Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ri'ke jikinsa na rawa ya ce" Ki daina tunani a kaina matata kuma kada ki dauki abinda nayi miki da wata manufa! nayi hakan ne domin na gwada ki kuma alhamdulillhi, kin yi d'ari bisa d'ari! ni yanzu na ga matar aure." Ido kawai na zuba masa ina auna maganganunsa, yayin da shi kuma ya zage! sai kalaman soyayya yake zuba min tare da rarrashi da daukar alkawari. Na ce" Ni dai gaskiya zan fad'a maka abinda yake zuciyata shine, ba zan iya rayuwar aure da kai ba" Cikin rashin jin dadin furucina ya ce." Saboda me ki ke wannan maganar menene dani da ba zaki amince mu raya sunnar ma'aiki ba" Kasa magana nayi saboda yanda ya bani tausayi, nasan har cikin zuciyata nake tausaya masa, amma kwata-kwata bana jin sonsa a cikin raina. Cikin rashin jin dadi, ya tashi ya fita, sai na bishi da kallo, ina tunanin abubuwa da yawa a cikin raina. Minti ashirin da fitarsa, ya dawo amma tare da Hajiya suke, gabana ya fad'i, dama cikin tunanin yanda zata kar'bi al'amarin nake, duba da cewa; yayi abun a rufe bai bayyana gaskiya ba, fuskarta a sake ta nemi kujera ta zauna tana kallona. Saukowa 'kasa nayi na gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa gaisuwata sai kallona take wanda ya sanya na tsargu, na shiga wasa da yatsun hannuna tare da k'ok'arin mayar da hawayen dake kokarin zuba. Sai da ta bud'e muryarta sosai sannan ta ce" To ke Shahida idan ban da abunki menene abin damuwa a cikin wannan al'amarin, ai komai na Allahu ne , ni wallahi nayi murna sosai da jin wannan abu, kuma nayi muku fatan alheri, dama buri na kenan yayi aure, to Alhamdulillhi, bukatata ta biya, saboda haka ki kwantar da hankalinki, duk abinda ya same ki, na alheri to halinki ne ya ja miki, domin mijinki yayi min bayanin dukkanin abinda ya faru, don haka ki saki jikinki damu, sannan kuma kiyi hakuri ki 'karbi wannan aure hannu biyu, domin hakan alheri ne. Ajiyar zuciya na sauke na ce" Hajiya al'amarin ne na rasa ina zan ajiye shi a raina, amma cikin zuciyata sai nake tunanin kamar ni ba tsaran auransa bace, bayan haka kuma ina tunanin wani abu." Shi ya rigata magana da fadin" Wannan ba hujja bace Shahida, na san abinda kike tunani, amma bari kiji wani abu, ko kin fi haka rauni ko nakasu! wallahi zan aureki, domin ni bana bukatar kyau! ko wata d'aukaka! tarbiya nake buk'ata da amana, kuma na samu da yardar Allah, saboda haka kisa a ranki cewa; ni naki ne har abada kuma uban 'ya'yanki." Kallonshi nayi, tare da girgiza kaina, domin ni abinda nake dubawa daban da tunaninsa. Ta ce" Nima hankalina ya kwanta da yarinyar nan Alhaji Habu, saboda haka kayi k'ok'arin rarrashinta domin ta samu nutsuwa." Ya ce." Insha Allahu Hajiya." Ta kalleni tare da cewa" Shahida ni zan tafi amma don Allah kada ki bijirewa auranan, kiyi hakuri ki zauna tare damu kinji ko" Tausayi ta bani sosai! na ce" To shikkenan Hajiya nima na gode sosai" To tunda ya fita bai sake shigowa ba sai bayan isha'i, ya shigo ya same ni kan dadduma na idar da sallah, ina addu'a. Zama yayi kusa dani tare da d'aga hannunsa sama yana fadin" Allah ka mallaka min zuciyar matata ka bamu zuria masu albarka. Ina jinsa yana ta addu'oi, nima ina yin nawa, na shafa a fuskata, shima shima ya shafa, ya kalle ni da murmushi na mussaman a fuskarsa, babu yabo babu fallasa na gaishe shi, ya amsa a lokacin da yake 'kok'arin rike hannuna. da sauri na janye, na tashi na bar shi a gurin. Beyi zuciya ba, ya sake zuwa kusa dani ya zauna tare da rungumo ni jikinsa, kawai sai na fashe da kuka! ina ture shi! " Ka matsa daga kusa dani" Ya ce" Me yasa zan matsa bayan ke din halalina ce'' "Ni ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba, domin baka cikin tsari na" Na fad'a tare da cire hannunsa da d'ora a saman cinyata. Ido ya zuba min da alamun damuwa a tare dashi ya ce" Menene abinda ba kya so a tare dani?" Shuru nayi masa, ya ce" Kada fa ki butulcewa Allah Shahida." Ajiyar zuciya na sauke da fad'in" Nafiso na auri daidai da ni, mai rauni da rangwamin gata. Ya ce"Sai kuma Allah ya baki Saddiku a matsayin miji shin ya za kiyi kenan? da yanayi na 'bacin rai yayi maganar. Tashi nayi na shiga d'aki na kwanta tare da tsirawa rufin d'akin ido! hawaye masu zafi suke zuba, shin ya zanyi ne? na san Ubangiji ya gama yi min komai da ya mallaka min babban mutumin mai daraja irin wannan, amma a jikina nake jin kamar akwai abinda zai faru mara dad'i dangane da auransa. Shigowarsa d'akin yasa nayi saurin goge hawayena, ya ce" Kina yi min asarar hawayenki wanda ya fi gold tsada a gurina, bari kiji wallahi duk abinda za kiyi ba zan rabu dake ba, domin ni naga matar aure. Kallonsa nayi a lokacin da yake maganar, nan naga tsagwaron sona a cikin k'wayoyin idanuwansa. Ya ce" Yini guda duk kin rasa sukuni! kinyi rama ta ba gaira ba dalili, kowane bawa fa, da kaddararsa, ke taki k'addarar auran dattijo wato Saddiku, kuma kin shigo hannunsa kenan, domin ba zan iya rayuwa babu ke ba. Na ce" Aikuwa ba zaka samu nutsuwar da kake bukata ba, tunda dai ni bana 'kaunarka, tausayinka kawai nake ji, kuma ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba. Murmushi yayi kafin ya ce" To tunda akwai tausayi ni na tabbata da akwai k'auna, amma mu je zuwa dai tunda kin fad'i haka. Juya masa baya nayi tare da rintse idona! sai kawai na jishi a kusa dani, yana k'okarin rungume ni! na ture shi da karfi! na tashi zaune tare da matsawa 'kuryar gado! Kallo na yayi na minti biyu kafin ya ce" Kin san dai hukuncin matar da take 'kauracewa mijinta ko?" Gabana ya fad'i! da jin maganarsa. Cikin rawar murya na ce" To me kake nufi?" Murmushi yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa ya ce." Bana nufin komai sai alheri, ko zan kar'bi hakkina ba yanzu ba sai zuciyarki ta aminta dani, amma yanzu ina so ki bani hankali domin cigaba da warware miki abinda ya faru da rayuwata wanda baki sani ba, ina so na baki labarin d'aukakata da kuma cigaban labarin zaman aure na da matata ta biyu. Jin haka yasa na kalle shi da fad'in" Ya sunanta?" "Zinaru" yafad'a yana kallon fuskata. baki na ta'be da fad'in" Yunwa nake ji yanzu" sauka yayi daga gadon, ya kama hanyar fita ba tare da yace min komai ba, nima na bishi da kallo tare da nazari da tunanin abubuwa da yawa a tare da ni, da shi. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 80&81 Kafin nayi magana sai ga ta fito, kamar wacce take la'be, ta tsaya 'kerere! a kan mu, ta nuna Hajiya da yatsa tare da fad'in'' To magulmaciya tsohuwa mai zuwa lahira da 'ko'kon dambu, duk na ji abinda ki ke fad'a masa sharri za kiyi min Allah ya isa tsakani na dake." tana

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});