Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

same ni a d'aki ina shiryawa domin fita aiki, "Asibiti zan je." ta fad'a kamar bata so. na ce" Ai yana da kyau, dama tuntuni nake ce miki kije domin a duba lafiyarki, data baby, yanzu me kike bukata?" "Ku zaka bani." a lokacin na dauki dubu biyu na bata, tayi wa kudin wani irin riko kafin ta ce"Dubu biyu me za tayi min gaskiya sai dai na fasa zuwa" Na ce" Yau ban tashi da kudi ba, kiyi hakuri kiyi maleji mana" "Gaskiya ba zan iya ba" tafad'a tare da ajiye min kud'in tana kokarin fita, sai na ce "Zo ga dubu daya na kara miki." Ta ce" Dubu biyar zaka bani domin har scanning za ayi min." Da yake ina so taje asibiti a lokacin, haka na dauki dubu biyar din na bata, ashe zubar da cikin suka tafi. Ni dai na dawo gidan na ganta a galabaice, na ce" lafiya dai." sai ta ce" Gajiya ce kawa." Na ce" Ba kiyi girgi ba kenan? kai ta daga alamar eh! da kaina na shiga kicin din nayi mana shinkafa da wake. Da daddare kafin mu kwanta nake tambayarta takardar scanning, sai ta ce" ai sakamakon bai fito ba." ban kawo komai a raina ba, na kwanta domin huta gajiya. Sati biyu da faruwar al'amarin, sai naga ta warware! tana ta walwala babu alamun laulayi a tare da ita, al'amarin ya bani mamaki sosai, na ce" Da alama dai magungunan da na siyo miki suna da kyau, naga kwana biyu kin samu lafiya" Ta'be bakinta tayi can kasan ma'koshi ta ce" Na dai rabu da jaraba." Na ce." Me kika ce?" shuru tayi bata tanka ba, sai nasha jinin jikina domin duk da tayi maganar a can k'asan mak'oshi, sai da na fahimta. Na ce" Baki da gaskiya Fatima kin rabu da jaraba ko?" Ta ce" Eh mana ni wallahi ba zan haihu yanzu ba." Gabana na faduwa na ce" Me kike nufi kenan?" "Zubar dashi nayi" ta fada hankalinta kwance! Ban san sanda na kai mata wani mugun mari ba wanda yasa hancinta fitar da jini! Jikina na rawa na ce" Cikin nawa ki ka zubar akan me?" Ta tashi tsaye hannunta dafe da kumatunta ta ce" Saboda yana bani wahala kuma ban shirya haihuwa yanzu ba" A zafafe! na sake zabga mata wani marin! na ce" Me na rage ki dashi a gidan nan? duk neman da nake akanki yake 'karewa, me yasa za kiyi min wannan wulakancin?" Tana kuka take fadin" Kada ka sake mari na" na ce " Duka zanyi miki ma yanzu" da sauri na je na rufe kofar d'akin, na sanya blet na zane ta ciki da waje sai da na huce! fushina! sannan na kyale ta, na ce kuma lallai kada na dawo na sameta a gidana. Tana kuka take fad'in"Ai dama ko baka fad'a ba, mugu azzalimi kawai" fita kawai nayi na k'yaleta domin idan ba hakan nayi ba, to zan iya kashe ta har lahira, saboda takaicin da ta 'kunsa min." [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 73&74 'Bacin rai ne mai tsanani ya biyo bayan al'amarin da ya faru tsakanina da Fatima, domin zuwa tayi ta juya maganar, ta ce na rufe ta a daki nayi mata dukan tsiya! har sai da cikin jikinta ya zube! duk yanda naso da na kare kaina abin ya fassakara domin babu wanda ya tsaya ya saurareni, mussaman mahaifiyata da ta dauki fushi! mai tsanani! wanda ya d'aga min hankali mutu'ka! na dinga bata hakuri, amma fafur! taki saurarata, sai dai 'kyar na samu tayi min magana kan cewa; muddun ina so naga farin cikinta, to naje na bawa matata hakuri akan abinda na aikata, sannan na nemi gafarar Hajiya da shi kansa Baba Auta, to fushin Ummana yana da ala'ka da rashin kwanciyar hankalina, wannan dalilin yasa dole na sauke duk wani 'bacin raina, na je na samu Hajiya na bata hakuri, itama dai magana d'aya ce wato na je na bawa Baba Auta Hakuri da 'yarsa, haka nan, ba don raina yaso ba na nufi gidan, sai dai nasha wulakanci ba k'arami ba a gurin Baba Auta ya dinga nannago ba'kaken maganganu ya narka min, haka dai na daure na dinga bashi hakuri, kafin ya bari Fatima ta dawo gidana sai da ya kafa min sharad'ai! na ce na amince duk don samun zaman lafiya, da gujewa fushin mahaifiyata. To koda ta dawo gidan, sai dana kai zuciyata nesa sannan na fara mu'amula da ita, amma na daina sakar mata fuska, kuma na sanya mata matakan tsaro sosai domin na hana duk wasu 'kawayenta zuwa gidan. Da yake idan na fita tun safe bana dawowa gida sai wajejen sha biyu na dare, domin wani sa'in da daddare kasuwa tafi bud'ewa ga wad'anda basu da bukatar shiga gidan mai, sai su tsaya a gurina su saya, gefe guda kuma idan faci ko gyara ya samu ina yi duk domin asiri na ya rufu. Tun safe na tashi da ciwon kai, na san hakan baya rasa nasaba da rashin samun wadataccen bacci, na daddafa na fita domin nasan ko na zauna a gidan don hutawa, 'bacin rai ne zai biyo baya gwara fitar tawa tafi alfanu. Ina tsammanin ko rabin awa banyi da zama gurin aikin ba, na kasa jurewa domin saboda tsananin ciwon kai har jiri nake, sai na yanke shawarar komawa gida na samu nasha magani na kwanta Sai dai me? tun daga nesa na hango 'katon 'kwado! a jikin kofar gidan, raina ya 'baci ainun! wato a duk sanda na sanya 'kafa na fita daga gidan, itama rufewa take ta tafi nata guri. Allah yasa ina da mukulli a hannuna kawai sai na bude gidan na shiga, yanda na fita na bar shi a hargitse babu gyara haka yake bata gyara ba. Damuwa sosai na shiga da wannan abu da faru, kuma zuciyata ta dinga munanan tunane-tunane a kanta. A takaice! dai Fatima bata dawo gidan ba sai bayan isha'i! tayi sallama ta shigo jikinta duk a sanyaye, lokacin ina kwance kan doguwar kujera na d'an ji dadin jikina, sakamakon magungunan dana sha, amma duk da haka sai da mai chamis din ya bani shawara cewa naje asibiti likita ya duba ni saboda yanda nake kuka da ciwon kai. Ta zo ta tsaya a kaina tana wuri-wuri! tare da shirya karya da gaskiya, wai gidansu taje Mamanta bata da lafiya. Na kalleta kafin na ce"Kin san dai ban yi kama da wanda zai yarda da wannan shirmen ba ko?" "Wallahi tallahi ba 'karya nake yi ba ko za kaje ka tambaya ne" Tafad'a tana kokarin kare kanta Zaune na mi'ke na d'aga mata hannu da fadin " Ki fad'a min gaskiya idan kina so ki tsira da lafiyarki, don wallahi tallahi rufe kofa zanyi naci ubanki sai dai duk abinda zai faru ya faru.'' "Ubana kake zagi?" ta fad'a tana nuna 'kirjinta. Na ce" Ba shine yake daure miki gindi ba?" Shuru tayi tana kallona . Na ce" Na fi ki iya sharri! da mugunta! Fatima, duka zanyi miki na zubar miki da ha'kora! don ba zan yarda da munafurci ba, da aure na ki ke zuwa kina neman maza a waje" Sai ta fashe! da kuka da fadin" Wallahi

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});