Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

taji an fizge jaririyar dake hannunta tana kallo akayi sama da ita Ta kuma kwallara Kara kafin ta farka.... Ta farka inda take jiyo hucin wutar na bin jikinta Babu batun ADDU A irin ta Wanda yayi mugun mafarki don gaskiya Bata iya ta ba sai ta shiga laluben fassara mafarkin ta Da taso gaskiya koma ace da Dan guntun sani akanta to zata Gane wa azi ne da izna akayi Mata tunda tagani ta samu yarinya Amma hayaki da wuta sun biyota akwai kura kenan Kuma lubabatu da tagani da ak in batayi sannu ba zata barwa lubabatun ak da filin gidan ta Amma sai batayi wannan hasashen ba sai kawai ta kalli mijin da tagani amatsayin Wanda zata haihu dashi sai ta haukace ta Kuma tada bular lallai sai ak ya sauwake Mata auren shi Ta nufi dakin shi don tuni suka Raba makwanci don tace bataga amfanin zuwa dakin nashi ba sai ta fito da tsiya taku kala kala inda Kuma tafi sauke tsiyar ta Akan tsohuwa talai. Ta shiga dakin ak din Yana tsaka da bacci yaji ta antayo mishi ruwan sanyi ajiki gashi lokacin sanyi ya farka afirgice Yana shissheka ya dubeta tana Kada jiki da son ta fashe Ya dubeta cikin sanyin murya "me ya farune izzatu",? "So nake ka tashi ka sallame Ni don na gaji gaskiya ba Zan Kare a auren da Babu tsiyar da zai tsinana min ba........ [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 7* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ......... Ya share ruwan dake yarari akan fuskar shi Yana murmushi Yana kallonta "Izzatu Allah ya sani Ina Jin tausayin ki Zan Kuma Kara hadaki da Allah da manzon sa ki bar maganar Nan haka...... "Kar ka Kuma Jin tausayi na Kai ne abin tausayi ba Ni ba don Ni na hango mafitata a mafarki don haka sallame Ni kawai in Kama gabana. Yayi murmushi "Abinda Kika gani a mafarki ba lallai ya zamo gaske ba sai dai nuni ko izna don Allah kiyi hakuri ki barni nayi barci na kaina ciwo yake, Ya kwanta ya barta tana jijjigar jiki idonta fal masifa ta fito tana sababi inda ta iske tsohuwa talai zaune tana Gyan gyadi sai kawai ta shara Mata Mari Abin tausayi tsohuwar ta farka afirgice "Wane irin dabban cine ki share wuri ki zauna kina min bacci da tsakar Rana? Ke Bari fa kiji in fada Miki idan kinji kin gaji da aikin Nan babu lallai Babu tilas na gaji da gayyar hakora in kin gaji sai na sallame ki Ta shiga zubar da ruwan tijara inda tsohuwa talai hawaye ya tararo Mata tana ta ahi da neman afuwa Jin Marin da izzatu tayi wa talai yasa ak fitowa ya na kallon yadda take Mata tijara ranshi ya baci matuka gaya don Allah yasaka mishi son tsohuwa talai don asali talai wurin hajiya Mama take aiki shine ya matsa da sai tsohuwa talai ta dawo gidan shi don ya Saba da abincin ta tun da sauran karfinta tayi aiki a gidan su shine mafarin tsanar da izzatu tayi Mata saboda tana ganin an turo tsohuwar ne don ta saka Mata ido ko da take wulakanta masu aiki tafi wulakanta Talai Ya karaso wurin ya kamo hannunta ya tada ita inda yaga hawaye na bin idonta "Kiyi hakuri talai Ni naji Miki Amma ban San haka kike muskanta ba . Ya dubi izzatu cikin wani irin fushi da Bata taba gani afuskar shi ba "Baki ji kunyar cire hannu ki Mari tsohuwa irin haka kamar talai ba? To ya zamo na karshe da Zaki Kuma yiwa wani ma aikaci a gidan Nan bare talai. Talai kamar Uwata ce daga yau kar ki Kuma sakata ko shara bare wani aiki na soke Mata duk wani aiki sai dai agirka abata...... "Wannan ne Kuma baka Isa ba wallahi muddin Ina gidan Nan to Dole ne tayi aiki ba tsufa ba ko mu kwana lafiya ce . Dama na Dade da ganota tsohuwar muna fukace wadda aka turo don tazo ta saka min ido to aiki ya Zama Dole tayi shi ko Kuma jikinta ya Bata Labari wallahi salon kasa ta kalli kanta a wata tsiya kace sai dai agirka abata ita a way? Bai San lokacin da ya faska Mata Marin ba karon farko a tarihin Rayuwar auren su da ya taba Kai hannu jikinta da sunan duka abinda bai taba yi ba. "Ba Zan taba Bari ki wulakanta tsohuwar da Ni ne na kawo ta gida na ba Akan talai ba sai kin roki saki ba Zan Baki shi jahilar banza wadda Bata San kimar tsoho ba. Idan har ka girmama tsohon wani to naka ka martaba don hak sai ki kiyaye ba Zan lamunci wulakanta mutanen dake kasanki ba...... Ta cakumo kwalar rigar shi ta tattare ahannun ta "Tunda har ka mareni akan wannan tsohuwar banzar ai kasan ta ballowa kanka aikin da ba zaka iya dashi in yaso sai ka auri talai ko hajiya mama....... Ya Kuma Bata kyakkyawan marika guda biyu ajere Wanda yasa taga wata koriyar walkiya Ya Kira duka ma aikatan gidan inda yace kar akuma saka tsohuwa talai aikin komai Koda dibar ruwa ne wankin kayan ta ma arika hadawa ana kaiwa shago a wanko Haka Kuma duk Wanda izzatu ta Kuma ciwa fuska ko wulakanci to ya fada mishi tunda ga wannan Rana tsohuwa talai ta samu cikakken yanci inda Kuma izzatu ta fice daga gida ta nufi nasu da sunan tagama auren dama sanadi take nema ta Kuma samu sai dai acan gidan Basu Bata samu goyon baya ba inda aka tuso keyar ta aka dawo da ita aka Kuma bawa ak hakuri inda ita Kuma take Jin ta gama auren shi Koda shi Daya yayi saura aduniya sai sun rabu inda Kuma ta fito da sabon salo na aunawa hajiya Mama da duk wani nashi zagi abinda yake Jin ba zai daukaba Tsawon sati biyu tana gurza mishi Rashin mutunci Yana dauke Kai inda washe gari sai ga hajiya mama da tarin magunguna ta diro gidan.......... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 8* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* ...........Hajiya Mama ta shigo gidan tana sallama inda izzatu ke zaune tana chatt a wayarta ta dago kanta ta dubi hajiyar ba tare da ta amsa sallamar ta ba ta maida kanta ga wayarta taci gaba da chat dinta Hajiyar ta karaso ta zauna tana kallon izzatu da ta baiwa banza ajiyar ta. Tayi murmushi kafin tace "Ga maganin Nan ki ajewa abdukarim da Zuma ake Sha safe da maraice. Bata karba ba kamar yadda Bata nuna ta San da zaman hajiyar a wurin ba Talai da taji zuwan hajiyar ta karaso tana gaishe ta "Yauwa talai ga magani Nan ki ajewa abdukarim kice mishi sau biyu ake Sha safe da maraice Kuma da Zuma ake Sha Talai ta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});