Chapter 23
Chapter 23
sai Yan Wanda ba za a rasa ba................... "Alhamdulillah tunda dai Basu taba kowa ba sai mu dage da addua Ubangiji yakiyayeka dukkan sharri ya Dora ka Kan makiya suka amsa da ameen da haka hajiyar ta koma gida tana ADDUAR Allah ya Kare Mata danta. Hon bello Rimaye ya soma budewa sister mero bakin aljihunshi akan son auren humaira fulani inda meron ke shirya yadda zata tunkari izzatu Amma acewar ta sai ta tatsi hon yadda Koda izzatu zata nemi kawo Mata wargi Wilson kuwa ya kasa samun nutsuwa don muddin zai runtse idon shi to Babu shakka zai hango ummita bare kuma yace bacci zaiyi kaf burinshi da tanajin shi zai Kare ga mafarkin ummita abinda ya tabbatar sonta Bai Kama shi don ya sake shi ba yayi zaton abin nawasa ne amma ya Gane yafi karfin wasa Gaba daya ya fice hayyacin shi har ya Daina fita ko Ina ya kwanta jinyar ciwon so Zuciyoyin shi sukayi ta kawo mishi shawara bi da bi har dai ya yarda ya dauki shawarar karshe ta yaje kofar gidan su ummita ko da ganinta ne yayi ya rage radadin sonta Ai kuwa ya Mike ya fice sai gashi kofar gidan su ya faka motar can gefe ya dawo nesa kadan da gidan ya zauna Yana zubawa kofar gidan ido Zaman shi ko minti talatin ba ayi ba ta fito cikin motar ta tafice inda ya bi motar da kallo ko ba komai yaji sanyi tunda akalla dai ya hangota inda wata zuciyar ke fada mishi yabi bayan ta zuwa inda zataje ko ba komai zai Kuma ganin ta ai kuwa ya dauki motar yabi bayanta inda suka hadu a traffic wadda ta tsaida su ya juyo Yana kallon ta inda yaga tsantsar kwarjini da haiba inda ya tabbatar ita din me kyau ce Jikinta ya Bata lallai ana kallon ta sai ta waigo inda idon su ya hadu yaji wani Abu me kama da Jan shock ya fizgeshi ita Kuma tana kallon shi ta tabbatar shine me kallon ta sai ta dauke kanta danjar ta Basu hannu suka wuce inda bisa Dole ya koma gida inda yakejin ya samu hanyar rage kewa Da yamma ya fito da zummar siyo kayan shayi ya wuce ta kuki cafee inda ya hango ta tafito daga kukin rungume da takardu ta bude motar ta SHIGA ta ja ta nufi gida Atake ya Gane kuki ta fito zuwa dazun me yuwa computer take karanta Ya wuce abin shi itama ta wuce batare da tasan yanayi ba Satin da gambo mafiyas ya dawo daga Lagos ya Kuma samo abin duniya Wanda suke karewa ga Matan banza da kayan maye don basa tsinana abin arziki don haka ya Isa gidan izzatu Yana zukar tabar iblis wiwi Da sauri ta toshe hanci tana tofar da yawu "Haba gambo meye haka zaka shigo min da wannan shegiyar tabar me warin Kashin jaki? Don Allah koma waje ka zuke abinka ko dadin me kukeji acikin zukar hayaki hayakinma irin wannan da ko dadin Shaka Babu?..........."yi hakuri hajiya kan ne in Babu hayaki fanko ne Rayuwa ta in Babu mandular Nan akwai damuwa har Rashin lafiya nake kwantawa idan ban busa ta ba Ya murtsuke sauran ya saka aljihunshi "Yauwa to haka dai yafi don har kaina ya soma juyawa Nima ka sakani kwalewar Dole "Yauwa hajiya Ashe akasi aka samu wurin aiki? "Ai shiyasa nafi yarda da aikin ka yanzu Yaya za ayi kenan? Ki bar komai a hannu na hajjya Ina me tabbatar Miki Nan da Rana irin ta yau wancan mutumin ya SHIGA UKU ke dai ku tanadi kudi don kin San Ni bana tare da tsautsayi ko kuskure bare wani Abu Wai shi sabani....... "Karka damu gambo idan aiki yayi kyau ma za a biyaka kudi lunki uku Kai dai baje basirar ka kayi aiki me shegen zafi don ka samu sallama me kyau.... "Angama hajiya bani sati guda Daya kacal zakiji mugun albishir da haka sukayi sallama ya fito ya Kama gabanshi inda izzatu ta Kira Kabir take sanar dashi yadda sukayi da gambo mafiyas yace yayi daidai Kuma zai biya gambon lunki hudu ma ko biyar matukar dai aikin shi yayi sanadin fakuwar eng AK Cikar satin da gambo mafiyas ya diba yayi daidai da kammaluwar aikin shi inda ya Kira Kabir yace yaje wurin hukuma ya sanar da akwai wani da yake kisan yaran mutane yau ya kashe wata yarinya ya sako a motar shi don haka su tashi Jami ansu da binciken motocin mutane ta haka ne tarkon zai Kama eng AK. Aikuwa atake Kabir mashi kashe arna ya Kira wayar D P O ya sanar dashi abinda gambo mafiyas ya sanar dashi inda Kuma suka tashi Jami ansu aka soma checking point Wanda duk motar da zataje ko tazo sai me ita ya fito ya bude but sun caje komai kafin su bashi izinin tafiya Bawan Allah eng abdukarim ya taho batare da sanin mugun qullin da aka hada mishi ba ya taho inda ya iske dogon layin na checking point Wanda ake ta bincike motoci shima ya bi layi batare da sanin shi ake son ganin baya ba ba Kuma Wai idan yajuya zaiyi tafiya ba. A a ganin baya na har abada inda ake son kasa ta rufe idanun shi................ Ubangiji kayi Mana sutura kar ka Bari makiya suga bayanmu 🤔 [5/22, 7:24 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 33* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Sannu ahankali akazo Kan eng AK Wanda ke kallon yadda ake binciken motocin mutane har akazo gareshi "Ranka ya Dade muna son duba cikin motarka idan Babu damuwa....... "A a Babu komai yallabai Bismillah ya fito Yana daga musu cikin motar suka bincike ba su samu komai ba sukace ya bude musu but Ya kewayo ya soma kokarin bude but din Amma wani abun mamaki tamkar an sakawa but din kwado yayi yayi ya bude Amma yaki buduwa yayi iyakar kokarin shi Amma but ya ki buduwa ya dubi Dan sandan Yana sharce zufa "Ranka ya Dade wallahi yaki buduwa karfen nasara kenan ban fa Dade da budeshi ba Amma yanzu da yake so ake ya bude yaki da zaku yarda sai ince muku babu komai aciki............. "A a ranka ya Dade a dai bude don Rana tsaka aka tashe mu aikin Nan .............. Ya Miko mishi key din motar "Karbi to ka gwada kagani Ni dai na gaji gaskiya, Dan sandan ya karbi key din ya soma kokarin gwada tashi sa ar inda ya turza sosai kafin yayi nasarar bude but din cikin sa a Kuma ya hango wani Abu me kama da jini na bin wani tsumma dake kudun dune yajawo shi ya warware inda yaga wani Abu me kama da hannun mutum inda kafar mutum ta fado Kuma wani Abu ya fado me kama da kokon Kan mutum Eng AK ya zaro idanu Yana mamakin yadda wannan alamarin ke Shirin faruwa ta Yaya akayi wannan abin ya shigo motar shi Inda Dan sandan yake kallon eng abdukarim da mamakin wannan abinda da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31