musamman idan Basu da kumbar Susa don kuwa mijin da take aure eng abdukarim fitaccen Dan kwangilar dake samu kwangila daga gwamnatin tarayya Wanda sunan shi ya tumbatsa aduniya shine barazanar ta da homar ta sai dai inda matsalar ta take shine tsayin shekaru Bata haihu ba inda har dangin shi ke yada Mata magana da habaici da arashi karshe ma said ga hajiyar shi da kanta ta wanko kafarta ta wanke ta soso da sabulu inda itama ta daura damarar yakar duk Wanda yace Mata kulle zata ce mishi Cass Ta shigo gidan sunan inda ta iske ana ta sabga ta dauke kanta tana hura hanci Da yawan Matan dake gidan suka bita da kallo suna kallonta awatse itama tana musu kallon sai dai aganni abarni ko Kuma bakin ciki ya kashe mutum. Kai tsaye ta shiga dakin me jegon Wanda yake cike da Yan uwa da dangi Tamkar wadda ta shigo cikin wata najasa haka take ta shakar hanci tana dauke Kai inda asmau take kallon ta tana mamakin daukar kanta Bata gaishe da kowa ba ta jawo kudin ta mikowa asmau "Gashi inji AK yace akawo Miki Yana Miki barka ta Mika mata tana dauke Kai. "Madallah na gode inji asmau ta fada tana Miko Mata jariri Shafa tace "Kai Yaya ak ya soma rage kyauta ba kamar da ba....... Samira ta karbe da fadin "Yaya eng ba zai rage kyauta ba wata Kil dai sauran kudin ne sukayi dimuwa Yar gidan ikon tashi ta na baza irin wannan ikon Allah yaushe zaiyi abin kuzo ku gani? Samira tace Ni wallahi Ina tausayin shi bawan Allah kowa da danshi Amma shi Babu Kuma an rufe mishi idon ganin gaskiya..... Ke dai Bari Yar uwa sai dai aci akima katon Kashi a hau mota ashiga gari ana hura hanci Ni wallahi har gobe mamaki nake yayun mu sunyi Rashin dacen Mata mu Kuma mazan mu sunyi dacen Mata.... "To ko kina da Sha awa ne akan yayan naki shafa? Cewar izzatu da tagaji da Jin shaguben su "Me kike nufi da ko Ina da Sha awa? Inji shafar, Izzatu tace "Wai ko ki aure shi nake nufi tunda Ni na tsare muku gaba na tsare muku baya tunda kina haihuwa kawai sai ki kaso auren ki kizo kuyi Maja Kinga sai kema ki biyo layin masu sa ar mijin harma ki yi abinda nakeyi. Sai suka harzuko Mata su duka tamkar zasu cinyeta. "Me kike nufi da wannan maganar? Dama kinzo don kici Mana fuska ? To aikuwa Wallahi jikin ki zai gaya Miki zakuma ki Gane karyar iskanci kike... Izzatu ta Mike tana aje jaririn "To Bari agano Yan iska tsakanin Ni da ku ai a yanzu dai dai nake da uwar mutum ma da uban shi bara ku gayyar na gayyaro "Eh kice dama da abinda ya kawo ki yau har hajiya ta samu tukwaicin zagi gareki ? Sai saka soma musayar yawu har an daura damarar dambacewa inda shafa ta rarumi izzatu suka soma dambe har suna yagawa juna sutura inda a karshe sukayi Mata taron dangi har suka fasa Mata goshi . Inda gidan suna ya hautsine wasu suka shiga tsakani izzatu ta taho da Alwashi kala kala Alwashin karshe shine rabuwa da

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});