Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi Mata wulakanci? A a hajiya Babu abinda tayi Mata dama Ina Shirin zuwa ne Kika zo. Hajiya ayi hakuri da maganar auren Nan don Allah. Auren ne kawai zamu iya hajiya Amma Babu me iya bani haihuwa sai Allah da yaso bani zai bani inko Bai zano ba to Matan kawai Zan Tara don haka hajiya na rokeki kiyi min addua abarwa Ubangiji komai Yana sane da Ni da matsala ta Hajiya ta sauke ajiyar zuciya, "To shikenan abdulkarim na fahimce ka Kuma maganar ka itace gaskiya na janye maganar lubabatu Ubangiji yasa kana da Rabon ganin naka diyan Amma gaskiya sai kajawa matarka kunne...... "A a hajiya tunda dai kin janye Taki maganar Ni Kuma yanzu ne zanyi tawa maganar "Wai hajiya Baki San shine da matsala ba kike kokarin yi mishi aure ? To Nima ba Zan iya auren Wanda baya haihuwa ba tunda ya Zama juya Nima Ina da muradin karawa gaba tsawon shekaru goma Sha inda haihuwa nayi yanzu da na kusa aurarwa tunda kun gama naku wulakanci Nima yanzu ne zanyi nawa Shekaru biyu kenan da suka wuce mukaje Asibiti akayi Mana gwaji Ni da shi inda likitan ya nemi in Basu wuri suyi ganawar sirri ban San me ya fada mishi ba Kuma har yanzu Bai sanar Dani ba inda ba gano an samu matsala daga gareshi shine ya boye min don kar in ce ba Zan iya ba inda kuka Dora min jakar tsaba to hajiya abdulkarim ne me matsala ba izzatu ba sai ku gaji ku hutas ku Kuma sakar min Mara inyi fitsari Hajiya ta dubeshi ta dubi izzatu cikin tashin hankali.......... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 5* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........ Hajiya ta dube shi da mamakin wannan magana ta izzatu. "Da gaske ne abdulkarim"? Yayi murmushi Yana mamakin izzatu akan yadda take kokarin butulce mishi "Hajiya mu rufe maganar Nan don Allah babu amfanin da tado ta zaiyi Mana mu barwa Allah ikon shi kawai sai mu zauna lafiya..... "A a abdulkarim idan har kasan kana da matasala kar ka rufeni fada min sai anema maka magani tunda Ubangiji Bai Saukar da cuta ba sai da ya Saukar da maganin ta. "Haka ne hajiya to anema Mana sai muyi amfani dashi Ni da izzatu........ "Adalilin me da Kare zai dauki Dame? Ai ba a taba karan ta min akan komai ba sai sai akan magani? Kuma Ni meye hadina da Shan maganin ka na matsala? Kai ne nasu Kuma Kaine da matsalar Nan meye nawa? Ni fa kasani wallahi na gaji da wannan zaman cutar don nazo karshe wallahi da zaka sauwake min zanfi farin ciki don yanzu Babu wani amfanin Zama da Kai Hajiya ta Mike da Shirin komawa "Zansa mas udu ya karbo min maganin sai kuyi amfani dashi mugani Allah ya sa mu dace Ya Mike shima suka fito don yiwa hajiya rakiya inda direban ta ya ke Izzatu ta rako hajiyar da harara tana Jin kadan ya rage ta make tsohuwar komai zai faru ya Dade Bai faru ba. Hajiya ta wuce shi Kuma ya dawo inda ya isketa sai cika da batsewa takeyi Ya soma rarrashin ta Akan tayi hakuri su barwa Allah ikon shi akan maganar haihuwa...... "Saboda ka Gane Kai ke cutata shiyasa zakace inyi hakuri Mana Amma ai ka Dade da sanin irin wulakacin da danginka harma da hajiyar ka suke min suna zaton nice da matsala har suka kasa yi min uzuri sai yanzu da Allah ya haska min na gano ka shine Nima za a cuceni? To kasani Kai namiji ne komai Daren dadewa zaka iya samun haihuwa Amma Ni da lokaci na ya wuce to yafa wuce kenan so abinda yafi kawai mu hakurewa juna don Allah ka sahale min aurenka tun lokaci Bai kure min ba. "Ni dai nasan duk kokarin me kokari Bai Isa ya samo abinda ba Rabon shi ko ya samo din kuwa zai sulale ya barshi don ba Rabo bane don haka Zan Baki shawara ki roki Allah abu mafi ALHERI a Rayuwar ki sai kiga ALHERI Yana samunki a ko ina Amma son zuciya Babu abinda yake haifarwa sai bacin zuciyar don haka don Allah don Annabin sa ina so daga yau ke daga yanzu ma mu rufe babin maganar haihuwa Ubangiji yayi Mana baiwa me yawa don Bai bamu haihuwa ba sai mu butulce mishi? Ina rokon Allah yasa Rashin haihuwar da Bai bamu ba ya zamo sanadin SHIGA ALJANNAH shi kenan magana ta Kare daga yau. Abinda ta kawowa ranta shine kawai Yana son taci gaba da Zama dashi Yana cutar ta tunda yasan shine bashi haihuwa Bata tanka mishi ba Amma fa tana Jin ba zata yarda da wannan cutar ba. Tundaga wannan Ranar sai zaman lafiya ya wanzu tsakanin ta da dangin miji su shafa duk da ba SHIGA sabgar su take ba haka ma hajiya Bata Kuma zuwa gidan ta ba inda Kuma ak yayi kwangilar shi ya gama ya samu ALHERI me yawa yayiwa hajiya da danginshi hidima itama izzatu ya Bata kasonta Wanda me yawa Wanda duk in yayi kwangila ya gama dama ka Ida ne sai ya Bata sai dai awannan karon Bata amsa ba tace ta gode ba zai siyi Ra ayin ta ba idan dai har son burgeta yakeyi to ya sauwake Mata auren shi ta Kara gaba inda itama zata haihu Yayi murmushi Nan ma rarrashin ta yayi Yana Bata hakuri shima tayi shiru ba don ta yarda ko ta aminta ba. Ranar wata alhamis ta kwanta barci inda tayi wani mafarki Wanda shine silar zamowa karshen auren su da AK ....... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 6* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .....Wani mutum tagani a matsayyin mijin aurenta Wanda ba AK ba kawai Kuma ta ganta da jaririya ahannu amatsayin yarta sai dai wani hayaki dake biye da ita ta rasa Gane hayakin meye akarshe ma sai hayakin Nan ya rikide ya koma wuta wadda ke biye da ita tana Shirin lasota aguje take gudu kankame da jaririyar inda ta hango ak Yana tafiya hankali kwance akan wani Abu me kama da jirgin kasa inda ta sheka aguje tana son ya taimaketa kar wutar Nan dake biye da ita ta lasota Amma ga mamakinta sai sai taga ko kallon ta baiyi ba ya wuce abinshi. Tabishi da kallo har ya kusa kurewa ganin ta inda ta hangi wata yarinya me kyau tana rungume da jaririya ta mikawa ak din ya karba Yana murmushi ya rungume yarinyar Yana murna inda ta ke kallon yarinyar da tabawa ak jaririya kamar lubabatu tana kallo Kuma ya dauketa cikin abin hawan shi me kama da jirgin kasa suka wuce suka barta ta shagala da kallon matar me kama da lubabatu har taji wani mugun radadi Yana binta ajiki kafin ta kwallara Kara inda Kuma

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});