Chapter 16
Chapter 16
Allah "To Allah ya rufa asiri dama cikon kudine so yayi min don Zan siyar da Yan awakina in nemi magani ........ "Ai da kin bugo waya ba ki wahalar da kanki ba yanzu irin haka ke Dadi kinzo kin Bata kudinki Kuma ba lallai ki samu kudin ba Sai izzatu ta SHIGA sababi tana fada Wai ba a haka sanar da mutum ake in za a zo wurin shi ba Wai azo ayi mishi tashi na kamaka ba in turawa ne in baka sanar dasu zuwanka ba ko ruwa ba zasu baka ba Haka Kabir ya dawo ya samu tsohuwar shi cikin halin ciwo Kuma ko ruwa ba a Bata ba bare abinci. Kafin ma ta sanar dashi matsalar ta izzatu ta rigata inda ta Dora da Wai Babu kudi yanzu Shima sai yabi bayan matar tashi akan dai Babu kudin don ya Gane izzatu batayi na am da bayar da kudin ba Dungo tayi murmushi "Babu komai Kabir ko aro ne anemo min ciwona Yana bukatar gaggawa....... "Gaggawa Kuma ? Yo dungo ko mutuwa ta shiga gidan da Babu ai dolenta ta fita Kabir ya dubi izzatu Yana mikewa inda ya nufi daki ta bishi "Gaskiya baba Bata da lafiya izzatu Bata taba tambayar kudi wurina ba So Zan Bata duk abinda take bukata........ "To kudin da zaka bani na bikin Barth day din fulani fa ? Shiyasa kaji tun farko na ce baka da kudi ka Bata kudin mota kawai ta koma gida zuwa wata me kamawa idan sun samu sai abata don hidimar zatayi maka yawa Haka kuwa akayi ya dawo ya sanar da ita ya buga waya ko rancen ya samu Amma abin ya gagara da haka ya aje Mata dubu biyar yayi Mata fatan samun lafiya Ta Dade zaune tana Kore sauro inda kuma har yanzu ba a Bata ruwa ba bare abinci Fulani ta fito ta dauko Mata robar madarar laban da abinci Wanda ta zubo Mata naman kaji zuku zuku ta dire gabanta "Ya Kaka Baki Jin yunwa kikayi shiru Baki Sha ko ruwa ba? Ta karbi madarar ta soma Sha kafin ta soma cin Naman inda wani ikon Allah sai taji kamar ana rage Mata ciwon Ni Kam gidan iko nace ko ciwo Yana son abinci me kyau Adakin humaira ta kwana cikin gidan sauro inda dungo ke ta saka Mata albarka washe gari ta hado kayan ta fulani ta kawo ta Tasha inda izzatu ke taksicin wannan kawa zuci na fulani ga jemammiyar tsohuwar Ai kuwa da ta dawo daga Kai dungo Tasha sai da taja kunnen ta kamar ta cire shi tana fadin Wai Babu ruwanta da tsohuwar "Haba momy kakata ce Kuma ace Babu ruwana da ita? ...... Ta gwabje Mata Baki "Baki hada komai da ita ba hanya ko ta rafi nono ko na gora meye hadan kifi da kaska? Fulani ta shige daki tana gunin Jan kunnen ta da akayi inda Kuma sister mero ta shigo gidan da sallamar ta me kwari. Arude izzatu ke kallon ta "Me ya kawoki gidan Nan mero? Me kikazo yi ? "Haba irin wannan tambayoyi tamkar na SHIGA kabari ko Dan ruwa ba za a bani ba ? Bakonka Annabin ka fa...... "Baki cikin layin bakon ka Annabin ka donke kallon tauraruwa me wutsiya nake Miki don haka Fadi abinda ya kawo ki kiyi ki bar min gidana.......... "Kai hajjaju makkatul mukarramina wannan dogon sharhin tamkar Baki San daga ina nafito ba? To dama matsalar kudi ce ta kamanni shine na tuna dake don haka milyon biyu kurum nake so ba yawa....... "Agidan ubanwa za a samo milyon biyun? Wace irin jaka ce ke ne? Kina bina bashi ne Zaki wanko tsantsaman jikinki kice na Baki kudi? "Karki Kuma zagin ubana izzatu arziki ya hadamu ba tsiya ba ke komai sai an biyo Miki ta bayan gida ake daidaita wa dake? Meye don nace ki bani milyon biyu Ina ce farin cikin da na Samar Miki ya zarta milyon dari? To bani in wuce don bana son ta kaimu ga cacar Baki in kuwa ba haka ba wallahi yanzu ne Zan fasa kwai ......... "Allah ya tsine Miki idan Baki fasa dangin kaji da tsuntsaye ba. Bari in gaya Miki mero na fiki tashanci da iya lalata ban San haka kike ba wallahi da ban yarda na hada hanya dake ba Amma ki sani duk Ranar da Kika kaini karshe na rantse Miki da Allah sai dai ki tsinci kanki kushewa Zan Baki milyon biyu Amma ki kaddara daga kanta ko a mafarki kar ki yarda kice kin sanni don sani na zai zo Miki da matsala.......... "To naji hajiya izzatu dauko min in wuce don sauri nake. Izztu ta rubuto mata cek ta Bata ta karba tana godiya inda izzatu ke Mata kashedi da idonta Sister mero ta Mike tana fadin Wai sai gani na biyu....... "To a gani na biyun ki tabbatar kin taho da likkafanin ki don Zaki zo inda Zaki gama yawo. Mero ta kyalkyale da dariya ta fice daga gidan inda izzatu tayi shiru tana tunanin mero da irin salon da take nufin kawo Mata Itama sai tayi murmushi"mero kenan muje zuwa Ni dake za agane waye gaba......... [5/17, 10:10 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 24* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Bai Kara tunawa da batun wata halitta Wai ita dungo ba asalima tun da ta tafi ya share da lamarin ta inda aka kashe kudi sosai wurin yiwa fulani bikin murnar cikar ta Sha bakwai da haihuwa akayi taro na manyan Yara ta Kuma samu kyaututtuka daga kawayen ta na karatu Kana biyu da yin bikin yake sanar da izzatu anyi mishi alkawarin bashi kwangilar gyaran wutar lantarki wadda zai samu manyan kudin na tashin zance inda ta cika da murna don duniyar su zata Kara haskawa Sai dai me ? Maimakon yaji Kiran daga fadar me bawa shugaban kasa shawara Kan abinda ya shafi aikin. Sai ji yayi Wai har anyi kwangilar an gama har ma an Dora da wasu manya har uku Kuma Babu wadda ta fito da sunan shi sai sunan eng AK Wanda a yanzu shike Kan gaba na karbar kwangila daga gwamnatin tarayya abinda ya girguza Kabir mashi har ya gurfana agaban me bawa shugaban kasa shawara "Ranka ya Dade na tuba don Allah a gafarce Ni idan har da kuskure a cikin aikina to asanar Dani Zan gyara ban San abinda nayi ba aka mayar Dani gefe anyi mini alkawarin bani kwangilar gyaran wutar lantarki Amma sai ji nayi har anyi ta angama menene laifina? Alh uba Dan yaro ya dubeshi "Agaskiya Kabir sunyi bincike ne akanka inda suka gano kana bada rata da yawa har aikin ya zamo Babu nagarta inda sukace aikin eng AK yafi naka nesa ba kusa ba shiyasa suka juya akalar Kan shi Amma idan zaka gyara ba damuwa bace sai nayi maka request wata ta gaba abaka don nasan wata Kil waccan akasi aka samu Ya zube Yana godiya da alkawarin zai gyara da haka ya taso ya taho Yana mamakin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31