Chapter 20
Chapter 20
an bani nawa Ina Kuma Ina tsoron taba mishi dukiyar shi don nasan hadarin dake tare da cin dukiyar maraya aka Kuma sanar dashi na yafe mishi Amma yayi sannu da wannan Rayuwar. Ta Miko mishi tsohuwar takardar "Wannan Kuma sadaukarwar da nayi mishi ce wadda shi ya kasa yi min irinta itace rubuce aciki ya karanta ko don ya Gane Ni naso shi tun kafin ya shigo duniya Amma shi duniyar ta rudeshi ya watsar da lamarina . Ta fada da hawaye na bin idonta Malam Ali ya karbi kudin da takardar Yana dubanta "Lallai uwa da Da sai Allah dungo kina aje da kudi kina fama da rainon yaran da ake biyanki ki cida kanki kina tanadawa Dan da yake can Yana more Rayuwar shi baya ma sakoki a lissafi. Zan cika Miki wannan alkawarin Zan Kuma kiyaye da ko duba takardar ba Zan Bari wani yayi ba bare ataba mishi kudin shi ke Kuma Allah ya Baki lafiya Ta amsa da ameen "Nayi maka izini ka duba takardar Nan malam Ali ko don kaima ka San abinda nayiwa kabiru Amma shi ya kasa yi min irin shi na yarda ka duba ai Ni da Kai mun Zama Daya Malam Ali yaji Yana son duba takardar ko don ya fita daga zato Ya bude takardar ya soma bin rubutun cikin ta Yana karantawa dogon rubutu ne har ya gama karance shi tsab inda hawaye ya kece mishi Banda Yana da karfin hali da Babu abinda zai Hana shi kokawa Dungo ta dubeshi "Ban San lamarin zai motsa zuciyar ka ba da bance ka karanta ba......... "Dungo Anya kuwa kabiru na son gamawa lafiya? Anya kuwa Yana son DUNIYA da Rayuwa su barshi Zama cikin salama? Kinyi kokari Allah ya biyaki da ALJANNAH kin Kuma fita hakkin shi shine ya kasa fita naki Ya Mike ya fice tun Bai durawa kabiru ashar ba. Haka ya wuni Yana mamakin yadda wannan yaro da abinda ke Rudin shi Haka Jamila ta wuni zaryar dubata da girka Mata Dan abin tabawa inda da Rana ta girka Mata wake da Yar anta ta kawo Mata inda ta isketa ciwon ya taso abin sai da yasaka Jamila hawaye ta tallabota ta Dora kanta bisa cinyarta inda taga kamar tana Suma ta soma shafa Mata ruwa afuska har ta kawo numfashi ta farko cikin wani irin yanayi me kama da son wucewa kiyama inda Jamila ta tashi don ta taro mota su wuce Asibiti Ta samo me napep da kyar saboda wahalar da napep din keyi ta iso gidan inda ta iske wani bakon Al amari me kama da mafarki "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Ina dungon ta shige ? Ta duba gidan kaf Amma Babu dungo Babu dalilin ta Ta ci gaba da karade lungu da sako na gidan Amma maganar guda ce Babu dungo Babu dalilin ta Malam Ali ya shigo shima Yana son duba dungon Amma ya riski lamarin me kama da almara Jamila kuka take tana karawa inda malam Ali ke tunanin ko dai rijiya dungo ta fada saboda bakin cikin abinda danta ke Mata? Don haka yayi maza ya bude rijiya Yana dubawa Amma Babu ita Sai aka shiga nema da Jaje da duba asibitoci Amma Babu labarin dungo har dai daga karshe aka barwa Allah lamarin inda aka rufe gidan dungon Wanda hatta wayarta Bata dauka ba komai Yana Nan abinda ke Kara saka baba Ali zubar hawaye shine abinda ya dauki dungo shin wani ne ya dauketa Koko ita ta gudu da kanta ? Idan ita ta gudu ina ta tafi to? Idan Kuma wani ya dauketa meye hikimar daukarta? Haka malam Ali ya rufe gidan ya na tunanin Ranar da zai iske Kabir ya isar mishi da sakon uwarshi.................. [5/21, 5:47 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 29* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ......... Aguje fulani ta sheko akan titin tamkar zata tashi sama inda ta wuce wata hamshakiyar mota wadda ta rasa gano inda ta santa. Atake ta gano motar gayen Nan ce da yayi Mata Rashin mutunci Ai kuwa da sauri tayo rubos ta dawo inda taga ya faka motar shi zai siyi tuffa da inubi Ta fito tana sanye katon gilashin ido Wanda ya mamaye fiye da Rabin fuskar ta tana sanye da doguwar Riga ta yadin material lemon green anyi mishi adon fulawowi ja da Baki tayi kyau sosai ta yafa mayafi Dan karami Wanda Bai rufe Mata dogon goshinta ba Wanda iska ke kadawa tamkar kwallo Kai tsaye ta tunkar me kayan fruit din tana takawa tamkar me tafiya akan kwai. "Malam bani aybar Nan ta dari biyar ta fada tana Mika mishi gudar naira dubu Ya karba Yana saka Mata aleda ta Ciro guda biyu tana barewa inda Anwar ke kallonta Yana mamakin yadda take mishi kallon da wa ka shigo garin Abuja? In har ya fahimta dai dai ma sai da yaga bakinta na motsi duk da baiji abinda take fada ba Amma yayi sa ar jiyo tsakin da tayi Me fruit din ya Miko Mata cikon dari biyar dinta ta dubeshi ba tare da ta karba ba. Ta Nuno Anwar dake zaune cikin mota Yana kallon ta "Ka bawa wancan matsiyacin sadaka don nasan irinmu irinmu ya ke jira yayi maula ta fada dai dai da ta jefa mishi bawon ayabar afuskar shi Daya daga cikin masu biye dashi don bashi kulawa wato body guard dinshi da ya kula da abinda tayiwa uban gidan su ya daga hannu zai sharara Mata Mari Amma da sauri Anwar ya dakatar dashi. "Da dai ka barshi ya mareni ya Maro ajalin shi jaki da shi Yana biye da jaki Dan uwanshi, Ta bude motar ta tashige ta figeta aguje ta hau titi inda wani hamshaki da abin ya faru akan idon shi yaji ya mutu da son fulani don shi Allah yayi shi da son mace me tsiwa tana burgeshi don haka da sauri ya shiga tashi motar ya rufa Mata baya inda suka bar Anwar Yana mamakin wannan yarinya daga karshe dai yayi murmushi ya siyi abinda ya kawoshi ya wuce gida Sister mero tayi sallama gidan izzatu tana murmushi inda izzatu ta fito tana nunata da yatsa , "Ina fatan kinyo wankan gawa kin Kuma taho da likkafanin ki don Ina me tabbatar Miki dab kike da kushewa.......... "Wai Ni na mutu yanzu izzatu? Kai bana zaton Koda kuwa zanyi ido hudu da mutuwar to Zan roki tayi min alfarma in gama dake tukuna ta dauke Ni , ai Ni in kin ganni lahira kaini akai don haka SHIGA ki fito kudi nazo karba......... "Saboda gyatumin ki ya bani ajiya? "Ko daya gyatumi na Bai Baki ajiya ba Ni dai na Baki ajiya.......... "A gidan ubanwa Kika bani ajiyar? Ke mero ki fita idona wallahi na rantse miki in Kika kaini karshe Zan iya murde Miki wuya ki mutu murus ! "To Bismillah ai ke da kanki kinsan Ina da kaddara a wurinki itace humaira inda kikayi kuskure da tun farko kikace Lada Zaki biyani da cewa kikayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31