Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

duk maganganunsa akan hanya suke, yanda yake rantsuwa da Allah a kan 'kaunar da yake min, hakan ya 'kara min 'karfin gwiwa, sai dai kuma tils na cigaba da addu'a akan Allah ya kore mana fitina a cikin al'amarin. Tare muka ci abincin, yana ta jana da hira, ni dai umm kawai nake cewa, sosai ya warware kamar ba mara lafiya ba, ya saki jikinsa yana ta zuba min kalaman soyayya wanda suka ragargaza min ga'bo'bin jikina, domin da abincin ma wai a baki zai ba ni, na no'ke don gabad'aya kunyarsa nake ji ganin kamar yana so ya wuce gona da iri. Har dare ina d'akinsa kunya nake ji na sauka 'kasa, shi kuma tun bayan da ya fita sallar magariba bai dawo ba, duk na takura! a dak'in, gashi ina da bu'katar zuwa tsohon guri na, domin d'auko rigar bacci amma ya hana ni, daga ni sai doguwar rigar atamfar dake jikina sai kuma mayafin dana yafo ina zaune nayi tsuru tare da tunanin abunda zai faru tsakanina dashi a wannan rana. [1/12, 11:28 PM] GARKUWAR MATA: 90&91 Hajiya da kanta ta shigo ta kawo mana abinci. Fuskarta kawai na kalla na fahimci cewa tana cikin farin ciki da abinda nayi, don babban burinta shine na zauna tare da su, ganin haka yasa na k'arawa kaina 'karfin gwiwar ha'kurin zama a d'akin mijina, ko don saboda 'yar tsohuwar ta kasance cikin walwala da farin ciki. A can 'kasa kuwa Hajiya na zama Shukura ta fara 'kananun maganganu na rashin mutunci, domin kishi 'karara take nunawa akan matar mahaifin nata, ita dai bu'katar ta mahaifiyarta ta dawo gidan. Hajiya ta katse ta da fad'in" Idan zaki kwantar da hankalinki akan wannan al'amari to, domin da mahaifinki zai dawo da Fatima gidansa da tuntuni ya dawo da ita, sannan kina fadin na tilasta shi, akan me zanyi masa dole? shine mai auran kuma yace ba zai zauna da ita ba saboda wasu dalilai, to akan me zan matsanta masa, don Allah Shukura ki samu nutsuwa, kada ki tayar mana da hankali a gida da fitina mara dalili. Hawaye ta share ta ce" Hajiya ni kawai yarinyar ce ba tayi min ba, ai ba tsaran auransa ba ce, don wulakanci shine zai auri 'yar 'karamar yarinya bayan duk ga mata nan a gari." Cike da mamaki! ta ce" Mahaifin naki shine wulakantacce?" Hanci ta sha'ka ta zumbura baki ta ce" Ai dama ba kya 'kaunar Mommyna kamar ba ke ki ka haifi Ubanta, 'kiri-'kiri ki ke nuna fifiko saboda kawai Daddyna yana da kud'i." Hajiya ta ri'ke baki da d'umbun mamaki! a tare da ita ta ce" Rashin kunya za kiyi min Shukura yanzu ni ki ke fad'awa wannan magana?" Ta bud'e baki za tayi magana ya shigo falon, duk sai su ka yi shiru, amma fuskokinsu da alamun 'bacin rai! don ita Shukuran ma kuka take. Cike da kulawa ya kalle ta da fad'in."Menene?" yana son yarinyar sosai! saboda ita kad'ai gare shi, halayenta ne baya so shiyasa ba kasafai yake yarda ta je gurin gurin uwarta ba. Sake rurucewa! tayi da kuka tana takure jikinta a cikin kujera! Ya zauna yana kallon Hajiya domin tayi masa 'karin bayani. Tsaki! ta ja ta ce" Wannan yarinyar sam bata da hali wallahi. kuma yanzu na fahimci abinda ka ke gudu tsakaninta da mahaifiyarta, domin dai wasu halaye take masu kama da na uwarta. Ya ce." Menene ya faru?" Nan ta kwashe komai ta fad'a masa. Ya sha kunu sosai! yana kallonta da kakkausar murya ya ce." Wallahi ki kiyaye ni Shukura ki bar ganin ina biye miki ko ina nuna miki 'kauna, akan Shahida za mu 'bata sosai ranki zai 'baci mutuk'ar baki daidaita hankalinki ba, ina ruwanki da ita? muddin kin d'auke ni uba to itama uwarki ce, saboda haka kada na ji ko na gani kinyi mata rashin kunya, duk ranar da hakan ta faru sai na 'bata miki rai." Cikin kuka ta ce" Daddy kayi hakuri don Allah, amma ina neman alfarma a gurinka. Ya kalle ta babu fara'a a fuskarsa, ta ce" Don Allah ka dawo da Momnyna wallahi tayi nadama, kuma 'yar uwarka ce." Shiru na minti biyu kafin ya ce." Zanyi shawara akai." Daga haka bai sake magana ba ya tashi ya hau sama. Itama Hajiya tashi tayi ta shige dakinta cike da takaicin abinda yarinyar tayi mata. Ganin saura ita kadai a falon yasa ta dauki wayarta "Mommy kin san wani abu?" Daga d'aya 'bangaran Hajiya Fatima ta ce" Sai kin fad'a min." "Na roki alfarma a gurin Daddy zai mayar dake d'akin ki." Cike da murna ta fadi maganar. Hajiya Fatima kamar ta zuba ruwa a 'kasa ta sha don farin ciki, ta ce"Shukura da gaske ki ke ?" Tafad'a cike da zumud'i. "Wallahi kuwa Mommy amma ya ce"Zai duba ya ga ni, nan da kwana biyu zan sake yi masa maganar." Ta ce" To shikkenan zan zo a shirye in sha Allahu. amma ki cigaba da matsanta masa akan maganar, kuma kada ki bar matarsa tasha iska a gidan, 'yar iska nakasashshiya." "Mommy cewa yayi fa akanta zai 'bata min rai! wai dole sai na girmama ta! kamar yanda zan girmama shi." Tsaki! ta ja ta ce" A gaban idonsa ki bata girma amma a bayan idonsa ki ci ubanta, idan na shigo gidan, da k'afafunta zata gudu. "To shikkenan Mommy yaushe zaki dawo?" "Cikin satin da za mu shiga in sha Allahu." "Mommy kada ki manta don Allah ina son abaya masu kyau da takalma." Ta ce" Su nayi order baki da matsala daughter sai na dawo in sha Allah." Sallama su kayi da juna, kafin ta shiga d'akinta cikin farin ciki da an Nashua's mamanta zata dawo kusa da ita. Zaune a gefen gado ya same ni ina ta nazari da tunanin abinda zai biyo baya. Koda ya shigo d'akin, can wata kusurawa ya nufa ya cire wani babban zani akwatina ne a jere guda bakwai sababbi kar kuma daka gani masu tsada ne. Ya juyo yana kallo na kafin ya ce." Ga kayan lefanki nan na jima da had'a miki, duk yawanci a dinke suke, akwai komai na bu'kata a ciki kama daga kayan kwaliyya rigar nono kayan bacci wando siket da dai sauran abubuwan b'ukata na mata, daga yau kada ki sake amfani da kayan dake wancan sashen, tunda dai wasan kwaikwayon ya 'kare." Murmushi nayi wanda yayi kama dana dole na kaucewa maganarsa ta hanyar fad'in"Ga abinci Hajiya ta kawo" na nu masa kwadon dake cike da kwanukan abinci. Yana 'ko'karin sauke akwati nan 'kasa ya ce." Ni kam a 'koshe nake kin manta ban jima da jin abinci ba, ko da zan ci wani sai an jima, amma dai ke ina bu'katar ki ci abinci sosai! Yana maganar ne yanda zan ji sosai! don ya riga ya saba da d'aga sauti idan zai min magana. Na ce"Nima na 'koshi." Girgiza kansa yayi a lokacin da yake 'ko'karin zama a kusa da ni hannunsa ri'ke da wata figalalliyar riga, da kuma sababbin pant da brez. A cinya ta ya ajiye min pant da brez din kafin ya fara warware! rigar yana fad'in" Yau wannan rigar za kiyi min ado da ita." Gabana ya yanke ya fad'i! kallonsa

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});