Chapter 24
Chapter 24
ya samu acikin motar inda daga can baya Kuma cikin masu jiran go slow Kabir masi ya fito daga tashi motar ya karaso wurin inda shima yaga abinda ake mamakin gani amotar abdulkarim "Wai abdulkarim Kaine da part din mutum a mota? Eh lallai da gaske kake har da tsafi kake hadawa shiyasa ka shiga gabana to Allah ya shirye ka ya fada Yana murmushi ya koma motar shi Yana kallo aka fidda motar eng abdukarim aka saka Mata key aka kulle shi Kuma aka wuce dashi sashen da zai bincike shi yayin da Yan sandan suka ci gaba da bincike motocin mutane Da wata irin dariya Kabir ya SHIGA gida inda izzatu ta tarbeshi tana tambayar dariyar Nan ta lafiya ce? "Ki tayani dariya don ya akan idona Dan banzan can AK ya shiga hannu shigar da ba zai taba fita a yanzu ba. Kai lallai na yabawa gambo mafiyas akan wannan aikin nashi Dole ne in mishi biya me kyau, Izzatu ta kyalkyale da dariya tana fadin nasan gambo mafiyas ya fi da haka Amma ya akayi har hakan ta faru? "Nima ban San yadda gambon ya shirya wannan makircin ba ya dai kirani ya fada min abinda Zan sanar da Jami an tsaro na Kuma fada musu sai gashi akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai Amma Bari in Kira gambo mafiyas din yazo ya karbi kudin shi kuma inji yadda ya shirya wannan makircin Ya dauko wayar shi ya Kira gambo ya ce yazo yanzu Ai kuwa ba a rufe awa guda ba sai ga gambo mafiyas Kabir ya daga mishi hannu alamar jinjina inda gambon ke murmushi "Me gida kaga aiki ne Hala? "Naga aiki gambo don akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai ya akayi ka shirya mishi hakan? "Ai me gida na Dade ina binshi sannu ahankali har na samu sa ar ya bude but din na fakaici idon shi na saka mishi hannu da kafar shiyasa nace ka sanar da hukuma don ta fara binciken motocin ta yadda Za a kamashi kaga idan aka samu wannan abin a motar shi Dole za a shiga bincike kaga daga Nan sai sunan shi ya baci har ya Kai Babu me kallon shi bare sunan shi ya motsa Izzatu da Kabir suka tafawa gambo mafiyas akan makircin shi Kabir kuwa ya bashi kudi masu yawa ya Kuma ce zai neme shi matukar wani zai yi mishi shigar sauri irin na ak to yanzu ne zai Kira shi don yayi mishi maganin shi da haka sukayi sallama gambo ya wuce Yana murna izzatu da Kabir ma suka wuni farin ciki sun jefa Rayuwar bawan Allah cikin garari.................... [5/22, 7:24 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 34* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Bincike tamkar za a binciko yadda uwa tayi ciki har ta haife lamarin da yazo mishi da wani irin rudani har yakasa Gane inda mafita take bayan ta Allah Yasha tambayoyi har na tashin hankali inda lamarin ya koma hannun C I D inda kuma suka rikeshi Wai sai sunyi bincike agidan shi Wayarshi ma kasheta akayi don kar ya Kira wani ko wani ya kirashi, Lubabatu da sukayi dashi ba zai wuce shida na maraice ba gashi har takwas da Rabi tayi mamakin abinda ya tsaidashi don ta San baya son yayi sallar magruba a waje Ta jawo wayar ta ta doka mishi Kira Amma abin haushi matar Nan me zakin muryar tsiya na sanar da ita sai dai ta sake Kira lokaci na gaba yanzu Wai ba za a samu layin ba Haka tayi ta jaraba Kiran wayar shi Amma ta kasa samun shi Dole ta hakura ba Kuma hakura tayi ba tunanin abinda ya tsaidashi da kuma Rashin samun wayar shi don tasan ba lafiya ba don ta San wayar shi Yana da caji Ummita ta shigo Mami Ina Abba ya shige yau har yanzu Bai dawo ba? "To Ni kuwa ina Zan sani ummita? Gaba na dai na faduwa don na fara tunanin ba lafiya ba............ "Mami bara na Kira wayarshi naji inda ya tsaya................ "Wayarshi Bata shiga na Kira na kasa samun shi Ubangiji yasa dai lafiya. Hankali ya kasa kwanciya inda ummita tace zata Kira haj mama taji ko ta San inda abban ya shiga Amma lubabatu ta ce ta saurara tukuna Sai dai har Sha dayan dare Babu wani Abu ko da na samun wayar shi ne Dole lubabatu ta Kira wayar haj Mama wadda har ta fara bacci ta jiyo karar waya ta farka tana tambayar lubabatu lafiya kuwa? "Hajiya AK ne har yanzu Bai dawo ba Kuma duka layikan shi arufe shine ko ya fada Miki zaije wani wuri? "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Wallahi lubabatu bai fada min ko zaiyi tafiya ba Kuma kince duka layi kanshi basa aiki ? Eh wallahi hajiya Amma Bari na Kira abokin shi zayyan ko ya san inda yaje da haka lubabatu tayiwa haj mama sallama ta Kira wayar zayyan din take tambayar shi ko yaji AK din zaije wani wuri Amma ya sanar da ita Bai sani ba Rabon shi dashi tun la asar. Hankalin lubabatu da ummita ya tashi matuka gaya har dai bacci ya gagari idon su suka kwana salla suna fadawa me babbar rumfa me iko akan komai me tassarufin Al amura haka suka kusa kwana zaune inda Mubarak da Ahmed da Fatima ke ta sharar bacci abinsu saboda yarinta da kuruciya Wayewar garin na laraba yazo musu da wani irin tashin hankali domin ko Jami ai ne daga hukumar bincike ta C I D suka diro gidan eng abdukarim inda lubabatu ta rude da Ganin su suka Fara yi Mata bayani "Karki damu hajiya tambayoyi ne kawai Zaki amsa Mana da Kuma binciken da zamuyi agidan Nan saboda an Kama me gidan Nan da part part din mitane amota................ ",Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un hasbunallahu wa Ni imal wakil Allahumma ajirni fee musibaty haza wa ahalufnee khairan minha. "Abdulkarim din ne akewa wannan zargin? Ubangiji ka bashi mafita da mafitar ka........ "Kar ki damu hajiya bincike muke tukuna ba Wai an tabbatar ba abinda kawai muke so shine ki bamu hadin Kai mu gudanar da binciken komai zai daidaita da yardar Allah, Ta share hawayenta da habar hijabinta ta soma amsa masu duk tambayoyin su har suka Kare suka shiga bincike gidan shima Allah da ikon shi ko wata kakkaifar wuka Basu samu ba da haka suka kammala sukayi Mata sallama bayan sun sanar da ita Yana hannunku Kuka ummita keyi tamkar zata hadiye zuciyar ta inda lubabatu ma ta ke nata kukan sai yaran ma suka dauki kukan Babu Wanda yayi kokarin rarrashin wani inda Kuma haj mama ta taho gidan don taji ko AK din ya dawo don itama ta nemi wayar shi yafi akirga Amma Bata sameshi ba sai ta iske iyalan gidan sunata rizgar kuka Hankalin ta ya tashi inda lubabatu tayi shiru tana korawa hajiyar bayani abinda ya gigita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31