Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ak Kwana biyu da yin hakan me gidan ya dawo daga tafiyar da yayi ayadda taso ba zata Kuma kwana gidan ak ba Amma wani Abu da ta kasa ganewa shine ak kwarjini ne gareshi Koko son shi ne takeyi da har in tayi arba da shi take mantawa da kanta? Ganin ak yasa taji ko za a dawo da bara bana ba zata Rabu da ak ba Ta tarbeshi cikin salon kissa da kisisina Wanda take siyeshi har ma ta mantar dashi tunanin wata ya mace. Washe gari ya fice zuwa gaishe da hajiya Mama inda acan ya karbo umarnin hajiyar na ya karo aure ko Kuma ita tayo mishi Ya dawo inda ta kula da Yana cikin damuwa duk da Bai fada Mata ba Amma ta San kwanan zancen don haka sai kawai ta fada mishi yadda sukayi da Hajiya. Ya dubeta "Ni kamar Ni ace za ayi min aure ai kamar an sarawa matar da aka aura min aiki. Ta Sha mur tana hade fuska "Nifa har yanzu kaki fito Dani duhu akan gwajin da akayi Mana Amma ko baka fada min ba na san an samu matsala ta bangarenka don da akaina aka samu matsalar da tuni ka bi bayan hajiya ka karo aure shine ka rufe min har kana tsallake kasa neman lafiya to kasani Nima hakuri na ya Kare tunda hajiya ma tazo har gida taci min fuska akan hakan bare su shafa dake fasa min goshi Lokaci yayi da ya kamata ka fito ka fada musu gaskiyar magana akan Kaine me matsalar don su sakar min Mara nayi fitsari idan Kuma na gaji da mugun halin su sai ka sauwake min auren ka kawai. Yayi murmushi Yana dubanta "Wa ya fada Miki magani naje nema India? Yo har sai an fada min ga Abu abude? Ai na San halinku ne maza na Rashin adalci da Akaina aka samu matsalar nan da tuni ka samawa kanka mafita to Nima na gaji Ya Kuma yin murmushi " to haka din ne Allah ya bamu lafiya Amma Ina so ki sani Ni haihuwa da ake ta maganar ta akaina ban wani damu ba saboda na San komai Allah NE ke yin shi idan Ina da rabon haihuwa Zan haihu idan Kuma bani dashi auren ne kawai ake da ikon yi min Amma haihuwa Babu me ikon bani ita in ba Allah ba So ki bar damuwa hajiya Kuma kiyi Mata uzuri Dole ne taji tausayina Amma ko ita ki Bari Zan fahimatar da ita zata Gane sai dai ki sani ba Zan lamunci Raini gareta ba duk abinda zatayi Miki saboda kin rabeni ne idan Kuma kina sona Dole ki girmam min mahaifiyata don su shafa in sukayi Miki zanci mutuncin su Amma akan hajiya komai zai iya faruwa Ta dubeshi cikin Jin haushi da takaici "Kana nufin sai don Ina sonka sai in Bari hajiya ta takani akan abinda ba laifina bane? Shima ya dubeta cikin Jin haushin abinda take kokarin fada akan mahaifiyar shi........ [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 4* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........."Me kike son ce min ne"? Ko hajiya Bata haifeni ba nayi Zaton girmanta zaisa ta ci albarkacin sa bare kuma Ni da kaina. To kar ki Fara don Zan iya jure komai akaran kaina Amma ba Zan jure ko kallon banza ga hajiya ba bare ki nuna Mata yatsa....... "Ohooo sai nice za a iske gida azageni in Kuma shiga sabgarsu su zageni saboda Ni ban San yanci ba ko kuma shago aka bude na fito ko Kuma daga sama na fado? "To na rantse maka Babu shegen da Zan Kuma yarda ya taka Ni in zuba ido in kyale shi don yanzu Kai nakewa Alfarma ba kamar Ni da suke zaton kayi min Alfarmar ba sai Kuma ka shirya sanar dasu Kaine da matsala ba Ni ba. Ya dubeta "Ina fatan cikin shegun da ba Zaki yarda su taka ki ba Babu hajiya? Kiji ki Kuma kiyaye Babu wani Abu da hajiya zata so ko ta sani Wanda ba zanyi shi ba don bani da wani fata ko buri sai na in rabu da ita lafiya. Ko auren take so nayi zanyi don zanyi biyayya agareta sai ki kiyaye. Tayi wata kwafa ta shige daki ta barshi da yi Mata rakiya da ido kafin yayi murmushi kishi manya kowace mace da kalar nata abinda ma yake tambaya shine shi kishi dabi a ce ko hali ne? Tunda sukayi haka sai izzatu ta fito da sabbin salo tamkar wadda ake zugawa Amma dayake Allah yayi mishi hakuri sai yayi Mata uzuri akan cewa maganar hajiya ce ta sa ta daukar Kai Sati biyu Yana gida Yana kallon idon mikiya a tashar farin wata shafa ta shigo ita da wata budurwa me shegen kyau ya tashi zaune inda izzatu ke kallon su awatse Suka zauna suna gaishe da shi inda ko kallon izzatu Basuyi ba Bayan sun gaisa shafa tace "Dama hajiya ce tace na kawo maka lubabatu gata nan kanwar mijin asiya ce idan Allah ya yi sai ku dai dai ta". Lubabatu ta sunnar da kanta kasa cikin Jin kunya inda yaji wani Abu marar Dadi in Banda hajiya yaushe zata turo mishi yarinyar har gida Mai makon ma ace yaje ya ganta. Izzatu da take kallon su cikin kaskanci ta tofa albarka cin bakinta. "Wane irin aure ne haka marar daraja da sanin kimar Kai? In ba lalacewa ba lubabatu yaushe za a turoki gidan mutum maimakon shi ya iskeki gidan ku in dai ba zubarwa Kai daraja ba? Shafa ta dubeta "Ai Rashin daraja ya Kare ga ci kasayas? Babu komai indai ta samu shigowa ai tayi daraja..... Ya dago Mata hannu cikin fusata "Ashe kema kin iya wannan iskancin irin na su Samira da asmau? Akan idona kike fada Mata haka? "To Yaya bakaji abinda tace ba? .... "Tashi kuje Zan zo in samu hajiyar muyi magana.... Shafa ta finciki hannun lubabatu suka fice daga gidan "Gaskiya ba Zan boye maka ba ak indai aure ake Shirin Yi maka Ni Kam sai dai ka sauwake min aurenka don ba Zan iya zaman hakuri biyu ba, ba zanyi hakuri da Rashin haihuwa ba Kuma inzo inyi da kishiya da dangin miji abarni inji da Abu daya Bai tankawa maganar ta ba ya ci gaba da kallon shi inda wayar shi tayi Kara ya duba ya dauka da sauri inda ake sanar dashi batun kwangilar da aka bawa wani Dan kwangila ne wato Kabir mashi Wanda aka karbo aka bashi don anfi yarda da aikin shi fiye da Kabir mashi din don haka ake son ya fara cikin watan Nan kwangilar shimfida tituna ce a wasu kauyuka wadda za a samu ALHERI sai dai baiji dadin karbewa daga hannun Kabir mashi ba don Babu me son ayi mishi haka Amma dai ya amsa sukayi sallama Washe gari sai ga hajiya Mama ta diro gidan ak na Shirin ficewa Ya zube gaban ta Yana kwasar gaisuwa "Jiya na turo shafa da lubabatu akace matarka

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});