Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Yana kiranta Ta dago da sauri "gani dady Yauwa dama bakone gareki Yana can masaukin Baki kije ku gaisa.......... "Bako Kuma dady? Ni yace maka yake nema? Gaskiya dady bani yake nema ba sai dai in wrong address ya samu don Ni ban ba kowa address Dina ba....... "Eh shi wannan din ma ba cewa ke Kika bashi ba Ni nace mishi yazo ku daidaita ke dai jeki idan kin dawo zamuyi magana. Ta motse fuska don Sam acewar ta Bata ga mijin Aure a yanzu ba sai gashi Kuma ana son shigs Rayuwar ta Tasa me aikin su talatu ta biyota da ruwa da lemu inda ta yi gaba don zuwa duba wannan marar kunyar da aka jajubo Mata Ta taho tamkar tana Jin tausayin kasar fuskar ta murtuk Wai don kar yaga hakoranta ta shigo Babu ko sallama inda idanun su suka hadu su duka tamkar wuta taja su suka ji bugun zuciya Atare inda ta zauna tana auno mishi harara tamkar idanunta zasu fado inda talatun ta shigo dauke da tire Wanda ta jero ruwa da lemu tana Shirin ajewa humaira ta doko Mata tsawa..... "Koma da ruwan Nan talatu wannan ba bako bane abokin Adawa ne..... Talatu tayi dabar dabar don Bata fahimta ba inda kuma humaira ta Kuma daka Mata tsawar "Nace ki koma dashi ko bakiji ba? Da sauri talatu ta dauki tiren ta koma ciki inda ta fusknce shi shima Yana mamaki abinda suke nufi da turoshi inda atake ya gano gatan da dadyn yace yayi nufin yi mishi har yayi murmushi don yasan ba zasu taba daidaita wa da wannan marar mutuncin ba Murmushin shi ya Bata haushi. "Au harma na Zama abin dariya agareka ? "Uban me kazo yi agidan mu? Ko Nan ma kazo ne don ka sake bawa Yan sanda damar su kulle Ni ? Ta fada tana Kada kafa alamar masifa na Shirin tashi Ya Kuma yin murmushi Wanda ke kuleta da haushi da takaici "Kiyi hakuri Ranki ya dade............ "Kai bari fa in gaya maka dama inajiran Allah yasake hadamu don in Rama abinda kayi min To Ni nan da kake gani wallahi uban kuturu ma ya Yi kadan bare na makaho da ba gani yake ba duk uban da ya daure maka..... Ya gaji da Jin zagin da take mishi don Babu abinda ya tsana a Rayuwar shi irin zagi don haka ya cire hannu ya tsinke ta da Mari Marin da sai da taga giccin koriyar wuta "Nafi karfin zagi agareki ko Zan zagu ba dai ga irin ki ba jahila marar tsinkaye wallahi ba Irina Mata ke zagi ba nafi zagi ga irinki dabba dake Kuma in har kece ake Shirin abinda aka shirya zanyi maraba da hakan ko don in koya Miki tarbiyar da uwarki Bata koya Miki ba Ya Mike afusace ya watso Mata kudin da dadyn ya bashi ya Bata "Gasu Nan ki kaiwa Kabir mashi don saboda su yayi tallar ki inda ya San zai samesu Ashe ke da uban naki duk nema kuke akarkashi na to ku biyo Ni Zan baku na cin abinci Tana dafe da inda ya zabga Mata Mari har ya fice ta kasa cewa komai Akan cin fuskar da yayi mata Me yake sanar da ita? Da gaskene tallarta dadyn yayi? Eh ai in Bata manta ba dadyn ya fada Mata shi ya turo shi don haka ta tabbata sai dai tanajin ba abune me yuwa ba matukar Kuma akace hakan sai ya yuwu to za ahaife da marar ido Ta kwashe kudin ta nufi cikin gidan inda take ganin karfin halin shi na zuwa har cikin gidan su ya zabga Mata Mari Kabir ya tareta "Yaya Yar dady Yaya Kika ganshi ? Yayi Miki? "Wai dady baka San shine yayi min wulakanci har sau uku ba? "To dady bana son shi don fansa ma Zan dauka akanshi ba Kuma Zan kyale ba don bashi da mutunci to nima Zan gwada mishi bani da mutunci..... "A a karkiyi haka Anwar Yana da kirki Baki fahimce shi bane don haka dama fada Miki ne bamuyi Anwar shine mijin da aka tsayar Miki Nan da lokaci kadan za ayi biki..................... [5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 39* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........."A a dady wallahi bana son sa don ya gama saka min kiyayyar sa idan kuma kace Dole sai na aure shi to wallahi Zan bar gida ne kawai in SHIGA duniya........ "A a ba za ayi hakan ba cewar izzatu tunda dai Baki so an Bari. "To hakan dai yafi momy.... Ta fada tana hayewa saman bene inda Kuma Kabir yace "Ba fa Zan janye hadata aure da Anwar ba don auren su shine tabbata ta Akan aikina don auren ta zai zamo min tsani.......... "Nima ba zanso fasuwar auren ba Kabir na dai fada ne don kar ta gudu Amma ai gata can gidan Anwar din da haka suke rufe zancen Koda Anwar ya koma gida Mr President ya tambayeshi "ya ka ganta ne Anwar? Ya shafa sumar kanshi 'dady batayi min ba wallahi Bata da tarbiya......... "In Dan tarbiya ai me sauki ne Anwar sai ka dorata Kan irin taka tarbiyar munyi magana ne tuni da ubanta Kai ai Dan gata ne Mata biyu lokaci Daya? Tashi kaje zamuyi magana dashi Kabir din Kai dai ka zamo me adalci agare su Allah yayi jagora Ya tashi ya fito yanajin shi Kam baiyi sa ar aure ba don kaf Matan da ake Shirin bashi Babu wacce yake so Amma yanajin zaiyi biyayya tunda duka iyayen shi ALHERI suke nufin shi dashi don haka ya zari key din mota ya fice wurin abokin shi badamasi Wanda ya zamo Dan gidan Alh uba Dan yaro don ya sanar dashi irin auren da ake Shirin yi mishi Yana tafe kamar Wanda akacewa kalli can sai kawai idon shi ya hango mishi ummita wadda ke tafiya akasa zuwa kuki Gabanshi ya amsa inda ya kusa buga motar Amma Allah ya tsare ya dawo Kan doka da oda inda Kuma ya nemeta sama ko kasa ya rasa Haka ya Isa gidan su badamasi ya sameshi suka kashe inda badamasin ke fada mishi yanzu yake Shirin zuwa ya Kai mishi albishir din ya samo mata.......... "Kai Amma nayi maka murna don gara kayi aure da dai barikin da kake Kai ba mutumin banza ba Amma ka biyewa Matan banza nima dama nazo ne in fada maka yadda ake Shirin aura min Mata biyu Kuma duk cikin su Babu wadda nace inaso daya daga haj daya daga dady Amma yanzu tahowar Nan da nayi Allah da ikon shi nayi tsuntuwar soyayya Amma Wai kafin na kyafta ido har ta bace wa ganina Amma nayi alkawarin duk duniyar da tashiga sai na nemota nayi ta uku da ita......... Badamasi ya kyalkyale da dariya "Kai Amma wallahi su Dad sunyi min daidai Mata biyu lokaci Daya in ba irinku Yan gata ba Ya Mike da Shirin tafiya "Na lura ban baka tausayi ba badamasi Bari kawai in wuce tun baka

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});