Chapter 28
Chapter 28
yanzu basa tare, amma haushinsu nake ji sosai! Shiru d'akin yayi na 'yan mintina, kafin ya kalle da cewa" Ki tashi ki ci abinci ga farfesu Hajiya tayi miki." Yana 'kokarin bud'e fulas din yake magana. Motsi ban yi ba ballanatana yasa ran zan sauko na ci wani abu. Ya gaji da maganarsa ya had'a shayi da kansa ya karya ya sha, kafin ya zuba farfesun ya dangwala da biredi. Cikin bacci da ya fara fizgata na ji shi yana laluben hannuna dake cikin bargo, ya saka min wasu takardu. "Tashi zaune za muyi magana." Yafad'a babu wasa a muryarsa. Sai da na mula tukkuna na tashi zaune. har yanzu na kasa sakin fuskata, duk na damu jin maganar dawo da uwar gidansa. Cikin nazari ya ce " Duk kin sauya fuska saboda wani dalili mara tushe! kada fa ki damu, na riga na shafe babin Fatima a rayuwata, domin da zan dawo da ita to da tun kafin na aure ki na dawo da ita, don haka ki samu nutsuwa. Daurewa nayi na ce'' Waye ya fad'a maka na damu? kaina ne fa yake min ciwo ba wani abu ba. Murmushi kawai yayi tare da fad'in ''Ai na gane ana 'kaunata yanzu tunda na ga kishi 'karara a cikin idonki." Shashantar da maganar nayi ta hanyar fad'in" Wannan takardun fa?" Ya ce" Naki ne." Na tsira masa ido domin yayi min 'karin bayani. Ya fuskance ni sosai kafin ya ce." Kasancewar na samu abu mai muhimmanci a gurinki yasa nayi miki wannan kyautar. takardu biyu ne a hannunki, akwai na gidan mai da kuma na rumfar kasuwa dake kwari, yanzu haka ana cigaba da hada-hada na kasuwanci a kowane sassa, abinda aka samu duk ya zama mallakinki, ina miki fatan alheri. Na kalle shi da mamaki mai yawa a tare dani, na ce"Saboda kawai ka samu budurci a tare dani zaka bani gidan mai sukutum! nayi me da shi to?" Sai ya 'bata fuska da fad'in" Ba wai ba ne a gurina, kuma budurcinki ya cancanta da komai. domin zan iya tattare duk abinda na mallaka a duniya na baki saboda farin cikin da ki ka sanya ni a ciki, saboda haka ki dauki al'amarin da muhimanci, ki kuma sa a ranki cewa; kin bani abu mai daraja wanda bani da abinda zan biya ki dashi. Gabad'aya jikina yayi sanyi da kalamsa. kawai na ri'ke takardun tare da zuba masa ido, ni dai ban ga abinda zanyi da gidan mai ba, ina lefin rumfar kasuwar. Kira ne ya shigo wayarsa ya d'auka! nan na ji yana fad'in" In sha Allahu gobe zan shigo kano d'in sai a san yanda za a yi. Na ce" Don Allah mu tafi tare." Girgiza kansa yayi da fad'in" Za ki je amma ba yanzu ba sai kinyi nauyi. Sai na rasa inda maganarsa ta nufa, sai nayi nauyi kamar yaya? Ya katse tunani na ta hanyar fad'in." Kina bu'katar zama a wannan sashen ko za ki koma naki domin na riga na gama shirya miki komai." Girgiza kai nayi da cewa" A'a gwara nan d'in." Ajiyar zuciya ya sauke da tare da cewa "Shikkenan abinda ki ka za'ba shine za'bi na."
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28