Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kwangila har abada ba Wai wani makararren wa azinka Wanda na Saba ji ba. "Gaskiya me gida ba zanyi maka karya ba don Bata cikin tsarins maganar gaskiya ba Zan iya barin kwangila ba tunda bani na tsara yinta Arayuwa ta ba Allah ne ya zano min ita don haka Ni ALHERIN Allah kawai nake roko ko da gwamnati ta daina yi Dani to zanyi ta mutanen dake can waje komai da lokacin da sa........... "To shikenan tunda haka kace Amma kar kayi kuka Dani akan abinda zai sameka ba Wai don na rasa yadda zanyi bane yasa nake ta binka a a don in fita hakkin ka Amma tunda ka kawo taurin Kai sai ince zakaga abinda zai faru...... "Me gida ai Babu abinda zai faru sai ALHERI................. "To shikenan tunda haka kace Ni na wuce Ya Mike Bai ko yi mishi sallama ba ya fice inda AK ya soma karanto addu oin nema tsari ya koma cikin gida Yana fadawa lubabatu yadda sukayi da Kabir mashi kashe arna inda itama ta bashi shawarar suyi ADDU A itace kadai mafita Amma mutum a yau Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro. "To Ubangiji yayi min katangar karfe da duk wani me sharri da abin cutarwa ta amsa da Allahumma ameen. Afusace Kabir ya koma gida izzatu ta tarbeshi tana tambayar yadda sukayi da AK din ya Kuma zayyane Mata yadda sukayi inda tace "Kaji ko ? Kaji irinta ko har ya dubeka ya fada maka Wai aikinka Babu nagarta? Duk yadda kake kallon lamarin da sauki bashi da sauki Kuma idan ba gambo mafiyas aka sako cikin tafiyar ba to sunanka ma ya kusa Daina motsawa.......... "Abinda ba zanyarda dashi ba kenan don haka maza ki Kira min gambon Nan yazo yayi min maganin wancan marar kunyar wato eng AK Izzatu tayi murmushi ta jawo wayar ta ta dokawa gambo mafiyas Kira Kara biyu ya dauka................... [5/22, 6:19 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 31* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ......... Izzatu ta jawo wayar ta ta dokawa gambo mafiyas Kira Kara biyu ya dauka "Allah ya taimaki hajjyata in karaso ne? "Kwarai kuwa gambo mafiyas maza kazo kayi min maganin wani tarnaki dake shirin konani taho da sauri don Allah......... "Angama hajiya gani Nan zuwa........... Minti talatin gambo mafiyas ya karaso inda Kabir ya dubeshi ya tabbatar da zai iya aikata kowane irin ta addancin Yayi gaisuwa wurin Kabir inda izzatu take Kora mishi bayani "Me Kaka so ayi mishi Kabir? Ga gambo Nan zai cika maka kowane irin aiki kake so don aikin shi Babu sabani bara kuskure fada mishi duk yadda kake so ayi mishi inma batar dashi kake so ayi nasan gambo mafiyas ba zai taba baka kunya ba. Kabir ya dubi gambo mafiyas "Gambo Ina so ayiwa eng AK abinda sunan shi zai Daina zagawa duniya inaso abatar min dashi ta yadda Zan dawo da duniya ta sabuwa tunda bayyanar shi ce take neman kaini kasa warwas "Angama me gida bamu address din gidan shi yau din Nan zamu kaddamar mishi Atake Kabir ya Basu address din gidan har da hoton shi sukayi sallama ya fito Yana cewa su saurare shi zasuji yadda abin zai kasance Sai dai wani akasi da aka samu Aranar shine gambo mafiyas ya samu Kiran wani abokin shi dake Lagos Kan wata harkallar wadda za a yo wata SATA ta manyan kudi don haka ya bar aikin su izzatu ya shilla Lagos inda ya wakilta ya ranshi su Wilson da zarto wadanda suka horu da aiki suka Kuma kware Amma Wilson din ya fi su kwarewa shiyasa gambo mafiyas yafi ji dashi duk da kasancewar shi mabiyin addinin almasihu Amma sauran duk hausawa ne su hudu sai Wilson na cikon biyar duk suna aiki da gambo mafiyas inda ake bin dare afasa shaguna ko su haura gidaje suyo sata atakaice dai Yan fashi Wilson ya yi shiri shida su zarto suka nufi gidan eng AK da son aikawa dashi kiyama don umarnin da aka Basu kenan Suka kumayi sa a suka samu haurawa gidan eng a wani dare suka Kuma tadoshi shi da iyalan shi suna bukatar kudi ya Kuma dauko ya Basu inda cikin sa a idon Wilson ya fada Kan ummita dake sharar kuka akan atak da zarto yayi Mata agoshi Sun rufe fuskokin su da face mask idon su kurum ake kallo inda ummita ta kula da kallon da yake mata shi Kuma atake ya tuno da ganin da yayi Mata a country mall da irin daukar da tayi mishi da mafarkan ta da yayi tayi har ya Rika zuwa country mall din Wai ko zai sake ganinta Amma ko me kama da ita Bai gani ba sai gashi Wai yau yazo har cikin gidan su da umarnin kashe mahaifin ta atake yaji zuciyar shi tashiga rawa ko babu komai ba zaiso abinda zai sakata zubar hawaye ba don haka ya yanke shawarar sama Mata farin ciki akasin cika umarnin da zai barta Cikin damuwa Tsini Wanda ya yiwa eng AK atek da bindigar yake fadawa Wilson shifa zai cika aiki ne ko suyi su wuce Da sauri Wilson din ya dakatar dashi inda yake fadin wrong address Suka dubi juna inda Wilson din ke fadin su fice kawai da sauri sukayi gaba inda Wilson ya dauko jakar kudin da gwalagwalan su lubabatu da ummita da aka karbe ya zube musu agaban su Yana Basu hakuri ya dubi ummita ya huro Mata kiss ya wuce da sauri suka bar gidan ida zarto ya dauko wata jaka me dauke da kudi wadda yace Wai ba a shiga arziki afita haka Nan Gambo mafiyas ya Kira Wilson da son yaji yadda aikin ya Kaya Amma Wilson ya sharara mishi karyar Wai wrong address ne aka bada Kudin da zarto ya dauko su suka rage musu zafi inda gambon ke fadawa izzatu wrong address ne aka sami inda izzatu taketa yiwa gambo sababi Wai ya fara saka wasa a aikinshi in ko hakane gaskiya ba zasu daidaita ba inda yace ta Bari zai dawo Nan da sati guda shi zaiyi Mata aikin da kanshi don ta San Yana Nan da hatsabibancin shi da haka sukayi sallama tace tana sauraren shi Nan da sati dayan ................... [5/22, 7:10 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 32* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Hajiya Mama tazo Jin abinda ya faru ga abdulkarim jikinta har Bari yake don Ubangiji ya hasko Mata lamarin amafarki inda gari na wayewa ta Kira abdulkarim take tambayar shi suna lafiya dai ko? Ya fada Mata suna lafiya sai dai abinda ya faru don haka hajiya Mama ko Karin kumallo batayi ba ta tashi direba ya kawo ta gidan AK Dukan su suka zube gaban hajiyar tana tambayar su "Basu dai taba kowa ba ko? "Basu taba kowa ba hajiya hatta kudi da gwalagwalan da suka karba sun maido

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});