Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zawarawa sukayo Mata sallama inda tayi nufin yin aure ko don ta nunawa ak ita din ba irin matar dake bandaro bace Wai don an saketa. Kayanta da ta baro gidan ak yasa aka kwaso Mata mota har gida ya kawo Mata inda ya Kuma Bata wata takarda yace taje ga likita Usman Wanda ya zamo musu family doctor Ada can wai zaiyi Mata bayani..... "Yo bayanin me zaiyi min tunda dai Allah ya Raba Ni da wahalar auren ka Wanda Babu komai acikin shi sai asara? Yayi murmushi "Kar kice haka don akwai wani Al amari da Usman din zai sanar dake Wanda zai haska Miki abinda ke cikin duhu Da haka ya juyo abinshi ya barota da yi mishi rakiya da ido tana hasaso wani Abu me kama da nadama Amma haka ta cije washe gari ta nufi Asibiti inda ta zarce office din doctor Usman............. [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *page 10* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ....... Doctor Usman ya tarbeta cikin mutunci don Bai zaci sun rabu da AK ba bayan sun gaisa yake Mata fatan alkhairi akan auren AK din "Ashe eng ya angwa ce madam ? To Allah ya baku zaman hakuri da haka Mata ke goyawa mazajen su baya ai da ko Ni Nan na karo wata to Amma abin ne ba duka Kai ba sunan wata hula Izzatu ta kwabe Baki kafin tace "Shi dai Kam ai aikin banza ne yake Wai jefa agwagwa ruwa Wanda Bai ko Kai ga harara cikin duhu ba . Doctor Usman yayi murmushi "To madam na Gane karatun sai ayi ta hakuri dama shi zaman haka ya gada Amma da anyi hakuri sai komai ya zamo ba komai ba duniyar ma guda nawa ce? "Likita bama tare fa da AK ahalin yanzu don Allah ya sani ba Zan jure zaman asara agidan shi ba shekaru goma Sha biyu Babu haihuwa haka Zan Kare saboda Allah? Yanzu ma zuwa nayi ka fasa min wancen KWAN na gwajin da kayi Mana don har yanzu Bai fuskance Ni da sakamakon gwajin ba Wanda Ni da kaina na gano matsala daga gareshi don yadda dangin shi ke son saka min ciwon Kai da nice da matsala da tuni sun mishi aure shine kawai na zabi ya sauwake min auren shi in Kara gaba don kasar Allah me yalwa ce in kaji matsatsi ka Kara gaba shine nake son sanin sakamakon don in har da bukatar Nima adora Ni Kam magani ko ya sakar min wata cutar sai na Tara kusa. Doctor Usman ya zuba Mata ido Yana Mata kallon kinyi wauta. Ya tambayeta "Yanzu shi eng yasan Zaki zo Nan wuri na? "Eh yasani ta bashi amsa Amma duk da haka sai da ya Kira wayar shi don sunyi dashi shima zai Taya shi rufe sirrin Kara biyu ya daga bayan sun gaisa yake sanar dashi madam ce tazo da wata magana wadda muka Dade da haka Rami muka binne na Kuma yi maka alkawarin sai dai ta fito ta bakin ka ba dai Baki na ba. "Kar ka damu Usman baba tare da ita a yanzu ta nemi saki ne gareni don tana ganin nine me matsala bayan ta gama cinye fuskar hajiya ta tas inda na sauwake Mata Kuma tunda tazo gareka na yarda ka fada Mata gaskiyar magana don ta Gane kalmar tausayin ta da nake yawan nanata Mata Amma Bata taba daga kalmar tayi Mata duban fahimta ba So kar ka damu na yarda na amince ba ita ba duk wani ma me min kallon da take min ka sanar dashi na gode ya fada Yana tsinke wayar shi Radam tajiyo maganar da AK yayi inda taji wani ruwa na bin jikinta inda ta Gane zufa ce don ko Usman Bai fada Mata ba ta gano bakin zaren. Usman ya soma da yi Mata tambayoyi akan Shan kwayar Hana daukar ciki Kai tsaye ta amsa mishi da eh kwarai ta yi su. Inda shi Kuma ya Dora yi Mata bayani "Wadan Nan magunguna da Kika Sha sune sukayiwa mahaifar ki muguwar illah wadda ta kassara ta har kikaji babu batun ciki ko haihuwa Ranar da kukazo gwaji eng ya nemi sanin dalilin matsalar ku inda ta bangaren shi ba a samu matsala ba sai ta bangaren ki inda bincike ya gano illar da maganin yayi Miki Dalilin da yasa na ce ki bamu wuri kenan don ban San ya me gidanki zai fahimci zancen ba inda nayi mishi bayanin komai Amma ga mamaki na sai Naga ya tausaya Miki har ma yace mu haka mu binne Ni da shi baya son kowa yaji shine dalilin da Bai fuskance ki da maganar ba ya dai karba Miki magunguna Wanda ya sanar Dani Wai kinki amfani dasu wannan shine dalilin da kikji Bai sanar dake komai ba Amma banji Dadin abinda Kika sanar Dani ba gaskiya Kuma kin tafka kuskure ba karami ba Ta dafe kanta hawaye na zuba inda take Jin wani Abu me kama da nadama duk da Bata taba yin nadamar wani Abu da tayi a Rayuwar ta ba sai yau da taji inda ake halacci ba tare da an duba Kai waye Wanda akewa halaccin ba Bata cewa Usman komai ba ta taso ta taho Kai tsaye ta zarce gidan abdulkarim duk da ita Kanta Bata San me zai kaita gidan ba bare abinda zata yo............. [5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 11* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Ta shigo gidan cikin wani irin sanyin jiki da nadama tana tafe tana kunga kafa da son lalubo yadda zata dawo da bara bana Ta shiga gidan inda ta iske Lubabatu na aikin matsa katafun ak Wanda ke kwance akan kujera tree seater lubabatu ta amsa sallamar izzatu tana yi Mata sannu da zuwa inda ak ya tashi zaune Yana kallon ta Ta zube gaban shi tana sharar hawaye kafin ta kece da kuka tamkar wadda akayiwa mutuwa idan baka San ta ba sai ta baka tausayi "Me yasa baka fada min halaccin da kake min ba AK? Nayi nadama fiye da yawan shekaru na a yau na gano tausayin da kake fadar kana min a lokacin da damata ta barni Don Allah ka gafarce Ni abdulkarim yau Ni NA SHIGA UKU ina Zan sa kaina? Tsam ya tashi ya bar Mata gidan don Yana ganin Rainin hankali ne ma ya tsaya sauraren ta inda ta gama kukanta ta fito inda lubabatu ke Bata hakuri da haka ta fice tana tafe tana zancen zuci babu abinda yafi damunta irin yadda taga lubabatu ta murje har cikin ta ya bayyana ita kuwa har yanzu ba ta samu nasarar da take fadin asarace zaman gidan shi Mutumin da ta tsayar me abin hannun shi ne irin Yan bokon Nan Wanda duniya ke fadawa karya Wanda suke dadewa Basuyi aure ba saboda tsara Rayuwa

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});