Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Zan Fasa Kwai Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ko Zaki iya zuwa? "Eh Zan iya malam gobe zanje in Sha Allah sai afadawa su Jamila naje abuja don yau lahadi na San gobe litinin zasu kawo yaran su "To Babu matsala Allah ya kaiki lafiya ya dawo dake lafiya yasa kuma adace ya tashi kafadunki.. Ta amsa da Allahumma ameen Washe gari ta bugi hanyar abuja............... [5/16, 9:33 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 21* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........A yanayin tsarin halitta humaira fulani farace Amma ba irin farin Nan me haske sosai ba da kadan tafi wankan tarwada sai dai akwai wani Abu Wai shi kyau ga Kuma diri me tsari don dirarriyace me daukar hankali Bata Faye son yawan kwalliya ba Amma duk shigar da tayi zata karbeta Kuma ta zamo Zara cikin taurari akwai yauki da yanga da Kuma nuna matanci sai dai tsabar dagawa da izgili har da izza to dama yaushe barewa ke gudu danta ya rarrafa? Agefe Daya Kuma tsarin halittar ummita ya zamo Fara ce tas har tana yellow yellow ita kuwa macece me son ado da kwalliya Kuma idan tayi kwalliya Kai kace Yar tsanace Bakinta dauke da siririn hakorin makka Wanda shekarar da ta wuce ne abban nata ya biya musu kujera su duka hada haj mama sukaje suka sauke farali dama hakorin makka na burgeta sai Kuma akayi sa a ta sanyo shi inda ya Kara fito da martabar ta inda samari ke ta kawo mata Hari Amma Allah Bai sa taji tana son tsayawa da su ba inda Kuma abbanta yace ba yanzu ne zata soma magana da samari ba sai dokar tayi Mata Dadi ta kulle su ta jefar da makullin Ta kwashi su Mubarak a motarta da abban ya siya Mata elements suka nufi sahad don Allah yayi ta me son kayan makulashe dangin Zaki shiyasa Bata sati Bata zo sahad ba yadda take son chocolate da biscuits Bata damu da abinci haka ba shiyasa take kwaso kannenta suzo sahad ko jifatu su kwashi abinda suke so Ta faka motar a parking space dai dai da da fakawar wata katuwar mota kusa da inda tayi parking cikin Rashin sa a kyauren motar ya gogi motar da ta faka kusa da ita. Fulani ta fito tana kallon yadda kyauren ya Dan gogi motar ta ta lailayo wata ashar marar tsarki ta antakawa ummita ta fito tana Bata hakuri.....Kafin ta cire hannu ta tsinkawa ummita mari "Ubawaye ubanki agarin Nan da Zaki gogae min mota.? Wannan shegiyar motar Taki me kama da amalanken shanu ita kike kokarin lalata min tawa motar da sai ta siyi Taki hudu ko biyar? Ummita ta dubeta tana dafe da inda ta mareta dayake ba me son tashin hankali bace sai ta kuma Bata hakuri tana fadin ba da gangan tayi Mata kuskure ba Haka fulani ta wuce tana sababi inda ummita ta sauke ajiyar zuciya taja kannenta suka shiga cikin sahad din inda Mubarak ke fadin shi fa sai yaci ubanta idan ta kuma zagin ummitan....... "Rabu da ita Mubarak Allah ya hada ta da daidai ita Ni bana neman tashin hankali. Haka suka SHIGA suka judo kayan kwalam din su fal ledoji inda itama fulani ta siyo ice cream da da wasu abubuwan inda suka fito kusan Atare ummita na mamakin ta Akan zafin Kai da zuciya Adaidai kofar fita fulani ke gaba su ummita na bayanta inda sukayi taho mu gama da shi, shi zai shigo ita Kuma zata fita suka gwabza wani irin karo Wanda har kayan hannunta suka tarwatse ice cream din ya watse ajikinta ga Kuma goshinta da suka gwabza karo ya daku sosai "Ya subhallah ya fada Yana dafe goshin sa da yaji Yana mishi radadi ya duka Yana tattaro Mata kayanta da suka zube kasa ya kwaso su Yana Miko Mata inda zuciya ta ciyota maimakon ta karba sai kawai ta gaura mishi Mari tana sababi "Dabba da Kai zakayi min Bari salon kayi min sata banza matsiyaci". Ya dubeta Yana shafa inda yaji tafin hannun ta kamar shi namiji me jini ajika ace mace kamar wannan ta cire hannu ta tsinka mishi Mari ? Sai yaga ai shi yayi Mata laifi Don haka yace ta Bari ya SHIGA ya amso Mata kayan da yayi Mata asara.... "Kaine matsiyaci kaje da sauran ma na bar maka tunda dama kazo kayi min sata ne... Ta wuce fuuu ta bar shi da yi Mata rakiya da ido , Amma lallai yarinyar can ta sameshi da yawa yadda yake da zafin Kai Amma ace har amare shi Amma bai dauki mataki ba? Yana kallonta ta fice aguje ta bar sahad din inda su ummita da kannenta suka fito Mubarak nacewa "Kinga Allah ya saka Miki anty . "Uhm na gani Mubarak Kai dai bi duniya a sannu don Bata da tabbas itama Ina rokon Allah ya shiryeta don wallahi naji Ina son ta duk da abinda tayi min...... "Wallahi Ni bana sonta anty tunda Bata da kirki. Ummita tayi murmushi tajawo mota suka dawo gida Inda Mubarak ke fadawa ummansu abinda ya faru asahad ummita tayi mata bayanin komai haj lubabatu yace Allah ya kyauta sai ki kula . Ita kuwa fulani ko da ta fito daga sahad sai ta zarce jifatu ta siyo abinda take muradi tana tafe tana sababi da tijara ita kadai inda tazo dai dai traffic light ta tsaida su. Nan ma said masifa take Akan jiran traffic din inda ta waiwayo bayanta taga dogon go slow din da aka hada inda motar dake bayan ta ta hango gayen da yayi Mata Bari abakin sahad Taja tsaki tana Jin tamkar ta fito ta shake shi inda kuma traffic ta Basu hannu Amma tayi kunnen uwar shegu Taki matsawa saboda Wai ta Rama abinda yayi Mata. Aka ci gaba da danno Mata horn Akan ta matsa gaba Amma ta share sai ma latsa kida a CD ta Kuma Ware kidan.............. [5/17, 10:10 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 23* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Cikin ikon Ubangiji ta iso garin Abuja sai dai zaman mota ya jigatata don haka da kyar da gano gidan Kabir inda take ta shessheka numfashi na neman daukewa tamkar me ciwon asma Fulani ta tarbota don wani ikon Allah jinin su ya hadu Ta rungumota tana fadin "Ya Kaka Baki da lafiya ne? Da kyar dungo take magana "Bani da lafiya Aisha ina mutanen gidan ne? Izzatu ta fito ta aunowa fulani harara don Bata so take shiga sabgar tsohuwar "Tashi ki bace min da gani kilbabbiya, ta fada tana hararen humairar Ta tashi ta nufi dakin ta tana tausayin kakarta Izzatu ta dubeta tana dafe da gefen cikinta alamar ciwo yake Mata "Baki da lafiya ne dungo? "Wallahi kuwa izzatu jiki yaki Dadi Allah yasa Kabir Yana gari ? Yana Nan sai dai inma kudi Kika zo nema bashi dasu don kwanan Nan lamarin sai godiyar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});