Chapter 2
Chapter 2
d'aya! wani irin taushi tafin hannunsa. Jin saukar hannunsa kan mazaunata yana kokarin rungumeta, ta fizge jikinta ta matse gefe kwalla duk ta cika kwarmin idonta. Wannan mutumin shu'umi ne! Gabad'aya ta sanya hannu ta 'kan'kame kirjinta. domin ganin yanda ya tsira musu ido. Murmushi yayi gabad'aya kwayar idonsa ta sauya. Bud'e muryarsa yayi sosai kafin ya ce." Kwanaki ina ki ka shirya zuwa ne? ki ka yi basaja cikin mutane, ko kin dauka ba zan gane ki ba. Kai tsaye ta ce." Zan gujewa sharrin ka ne." "Da gaske?" yafad'a yana lumshe mata tsummamun idanuwansa da suka 'kankace! Kai ta daga da fadin." Kwarai kuwa domin zama a wannan gidan had'ari ne ga rayuwata. Le'bansa ya d'an lasa kafin yayi wani munafikin murmushi ya ce." Ai kin shigo gidan nan kenan har abadah." Wani kallo tayi masa mai kama da harara! sosai kallon ya tafi dashi, jikinsa ya 'kara rikicewa. Ya nemi kujera ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. "Sonki nake yi." ta ji sautin maganarsa yana fad'in wannan kalma. Ta dinga kallonsa a lokacin da yake ta nanata maganar...."Sonki ne keyi ina sha'awar ki mallaka min kanki" Wani tashin hankali ta shiga a lokacin ta kalle shi wanda har yanzu ita yake kallo irin kallon da ta tsana! ta ce." Har abada na haramta a gare ka domin komai kulafucin ka na fi karfinka." Murmushi yayi ya d'an sake lasar le'bansa a karo na biyu! gabad'aya sha'awa ta gama kashe masa, Ya ce" Ki daina cika min baki domin idan kin shiga hannuna ba zan sassauta miki kawai ina so mu yi komai cikin nutsuwa da walwala shiyasa nake rarrashinki." Ta ce" Ba zaka ta'ba samun biyan bukatarka." Sai ya tashi ya nufi gurin da take. tayi sakare domin ta d'auka wani abin zai mata. kawai sai ta ga ya zube a gabanta gwiwarsa a 'kasa ya 'kask'antar da kansa tare da rauntar da murya cikin sigar lallashi da yaudara ya ce.... [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 63&64 "So nake ki amince da b'ukata ta, ina nufin ki mallaka min kan ki koda na rana d'aya ne, wallahi ni kuma nayi miki alkawarin faranta miki rai, tun daga kan miliyan d'aya zuwa miliyan d'ari zan mallaka miki mutukar zaki bani kanki, sannan zan saya miki mota mai tsada, na kuma gidanawa mahaifinki gida, ke nayi miki alk'awarin duk danganinki za su fita daga cikin kangi na talauci muddun kin amince min na dand'ana zumar ki, wallahi zan iya sadaukar miki da duk abinda na mallaka." Yana maganar ne a lokacin da yake ka'sk'antar da kansa amma ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji sa'kon nasa! Ta dinga girgiza kanta tana auziyya a cikin ranta, wasu hawaye masu d'umi! ne suka shiga sauka a kumatunta, dama duk wani kwane-kwane da yake ta riga ta fahimci abinda yake bukata kenan da ita, ko ga yanayin kallon da yake mata a duk lokacin da suka had'u! ai talauci ba hauka bane, tana ganin ko me zai mallaka mata ba zata amince da bukatarsa ba. Ganin tayi shuru kawai tana kallonsa da hawaye a fuskarta, sai ya tashi jikinsa na rawa! ya 'kan'kameta yana shashshafa bayanta sai kisses yake mata har ya samu nasarar cire mata dankwalin kanta yana hargitsa mata gashi wanda ta wanke ta d'aure shi da ribbon. Wani 'karfi ne ya zo mata a lokacin, ta ture shi tare da kurma uban ihu! ta sa hannuwanta duk biyun aka tana kiran sunan Allah! kuka take tukuru! dan ganin yanda yanayin sa ya sauya gabad'aya! ya rikirkice! yana nema ya kwantar da ita a saman kujera tana duddukansa ta ko'ina! kuma ba ta fasa kurma ihu ba tana kiran Allah ya kawo mata dauki. K'arfi ya sa mata sosai ya ri'ke ta da kyau! don ganin ihun da take yana nema ya tarwatsa 'kwanyarsa! ya matse ta a jikin bango! sannan ya had'e bakinsa da nata! gam! ya ri'ke ya hana ta ihu! a lokacin da bakinsu ya had'u ji tayi kamar an bubbuga mata 'tabarya a k'afafunta sai kyarma take tana ta so ta k'wace bakinta abin ya fassakara, ya ri'ke harshenta da kyau! so yake kawai ta samu nutsuwa! Sanyi jikinta yayi sai uban hawayen da yake gararanba a saman fuskarta, wanda shima tasa fuskar duk ta ji'ke da ruwan hawaye, ba kuka yake ba amma tsabar tashin hankalin da ya ke ciki a lokacin ya sanya kwayoyin idanuwansa mugun ja! ita da shi suka dinga rawar jiki ita dai na tsananin tashin hankali da fargaba ne, shi kuwa na tsantsar sha'awa ne da bukatuwa zuwa wani abu da yayi shekara da shekaru bai samu ba. Sai da ya tabbatar ta nutsu jikinta ya mutu sannan ya cire bakinsa daga nata, ya dan ja baya tare da zuba hannuwansa cikin aljihu yana yi mata wani irin kallo na tausayi da mugun so! Ta zube 'kasan 'kafafunsa tare da ri'ke daya ta ce" Don darajar Allah da Annabi ka da ka aikata fasadi dani, kada ka janyo mana fushin ubangiji! zina babu kyau! mussaman ga masu aure hukunci mai tsanani Ubangiji ya tanadar ga masu aikata wannan lamari, wallahi tunda nake ban ta'ba zina ba, kuma bana fata na fara da kai, bana bukatar komai daga gare ka, ni na yarda na cigaba da zama matalauciya mai rangwamin gata, shin wai ma me za kayi da ni? duk ga mata nan a gari kyawawa masu aji da kyawun jiki, mai za kayi da iri na nakassashiya mara gata, kana da kudi ka je ka nemi irinka amma ni don girman Allah ka fita daga cikin rayuwata. Cikin tsantsar tashin hankali da kuka matsananci take wannan maganganu. Amma ko a fuska bai nuna sadudarsa ba ya cire k'afarsa tare da komawa kan kujera ya zauna yana kallonta babu alamun sassauci a tare da shi ya ce.'' Wannan shine karo na farko dana bukaci wani abu a gurin wata 'ya mace ta yi min gardama! kamar ni, na nemi da ki bani kan ki, amma ki cika min kunne da ihu! har kina kai min duka da cizo da yakushi! wai shin meye a ciki ne? na farko dai wannan lamari idan ya faru tsakanina dake ne, babu wanda ya ji ko ya gani, amma duk kin tashi hankalinki a banza a wofi wanda ni kuma duk abinda za kiyi ba zan janye kudiri na ba, dole sai na kwanta dake domin zuciya da gangar jikina suna bukatar hakan, saboda haka zan baki kwana uku ki je kiyi tunani, amma ki zo min da abinda zan gamsu, tunda na fada miki ni dai ba zan iya hakuri dake ba. cikin jaddada aniyarsa ya kai karshen maganar. Hannu tasa ta goge ruwan hawayen da yake zuba ta ce." Wai kai baka tsoron Allah? ba ka tsoron ranar da zaka tsaya a gabansa, ranar tonan asiri, ranar da kudi da mulki ba za suyi tasiri ba, a ranar ne Allah zai nuna wa jama'a waye kai cikinsu kuwa harda mutanan da suke ganin girma da mutuncinka, a gidan duniya, kowa yana ganin girmanka, dalilin taimako da sadaukarwar da kake da dukiyarka, a zahiri kai mutumin kirki ne, amma kuma wani 'bangaran ka samu nakasu! saboda miyagun halayen da kake aikatawa irin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28