Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kabir mashi ciwo irin Wanda Bata taba yin irin taba Amma da yake ta iya jarumta da hakuri haka take ta jaganiya da Yan yaran rainon ta yaran Babu Wanda ya shekara biyu ga Yar banzar rigima wancan yayi kuka ta rurruga wancan yayi fitsari ta wanke wancan yayi Kashi ta wanke ba zata taba samun sauki ba sai sunyi bacci ko iyayen su sun karbesu Amma Duk da haka ciwon da takeji Bai sa ta kwanta ba duk da kallo Daya zakayi Mata ka Gane Bata da lafiya matukar dai kana Gane lamarin Rayuwa sai dai Rashin kudi ya Hana Mata zuwa Asibiti inda ta Bari sai ta karbi kudin rainon ta idan anyi albashi sun karbi kudin su Sai dai kafin albashin ciwo yaci karfin ta har ta Fadi kwance ciwo riris inda har rainon ma ya gagara Wata daga cikin masu kawo yaranta me suna Jamila ta shigo gidan inda ta iske dungon kwance abin tausayi "Subhallah ladidi Baki da lafiya ne? Wallahi kuwa Jamila Ina Dan gidana fahat? Yaron da take raino ya SHIGA dago Mata hannu Yana son ta dauke shi saboda sunyi sabo me karfi da yaran Ta Mika hannu ya taho ta rungume shi inda Jamila ke kallon ta cikin tausayawa "Amma ladidi kinje Asibiti kuwa? A a Jamila banje ba saboda Babu kudi hannu na.......... "Karki damu taso muje in kaiki ai lafiya tafi komai Jamila ta kaita Asibiti aka dubata aka Bata magun guna suka juyo gida inda jamilar ta kashe kudi masu dama sama da dubu goma Sha biyar duka dawo gida gungo nata zuba godiya don gaskiya Jamila na mutunta ta ko abinci me Dadi tayi sai ta Aiko Mata bare ta dafa nama "Karki damu ladidi ai mun Zama Daya Babu komai ke dai Allah ya Baki lafiya Ta amsa da ameen ya Allah Haka Tasha magani har sauki ya samu Inda wata ya cika Jamila ta dauki albashinta ta kawowa dungo hakkinta Amma dungo tace Allah ya sauwake wallahi ba zata karba ba Amma Jamila tace wallahi sai ta karba..... "Haba Jamila don dai nice uwar marasa mutunci sai na karbi kudinki ?...... "A a sai kin amshe su wallahi banyi don komai ba sai don Allah da zaman tare Allah ya Kara Miki lafiya ta aje Mata kudin ta dauko danta ta fito inda ta bar dungo da zubar hawaye Wai yau Dan da ta haifa ta wahaltawa shi ke gudunta yayin da can wasu da Basu hada komai ba sai musulunci da mutunci suke wahala Mata har suyi Mata abinda danta Bai yi Mata ba Babu abinda yafi Kona ranta irin yadda ta taka har gida ta sanar dashi zubar bangon ta Amma har yau Bai tada Mata ba asalima an kusa shekara Amma har yau zuwan shi guda Kuma yaga yadda aka saka zana amma bai Kuma zuwa ba Kuma yanzu da mutuwa tayi ba lallai ya sani ba to in ta mutu ma Yana da asara ne? Amma dayake tana mishi uzuri sai ta bar abin ya wuce ko aranta Bata aje shi ba taci gaba da rainon yaranta Wanda ke debe Mata kewa fiye da zato inda makocinta malam Ali ya shigo ya duba jikinta inda yake tambayar ta Kabir ya Zo kuwa? Tayi murmushi "Bai zo ba malam Ali , to Allah ya Kara lafiya da haka ya fice Yana mamakin wannan yaro da duniya ke rudu duk shaharar shi Amma abin haushi ya yasar da uwar shi sai tayi raino ta ke ciyar da kanta Amma shi Yana can cikin katon gida daga shi sai matar shi suke hutawa Anya kuwa Bai dauko hanyar lalacewa ba? Uwafa? Uwar ma irin dungo wadda yasan yadda ta wahalta mishi har ya tako matsayin da ya tako? Babu wata riba ko nasara da ake samu ba ta silar uwaye ba koma an sameta to zata sulale saboda Babu albarkar iyayen sai yayi mishi adduar Allah ya shirye shi ya kuma shiryi Al ummar musulmi Baki Daya.......... [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 20* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* Yara suka taso cikin kulawa inda ummita iyaye da Yan uwan uwa da na uba ke nuna Mata so da kauna da Kuma kokarin dorata bisa bigiren tarbiya me kyau inda tayi matukar sabo da ubanta eng AK Wanda ko yaushe tana hannun shi Yana Mata wasa har tayi sabo me yawa dashi don in har Yana gida to Bata Rabuwa da shi tafi like mishi fiye da Uwar ta shima Kuma Yana janta jiki don wani irin so yake Mata jinta yake tamkar Ruhin shi lokacin da ta Kara wayo ma dakin shi take kwana in kaga sun Rabu to baya gari shima sai da hikima in ko ta na farke ya tafi ya barta to zata wuni kuka sai da kyar zata hakura in Kuma ya dawo kaf abinda ya Riko natane ba kuma zata yarda ya kubce Mata ba Lokacin da ta Kai shekara biyu sabon ya Kara karfi da ta kula zai yi Mata wayo ya gudu sai tayi ca cumi rigar shi ta rike Taki saki sai anyi da gaske kafin akwace shi hannun ta Sai da ta shekara biyar kafin lubabatu ta Kuma haihuwa inda ta haifo Mubarak bayan Mubarak sai Ahmed sai Fatima daga kansu haihuwa ta tsaya inda yaran ke samun kulawa Amma duk tsananin so da kulawar da ake Basu Bai Hana atarbiyan ce su bisa tsari ba don gaskiya lubabatu tana da kokarin tarbiya Bata kuma yarda da sakarci ba ko don ta tashi da tata tarbiyar ne? Sai yaran suka tashi cikin tarbiya da girmama mutane duk inda suka SHIGA sai sun zamo abin so da Sha awa Sai dai soyayyar ummita da ban take azuciyar mahaifin su sai dai Yana kokarin saita Kan yaranshi ba tare da nuna wariya ba Amma duk da haka ummita na karbar girmama wa irin ta babban wa sai lamarin gidan eng AK ya zamo abin Sha awa akasin na gidan Kabir mashi Daular da ake tanadawa humaira fulani ta zarce afadeta don akullum shaharar Kabir karuwa take kwagiloli Kai da Kai suke zuwa inda izzatu tace haihuwar fulani ne tazo da goshi Wai da ma ummul khairi aka samata inda kuma Kabir ya yarda da maganar ta Kullum Kara shahara yake inda izzatu ke matukar kulawa da humaira wadda ta taso ba kwaba ba harara ko da ko zata yaga kudi Yan magana sukace nono alkalin Da ai kuwa hakan ta na Shirin tabbata domin kuwa nonon da humaira ta tsotso ajikin uwar goyon ta na Shirin tabbata domin kuwa ta taso da wata irin sangarta da tabara bama wannan ne abin ji ba tun tana Yar shekara biyar ta iya tijara da wulakanci hakama idan ta na kuka Bata Jin rarrashi inda Kabir ke matukar so da kaunar ta Amma batayi sabo da shi ba sosai kamar izzatu Amma duk wani gata tana samun shi Makaranta ma pravet aka saka ta me shegen tsada aka Kuma yi sa a tana da fahimta sai dai

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});