Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yadda eng AK ya samu SHIGA fiye dashi matukar kuwa hakan yake nufi to zai ware kwanji sai ya dawo da bara bana Akan harkar shi da ake son yi mishi fin karfi Izzatu ma tamkar zata fasa kuka Amma tace itama ba zata taba yarda wani ak can da tagama rufe babin shi ya ce zai Kuma sake shiga Rayuwar ta da mijinta ba da sakel wallahi Aguje fulani take gudu akan hanyar don dama haka take Bata tafiya sannu sai dai tamkar zata tashi sama Cikin sa a ta shawo kwana daidai da wata katuwar mota itama ta shawo kwana Kuma hanyar Dole sai daya ya kauce kafin dayan ya samu zarafin wucewa Su duka suka sunno hancinan motocin su alokaci daya sukayi kallon kuda Atare inda atake ta ganeshi gayen Nan ne da yayi Mata Rashin mutunci har sau biyu dama neman shi take sai gashi sun Kuma haduwa inda zai Gane itama Yar zafin Kai ce Tama fi shi zafin Kai don haka sai ta kashe motar Taki fitowa shima ya kalle ta Yana mamakin kaddarar dake hadosu Suka Kuma yin kallon kuda inda yaga har da harara take Aiko mishi inda yayi murmushi Wanda ya kular da ita shi yaki yin baya itama Taki yin baya kowa na takama da zafin kanshi sai akayi sa a itace akan hanya shi in za a kwana bashi da damuwa ta Gane hakan ne ganin yadda ya tada kida amotar ya bawa banza ajiyarta inda ita Kuma aka fara Kiran wayarta don tana Kan hanyar zuwa bikin kawar tane Kuma itace babbar kawa shiyasa ma ta fito aguje gashi Kuma akwai tazarar da zata iya takawa kasa ba don haka kawai sai ta fito don ganin ya Dora kanshi akan sitiyarin motar Yana lumshe ido tamkar me bacci Kawai sai ji yayi gilas din motar tashi yayi Kara tatssss Ya dago da sauri inda yaga ta sauke katon dutsin akan gilas din motar shi wadda ita da kanta ta Gane tafi karfin yaro shiyasa ma ta ke ganin Yana ji da kanshi Abin ya Bata mishi Rai matuka gaya har Bai San lokacin da ya sauke Mata Marika biyu afuska ba abinda ya haddasa Mata daukewar gani na wucin gadi Lokacin da ta dawo duniyar mutane ne ta soma wanke shi da manyan asharai kafin ta fasa kuka ta Kira wayar izzatu take fada Mata ga Wanda ke Mata wulakancin Nan ya mareta har idonta ya fice........ "Kina Ina yanzu? Ta kwatanta Mata aikuwa izzatu ta Figo mayafi ta fice tamkar zata tashi sama inda ta Miki hanya sai gata agaban su fulani nata rera kuka Aguje izzatu ta fito ta soma wanka mishi Mari hagu da dama tanayi tana antaka mishi ashariya amma da yake namijin duniya ne Bai ko motsa ba Yana kallon yadda izzatu ke sauke mishi lodin zagi kala kala................ [5/19, 7:15 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 26* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........."Babu komai Anwar Rashin sani ne Kuma itama ai tayi maka Rashin mutunci Zan Kuma ja kunnen ta kaima kayi hakuri. Atake Anwar ya Kira wayar yasa aka saki su fulani inda Kabir yayiwa Mr President sallama ya wuce station ya kwaso su izzatu Wanda sukayi firgai firgai inda fulani ke ta kuka izzatu na Bata hakuri "Wallahi momy ba Zan taba kyale gayen can ba yayi min wulakanci Kuma yasa an kulle ki saboda Rashin mutunci ? Ko Zan kyale shi Akan abinda yayi min wallahi ba Zan kyale shi Akan kulleki da yayi cikin zarnin fitsari ba ko waye ubanshi kuwa duk Ranar da muka sake haduwa dashi Wallahi sai ya Raina kanshi da haka suka iso gida ta wuce ban daki don tayi wanka acewar ta duk zaurin fitsari take Shigar ta bandaki izzatu ke tambayar Kabir waye wannan yaron da yasa akayi musu wulakanci? "Anwar ne Dan gidan Mr President....... "Koda naji gadarar yaron ta nuna ya Taki wani Abu Amma Yana da hakuri gaskiya don inda yace sai yabi kadin ashar din da nayi ta banka mishi Babu shakka da fitowar mu ba yanzu ba......... "Ai albishirin ki ma kiji wani Abu da yasa nace gara da akayi Wai Mr President din ke nemawa Anwar din auren fulani Wai salon soyayyar sune haka........... Izzatu ta rangado guda me karfi inda take Jin tafi Kabir farin ciki yau ace yarta na auren Dan gidan shugaban kasa ita me yafi wannan farin ciki? "Kace gara da akayi Kabir ko ba komai lamarin zai zamo Mana tamkar jari don Dole ma abaka kwangila tunda ka zamo surukin masu Abu da kansu ....... "Ashe dai kin Gane Nima hakan nagani Zan dawo da martabata da ake son yi min fin karfi... "To Amma wani hanzarin ba gudu ba ta Yaya kake ganin yuwar lamarin alhalin fulani ta kullaci yaron ba kadan ba Kuma shima Ni Banga wani Abu da zai nuna zasuyiwa juna uzuri ba? Wannan me sauki ne idan akayi auren can zasu shirya kansu shima namiji yayi biyayya bare ita mace? Ai Dole ne ma tayi biyayya ke dai kar ki sanar da ita ayanzu sai lamarin ya tunkaro sai ta San komai da haka suka aje magana Dungo baiwar Allah ciwo yaki Jin magani duk Yan dabarunta na Shan magani Amma ciwo yaki inda ta siyar da Yan awakinta ta hada kudin da Basu Kai ko Rabin abinda ake nema ba ta nufi likitan ta Yi mishi bayani ya tausaya Mata matuka inda tace ya ajiye kudin hannunshi idan ta Nemo cikon zata zo ayi Mata aikin Ya karbi kudin sukayi rubutu ya Kuma nemi address dinta ta kawo shi har gidanta inda yake ganin kokarin ta na son ta taimaki kanta da kaucewa roko da tumasanci sai yake Jin ko da cikon ne ma zaiyi Mata in ta kama don haka sai ya saurareta Zaman gidan yayiwa ummita yawa inda ta nemi shiga makarantar koyon computer Kuma eng ya Goya Mata baya ta shiga inda take Jin ta rage kadaici Sai ya zamo ta fannin shaharar aikin kwangila ya zarta Kabir mashi kashe arna don gudar da akace za a rokar mishi ma ba a bashi ba eng AK aka bawa ita , idan har baiyi kuskure ba kusan wata goma Sha daya kenan Rabon da ace mishi ga aikin kwangila don haka yake ganin eng ne yayi mishi shigar sauri abinda kuwa ba zai yarda dashi kenan ba Izzatu da take ta durawa ak din ashar tace ya zamo Dole yaje ya samu ak ya yayi gargadin shi Akan ya Daina karbar kwangila sai dai ya Bari idan anyi a Yan mishi wani Abu Ai kuwa ya sallamawa eng Wanda ya fito ya tarbeshi suka gaisa inda ya fito mishi ta hanyar siyasa "Eng nazo ne inji adadin kwangilar da akace za a bani Amma shiru har yanzu sai ji nayi Wai an baka kayi ta harma ka Dora da wasu shine abin ya bani mamaki. "Kwarai kuwa me gida nayi ta har ma na dora da wasu guda biyu Wanda nakeyi yanzu. Amma

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});