Chapter 11
Chapter 11
huduba da sunan hajiya Mama wato bilkisu inda za a kirata da ummita Hidima sosai ak yayi tamkar Bai San zafin kudi ba tundaga Kan lubabatu har zuwa ummita inda akayi taro lafiya aka Kare lafiya lubabatu na kula da yarta wadda aka shiryawa gata da Jin Dadi ga Kuma kaunar Yan uwa da dangi na iyaye kasancewar an Dade ana jiran ganin ya'yan eng abdukarim din sai ummita ta zamo son kowa. Acan Kuma gidan izzatu tamkar ba gidan haihuwa ba saboda ta Raina ajawalin mutane ba kowane take ganin ya cancanci tayi Hulda dashi ba shiyasa Babu wasu mutanen kirki sai Yan uwanta suma ba kowa ba don yanzu ne zatayi maka Gori koma ta nuna maka iyakarka Ahaka dai akayi suna yarinya ta amsa sunan Aisha humaira inda izzatu ke kiranta fulani Wai alkunya ce irin ta Yar fari Sai dai abin haushi abin takaici Wai har akayi haihuwa har sai da aka kwana shida kafin Allah ya kawo dungo ba don ta San anyi haihuwar ba a a sai don ta duba izzatu don tunda tazo tayi mishi maganar zubewar katangar ta har yau din Nan Bai taka inda take ba Wai sai da tazo ta samu haihuwa har kwana shida gobe suna Ta cika da mamaki yadda Kabir ke kokarin mantawa da ita arayuwar shi Karin wani mamakin ma izzatu ta Hana dungon jaririya Wai bacci take yi Tayi Mata barka da sauke Kaya lafiya tayi nufin komawa gida don ko Kabir din ba zata tsaya gani ba Ta fito kenan motar shi ta faka inda yake ta shuga da fita akan hidimar sunan gobe sai kawai yayi karo da mahaifiyar tashi Wai sai yaji Bai kyauta Mata ba. Yafito Yana fadin yaushe tazo? "Yanzu nazo Kuma har Zan koma.... "Baba ba suna kikazo ba da Zaki koma?......... "Ina da wata martaba ne a idonka da zaka Fadi haka? Kuma ka fada min haihuwar ne da zaka zaci sunan ya kawoni? Atake ya Gane Yana Mata ba dai dai ba har ta Kai ga tankawa duk hakurin ta Da sauri ya soma tuba da Bata hakuri akan Wai ya shafa a ne duk da ranta ya baci Amma sai da tayi mishi uziri Kai lallai abar uwa da danta Da haka ya lallbota har ta yarda zata kwana ayi suna. Washe gari kuwa aka soma cin uban shagali Wanda Kabir ya Kashi kudi ba na wasa ba akayi taro aka Kare inda Kuma washe gari dungo tayi nufin wucewa birnin zazzau inda ya yi tsaye aka debar Mata nama me yawa acikin kattin Rigunan da ya yanka ya Kuma hadota da kudi masu dama ta wuto tana addua da sa albarka Haka humaira fulani aka ci gaba da rainon ta itama da shirya Mata ALJANNAR DUNIYA komai ya tafi daidai Sati biyun da sister mero ta diba Bata Kara ko awa da minti ba ta diro gidan izzatu wadda sai da akayi da gaske kafin a samo Mata maganin da zata Sha ruwan nononta ya Zo don ta gilla karyar Wai Bai zo ba ne inda cikin Yan aikinta wata ta sanar da ita agarin su da akwai me bada magsnin irin wannan matsalar a garin dutse ta jihar jigawa don haka ta hada Mata tafiya taje ta Kuma tako sa a har tayi amfani dashi Kuma ruwan nononta ya Zo don haka take shayar da fulani inda Kuma a yau sister mero ta diro gidan don karbar hakkinta Ta shigo gidan ta samu izzatu na bawa fulanin nono inda ta dubeta a sheke ta watsar ta zauna akan kujera tana duban izzatu dake Mata kallon ke kadai Kika San sirri na "Gani na biyo hakkina sati daya Kika bada Ni Kuma bayi biyu ai na daga kafa ko???......... [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *page 17* *_insha Allah zamu koma muku posting a Rana so uku safe Rana da dare in hakan Bai samuba zamu koma so biyu a Rana in Allah ya Yar da_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .......... Izzatu ta dubi mero cikin Jin haushi da takaici . Mero ta dubeta yadda take Brest feeding din yarinyar tamkar itace asalin uwar ta ta gaskiya "Uhum kinganki kamar dai ace da gaske kinji yadda akeji sai kokarin feeding ya akayi ma maman yazo? "Ba damuwar ki bace Ni bansan haka kike ba mero da ban hada tafiya ta dake ba Ina amfanin tafiya da matsiyaci? "Na ma fi da haka matukar kikce Zaki dawo min da bara bana akan hakki na don haka tashi ki dauko min in wuce me motar da na siya ya isheni da na kawo mishi kudin shi Izzatu ta Mike tana Saba fulani akafada tana fadin Banga amfanin tarayya dake ba tunda Baki da mutunci Ta shige daki ta rubuto check na milyon biyar ta Miko Mata "Sai abi wani sarkin ba na garin mu ba Mero ta dubeta tana kallon ceck din da take Miko Mata "Ai bamuyi dake Zaki bani takarda banki ba cash kikace Zaki don haka koma ki dauko min kudi na daidai. "Banda su ajiye sai dai kije banki ki karba ta fada tana cillo Mata ceck din afuskar ta Mero ta dauki cack din tana duba inda tayi arba da rubutun milyon biyar Ta dubeta "Ya Naga kin rubuta min milyon biyar amaimakon goma? "Biyar din Naga damar Baki don ko ke Kika yi cikin Kika haife iyakar ta kenan Mero ta Mike tsaye tana kwabe gyalenta ta na cin damara a kugun ta "Bari kiji in fada Miki izzatu bafiki iskanci don ni har takardar shaida sai da na Kama don haka bini sannu ko yanzu in fasa kwai rubuto min cikon kudina in wuce in ko Kuma yanzu in iske Kabir mashi in fasa mishi Kwan kigani idan Baki kwana gidan ku ba Da gaske kuwa ta Kada hantar cikin izzatu inda har ta rubuto mata cikon kudin ta tabata . "Ai kuwa godiya ma ya kamata in Miki don kuwa kin yi min silar farin cikin da ba Zan iya manta shi ba na gode sosai Allah ya Kara daukaka "To ameen in da gaske kike in ma ba gaske ba ne Allah ya biye bakinki Nima na gode da samun abinda ban taba zaton samu ba sai gani na biyu..... "Bana bukatar ganin ki a gidana don Zaki iya Zama barazana ga Rayuwa ta mu hadu Nan mu Rabu Nan Sister mero tayi murmushi ta fice inda ta shige mota ta nufi banki don ta fito da kudi ta biya me mota kudin shi. Fitar sister mero ya bawa izzatu damar kamo bakin zaren wani mugun qulli da tayi nufin zargawa mero Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira wani Dan ta Adda da ta sani Wanda ya taba yiwa wata kawarta aiki har ta zarga nata mugun qullin Don haka ta Kira wayar gambo mafiyas Wanda ya kware a iya Sara suka da ta addsnci Kara biyu gambo mafiyas ya daga "Allah ya taimaki hajjyata ta samu ne? Kwarai kuwa gambo maza kazo Ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31