Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

karba tana fadin insha Allah ba Zan manta ba hajiya Hajiyar ta Mike da Shirin ficewa inda talai tace "Hajiya ki tsaya ko ruwa Kisha Mana bare ki huta..... "Tunda gidan gyatumin tazo sai ki Bata ruwa gwana yar ka iya , cewar izzatu wadda ke wurgo musu harara "Ni in nagane mutum munafiki ne me zai hada Ni dashi da munafurcin sa? Wallahi a yanzu dai dai nake da anuna min yatsa na karya tunda tafiyar Babu mutunci Hajiya Mama ta Kada kanta "Allah ya shiryeki ya dawo dake hanya..... "Ameen in dagaske kike duk da kema kina bukatar shiriyar tsohuwar banza me bibiyar Matan ya'yan ta...... Kalmar tsohuwar banza ta fado akunne AK dake shigowa gidan wani Abu ya naushi kahon zuciyar shi ya dubi hajiya ya Kuma dubi talai da ta soke Kai kasa Yana son ya gano wadda izzatu ke jifa da kalmar tsohuwar banza amma ya kasa ganowa "Yanzu kike tafe hajiya? Yayi karfin halin tambaya "Yanzu nazo har Zan wuce dama magani na kawo maka gashi Nan wurin talai tayi maka bayani. Wannan saurin na hajiya shi ya alam ta mishi zagin tsohuwar banza da izzatu tayi ba da kowa take ba sai hajiya mama. Ya riko hannun hajiyar Yana fadin "hajiya don Allah me ya faru kike sauri haka? "Babu abinda ya faru ak Zan koma gida ne kawai ka tabbatar kayi amfani da maganin da na kawo maka.... "Ina fatan hajiya ba ke ko talai take Kira da tsohuwar banza ba? "To wacece Ni da ba za a zageni ba ...... Kafin ma hajiya ta dire zancen ta ya Cabo izzatu ya soma wanketa da maruka "Ayau Zan nuna Miki hajiya tafi karfin komai agareni Ina tausaya Miki Amma da yake jaka ce Baki San ana tausayin ki kije na sakek........ "Kar ka fara abdulkarim ! Hajiya ta katse shi da tsawa. "Ka rabu da ita Kai dai kayi ta hakuri..... "Ai dama da wannan manufar kikazo bakar munafuka annamimiya kin Kuma ci nasara don Ina me tabbatar Miki da yau wallahi aurena da abdulkarim ba zai Kuma kwana a duniya ba sai ya sakeni don in Kara gaba ko Zan haihu. Ta dubi ak "Idan dai Kai din Dan halak ne cikin wannan tsohuwar banzar da wancen tsohon banzan na kushewa ka sakeni saki uku.... Kafin ma ta dire zancen ya furta Mata kalmar sakin "Idan akwai sakin da ya wuce a lissafa shi fiye da uku to nayi Miki shi kije kije kije bana bukatar ganin bakar fuskar ki Arayuwa ta Ina fatan hakan zai tabbatar Miki Ni din Dan halak...... Ta dubeshi ta watsar "Sai ka auro hajiya Mama kasaka dakin da Zan bari....... Bata rufe Baki ba ya rufeta da duka sai da hajiya ta yi mishi tsawa kafin ya saurara Mata inda tafice aguje don ta tabbatar ba cikin hankalin shi yake ba "Baka kyauta min ba abdulkarim me zaisa ka biye Mata ? Zagi ai baya Kari don ta zageni sai menene? Naso ka lallaba matar ka kuyi zaman ku har Allah ya warware maka lalurar ka don ba kowace mace bace zata hakura da Rashin haihuwa shi yasa kaga Nima nake lallabata "Hajiya na gaji da halin matar Nan Kuma ba ayi wata mace da zata zageki ba in kyale ta ko Ruhin mu hade yake wallahi na gwammace in mutu da dai in Bari wani ya muzanta min ke bare izzatu dake home da barazana cikin rizgar arzina. Kuma Bari in fada Miki gaskiya hajiya da dai nayi nufin yin shiru har muddin Rayuwa akan matsalar Rashin haihuwa hajiya Ni lafiya ta kalau itace me matsalar ba Ni ba............. [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 9* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Hajiya Mama ta dubeshi azabure Jin Yana fadin ba shine me matsalar ba izzatu ce. "Dama lafiyar ka kalau abdulkarim Amma kaja Baki ka tsuke? Lallai na sarawa hakurin ka ka Kuma yi halacci Amma anyi maka butulci. "Tun tsawon wane lokaci ne kasan hakan? "Izzatu ta matsa min da son lallai sai munyi gwaji idan ma magani zamu soma karba sai mu karba inda na Gane manufar ta ta son agano me matsala ce. Munje Asibiti inda akayi gwajin sai dai akanta aka samu matsala don likitan ya fada min tayi shaye shayen magunguna na Hana daukar ciki Wanda suka haifar Mata da matsala a mahaifar ta inda ya bada magani don ta Sha Munyi ganawar sirri ne da likitan Wanda ya ce ta bamu wuri zamu gana inda ta fito ta dawo mota Ni Kuma ya sanar Dani matata ba zata taba haihuwa ba saboda illar da maganin Hana daukar ciki yayi Mata a mahaifar Ni Kuma nayi alkawarin Zama da ita da lalurar ta inda take min kallon nine me matsalar ba ita ba inda maganin da aka Bata ma Bata yi amfani da shi ba tace ita ta San lafiyar ta kalau Kuma tunda bataji nayi Mata wata magana ba to matsalar tawace Ni Kuma nayi nufin rufa wannan asirin don Ina tausayin ta gidan su ba komai bane bare Kuma duk ta wanke dangin da Rashin mutunci Kuma ma Bata San mijin da zata aura ba Wanda kalubalen dake tare da ita yafi na Nan shiyasa Kika da Ina hakuri da ita Amma tunda har lamarin ya soma shafarki Dole ne inyiwa tufkar hanci dama kwanaki ta Mari talai to ko akan Marin zanyi Mata hukunci sai gashi ta jawo abinda na gudar Mata na Kuma San zata gano hakan da kanta musamman idan ta Kuma yin wani auren Hajiya Mama ta sauke ajiyar zuciya "Allah ya shirye ta yasa ta Gane ko Babu komai dagawa da izgili aikin shaidan ne duk yadda kake tausaya Mata ita Bata tausayin kanta.... "Hajiya na yarda ki nema min auren lubabatu Amma ki Fara Jin Ra ayin ta idan nayi Mata sai ayi magana kawai... "To ko kaje da kanka kawai sai ku fahimci juna dama wancan zuwan shafa ce ta zanzame Ni akan ta kawo maka lubabatu don ita yarinyar cewa tayi kunya take ji Allah ya zaba abinda yake shine ALHERI ina fatan auren ku da lubabatu ya zamo silar farin ciki Kai da ita damu gaba Daya "Abu kamar was karamar magana ta Zama babba inda lubabatu ta amsa tayi na am da batun tuni aka tsayar da Rana cikin wata biyu aka Sha biki amarya ta tare inda Kuma can izzatu ta soma fuskantar kalubalen gidan su don tuni ta Gane Bata da uwa agidan sai dai Matan uba Wanda take wuni bauta musu Babu gode bare bare godiya ga Rashin abinci bare Kuma dare yayi sauraye su cika Mata kunne da guda har ta kasa barci Dawowar ta gida ko wata ba ayi ba taji shelar bikin AK da lubabatu Wanda acewar ta take barka da rabuwa da shi Amma sai da ta tsinci wata damuwa wadda ta rasa ko ta mecece Damuwar da Bata da maraba da kishi Amma sai ta maze taci gaba da harkokinta har ta fita daga idda inda Kuma

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});