Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kudin mota daga hamshakin Dan nata ta karba tayi godiya ta taho tanemo tashar mota kafin ta jirayi cikar motar da zata zo birnin zazzau inda sai dare sosai kafin ta iso gidan nata Wanda ta gada daga marigayin mijinta uban Kabir Wanda ta haifa shi kadai saboda yawan wabin da tayi sai da kyar ta sameshi inda ta zamo jajirtacciya wurin neman kwabo inda ayanzu ma hada rainon yara takeyi Wanda duk wata uwayen yaran Kan biyata dubu biyar inda take rainon yaran idan iyaye su zasu fita aiki su kawo Mata idan ta dawo Kuma su karbi abinsu yara biyar take raino inda suke biyanta dubu ashirin da biyar kenan shiyasa Kabir Bai damu da ya Bata kulawa ba Wai ai tana samun kudi sai Kuma akayi sa a ita din ba me son roko bace bare matsawa shiyasa idan taga ya Sharari lokaci Bai zo ba sai ita tazo ta ganshi ta koma Haka Kuma katangar da ta sanar dashi ta Fadi yace zai sa agyara Bai gyara ba sai dai itace ta siyi zana aka killaceta Izzatu ta bude fejin salo da firirita Wai ita adole ga me ciki inda shi Kuma yake biye Mata da tace uhum zai ce meye ko me take so? Tabara iri iri inda Kuma Yan aikinta suka SHIGA UKU da yawan aiki ta yi ta tofar da yawu da Aman karya suna faman wankewa da gogewa Inda Kuma kadan zasu kuskure tayi ta Danna musu ashariya sai dai su kauda Kai suyi hakuri Wata biyar dai dai da yin maganar su ta kwangila da sister mero lubabatu matar eng AK ta tashi da nakudar haihuwa ta biyu don wancan da ta haifa Bai zo da Rai ba kasancewar ta Sha wahala shiyasa wannan karon aka kawota asibitin national inda Kuma cikin sa a sister mero ce ke night duty inda tayi hikimar sakawa lubabatu ruwan nakuda dama tayi hakan don cimma kudirinta na son cika burinta ta kumayi sa a lubabatu tafita hayyacinta har Bata San lokacin da ta haife abinda ke cikinta ba........... [5/16, 6:07 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 15* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Wani ikon Allah da ya Saukar shine lubabatu ta haifo Yan biyu duk Mata batare da ta San tayi hakan inda Kuma sister mero take kallon lamarin tamkar cikin shirin film ko wani shiryayyen Abu inda kuma tayi maza ta aiwatar da wani shiri tamkar walkiya ko ibilishiya ta shirya yarinyar guda ta turo ta zuwa dakin hutu inda ta fito take sanar da wadanda suka kawo lubabatun ta haihu wato hajiya Mama da tsohuwa talai don AK baya gari inda Kuma mero ta sada su hajiya Mama da talai dakin da lubabatu ke ta sharar bacci saboda allurar bacci da ta zurkuda Mata da sauri mero ta zagaya bayan tagar dakin da lubabatu ta haihu ta Suri Jakarta wadda aciki ta saka jinjirar ta fice da sauri tana duba yarinyar dake tsotsar yatsun hannunta Ta jawo wayar ta ta Kira izzatu ta daga tana fadin ya akayi Kuma kike isata da Kiran waya... "Aikina Yana dab da cika ga kyakkyawar yarinya ahannu na ya za ayi kenan?..... "Ki Bari don Allah? Taho kawai gani Nan Zan bude Miki gida tunda Kabir na can Yana bacci Kinga sai mu kashe mu binne ba tare da ya sani ba Kinga asiri rufe kenan. To fito ki bude min don gani Nan daf da gidan don Ina so in koma Bakin aikina.. Duk dare ne kusan Sha Daya da mintuna haka izzatu ta taso tazo ta bude gate din inda napep ya sauke mero inda tace ya jira ya mayar da ita Asibiti Suka shigo da izzatu inda mero ta fito da yarinyar daga katuwar Jakarta ta mikawa izzatu dai dai da ta tsanyara kuka inda izzatu ta doka daki Kabir tana Kiran sunan shi ya taso Jin kukan jaririya ya fito da sauri inda yayi arba da sister mero cikin kayan aikinta "Kar dai Ina can Ina bacci har akayi haihuwar ban sani ba?, "Ai dayake ma ta samu nakuda me sauki shiyasa ta kirani na garzayo. Ya karbi yarinyar Yana kallonta kyawu Kam tamkar Hindu inda atake yayi Mata huduba Aisha humaira ya mikata ga mero Yana kallon izzatu Yana Mata barka. Mero ta Mike da Shirin komawa Asibiti inda Kabir ya debo kudi masu dama ya Bata tafito tana godiya ta shige napep ta koma Asibiti inda ta iske dakin da lubabatu take cike da Yan uwa suna ta yaba kyawun Yar inda mero ke musu kallon na Sha da ku. Talai ita tace zata kwana wurin uwar dakinta lubabatu don lubabatu Kam ta dauketa tamkar uwa ga kyautatawa da take Mata Kai kaf din ma aikatan lubabatu na kyautata musu shiyasa ma talai tace ita zata kwana hajiya Mama ta tafi gida ta huta Haka hajiyar ta taho kafin asubahi lubabatu ta farko inda mero ta tabbatar Babu matsala ta sallame su itama ta harlanta aiki ga Wanda zai canjeta ta taho gida tana fatan tayi baccinta zuwa Sha biyun Rana taje gidan izzatu ta karbo kudinta Sai karfe biyu na Rana ta nufi gidan izzatu inda Koda izzatu ta ganta sai ta hade fuska tana masifa "Me Kuma kikazo yi mero ? In don kudin kine ai Kya Bari ayi suna ko?...... "Bamuyi haka da ke ba indai ba Saba min alkawarin Zakiyi ba nayi cinikin mota kuma yau nace Zan bada don haka dauko min hakki na in wuce... "Bafa Zan Baki ko sisi yanzu ba wallahi sai bayan suna don haka karki tada min hankali, mero ta dubeta cikin sikewa da son ta nuna Mata halin Dan Adam na butulci "Bamuyi haka dake ba indai ba Saba min alkawari Zakiyi ba........ "Kije dai bayan suna ki zo ki karbi kudin ki don ai kin San nafi karfin kudin ki matsalar matsiyaci kenan Bai iya samun wuri ba.... "Karki Kuma zagina akan hakki na, na Baki kwana Sha hudu ma ba bakwai ba Zan dawo karbar kudina ina me tabbatar Miki idan nadawo wata magana me kamar irin haka ta sake faruwa tsakanina dake na rantse Miki da Allah ZAN FASA KWAI ! Mero tafice afusace inda izzatu ta bita da kallo tana tunanin lallai mero zata zamo Mata katon kalubale kuwa in ba sakin hannun juna suka yi ba To Bari mugani sati biyu ya wuce me zai faru?.................... [5/16, 6:07 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 16* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ............ AK ya samu wayar hajiya Mama take sanar dashi haihuwar lubabatu inda ya yi murna ba kadan ba washe gari Bai ko gama aikin da ya kaishi sokoto ba ya juyo gida ya iso Yana tambayar lubabatu Babu inda ke Mata ciwo ko? Ta amsa da Babu ta Miko mishi yarinyar wadda ya kankame tamkar za a kwace mishi ita inda yayi Mata

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});