Chapter 24
Chapter 24
kalle ni ba. Na sauke ajiyar zuciya da fad'in" Na ga ka dafa kai ne, shine nake tunanin ko ciwon kai ne ya matsanta maka. Ya cire hannuwan nasa tare da zuba min ido. Kasa kallonsa nayi sakamakon ganin yanda 'kwayoyin idanuwansa suka sauya jajawur! yanayin kallon da yake min ne yasa jikina mutuwa! gabana kuma na cigaba da fad'uwa! Hannu na ya ri'ke tare da fad'in" Ina da damuwa mai tsanani." Nayi shiru ina kallonsa. Ya cigaba da cewa; Kasancewar ki a kusa da ni ya janyo min sha'awa mai tsanani, gashi idan ina cikin wannan halin bana iya sarrafa kaina." Na kalle shi a lokacin da yake bin ilahirin jikina da kallon kurulla, gabad'aya yanayinsa ya sauya yayi sanyi sosai, hannunsa dake ri'ke da nawa sai karkarwa yake. "Yanzu me ka ke bu'kata?" Na tambaye shi duk da na harbo jirgin nasa. "Ki mallaka min kan ki a wannan lokacin." Ya fad'a tare da kusantar jiki na. Kai na girgiza. alamar ba zan iya ba. Ya ce."Saboda me?" Shiru nayi ban bashi amsa ba saboda na san da cewa bani da wata hujja. Rungume ni yayi tsam! a jikinsa! yana makyarkyata! kuka nasa ina ture shi tare da fad'in" Ka rabu da ni don Allah. Cikin kunnuwana na ji yana fad'in" Ki taimaka min na rage damuwa ta shekara da shekaru matata ba zan cutar dake ba." "Ni dai A'a ban shirya faruwar hakan ba.'' Cikin shagwab'a da sangarta nayi maganar ina kokarin raba jikina da na sa. Yanda na fahimta hakan da nake kamar 'kara masa 'karfin gwiwa nayi domin rikicewa yayi yasa 'karfi sosai ya kwantar dani kan gadon yayi min rufa! Sosai nayi mamakin abubuwan da yake min tamkar ba mara lafiya ba, hannayensa sai yawo suke a sassan jikinta. Gabad'aya gwiwa ta tayi sanyi sakamakon abubuwan da yake min, 'kamshin jikinsa ma ya taka muhimiyyar rawa gurin hana ni 'kwatar kaina. Kamar a mafarki mu ka ji an bud'e 'kofar d'akin an shigo da saurin gaske ya sauka daga kaina tare da juyawa domin ganin waye ya shigo. gefen rigarta kawai mu ka yi katarin gani domin da saurin ta bar gurin ba tare da ta rufe 'kofar d'akin ba. Takaice yasa na fashe da kuka da fad'in" Ka gani ko?" Ba tare da ya ce komai ba ya juyo da nufin sake kwantar da ni, sai na matsa gefe da sauri ina gyara wuyan rigata, sauka nayi daga gadon, k'afafuna sai rawa suke, na ce" Yanzu kayi wannan abun ya za a yi su yarda baka da lafiya. Murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga band'aki ba tare da ya ce min komai ba. Na zauna kan kujera gabana sai bugawa yake, komai yana bu'katar sirri ya zama dole ya takawa yarinyar nan burki ta daina bankad'o mana d'aki tana shigowa ba tare da neman izini ba. Ko da ya fito daga toilet din ban iya kallonsa ba, saboda tawol ne d'aure a jikinsa, cikin zuciyata na ce" Dole ciwo yayi ta damunsa ko da yaushe cikin watsawa jiki ruwa. Band'akin na shiga na tsafta ce jikina, domin ni kaina ban yarda da kaina ba, abinda ya faru a tsakaninmu yasa wandon dake jikina ya 'baci! wanke wa nayi na shanya a band'akin na fito na same shi a zaune kasan kafet yana duba wayarsa. Har nayi nufin zama kan kujera, na ji maganarsa. "Kada ki zauna zuba min abinci nan." Ya fad'a ba tare da ya kalle ni ba. Na zuba masa daidai gwargwado na ajiye a gabansa, niyyar barin gurin nayi, ya ce" Zauna ina so muyi magana. Zama nayi kaina a 'kasa Ya ajiye wayar hannunsa a gefe, kafin ya kalle ni, ya ce." Za mu ci abincin tare ko?" Girgiza kai nayi. Ya ce." me ki ka ci to?" shiru nayi masa tare da d'auke kaina. Ya ce." Na fara gajiya fa da wannan abubuwan da ki ke min zan kai 'karar ki gurin mahaifinki" Kallonsa nayi da mamakin maganarsa, ya ce." 'Kwarai kuwa! ki kalle ni da kyau! kin san a shekaru na haife ki ko? amma na ajiye girmana ina rarrashinki duk don mu zauna lafiya kina min wasu abubuwa saboda kin fahimci cewa Allah ya jarrabe ni da sonki shin ko ba haka bane?" Ban ce masa komai ba. Ya cigaba da cewa" Ki kula da ni a matsayin mijinki, kiyi kokarin sauke hakkina dake kanki kada ki zalince ni, sannan ina so ki d'auki wannan al'amari a matsayin 'kaddararki, kada ki butulcewa Ubangiji mana, da can kin yi soyayya da mahaukaci mara galihu! sai kuma Allah ya sauya tunaninki ki ka tsinci kanki a matsayin matar babban mutum wanda ya shallake tunaninki, shin me ya kamata ki yi?'' Jin nayi shiru ban ce komai ba ya cigaba da cewa" Allah subahanahu wata'alah za ki godewa a bi sa ni'imar da yayi miki, duk wad'an nan abubuwan da ki ke min kamar 'kara min 'karfin gwiwa ki ke domin ni ba zan iya rabuwa dake ba har abada don kin zama jinin jikina. Ya 'kare maganar tare da tsira min ido. Na ce" Ni yanda zanyi rayuwar aure da kai ne ban sani ba." Sihirtaccen murmushi yayi kafin ya ce." Saboda nayi miki tsufa ko?" Shiru nayi masa. Sai ya cigaba da cewa" Wace rayuwa ki ka shirya yi da masoyinki Baban-baba?" Kallonsa nayi sai na gana yana murmushi wanda ya 'kara masa kyau! Da sauri na ce"Rayuwa mai sau'ki da sau'ka'awa." Dariya yasa sosai yana mamakin yarinyar. 'kuruciya ce kawai take damunta, a ganinsa ai rayuwar da za ta yi dashi a yanzu sai ta fi armashi da wacce za tayi dashi yana fa'kiri (talaka) gabad'aya ya gaza fahimtar inda ta nufa, wata irin bahaguwa ce, ko da yake yana yawan ji daga bakin mutane suna fad'in (Kurame) ba su da saurin yarda domin duk abinka sai sun zarge ka a wasu lukatan( A yi min afuwa masu wannan laluran ban yi dan na ci fuska ba) Ya kalle ta da fad'in "Me yasa lokaci guda ki ka aminta da ni a lokacin da nake mahaukaci na 'kar'kashin mota" "Tausayinka na ke ji har cikin raina ina jin takaicin irin rayuwar da ka ke, kuma ina shiga 'bacin rai a duk lokacin da na ji ana kiran ka da mahaukaci! har kuka nake wani sa'in." Ya sake jin wani irin k'aunarta a cikin ransa. "Ni ma a lokacin ji nake duk duniya bani da mai 'kauna ta kamar ke, domin baki 'kyama ce ni ba, kin bani abinci kin bani ruwa, kin share min makwancina, wannan dalilin yasa na tsaya kai da fata naga na mallake ki domin samun mace irinki a yanzu babban aiki ne." 'Dakin yayi shiru na minti biyu, kafin ya cigaba da cewa; ki sa a ranki cewa abinda mahaukacin nan zai yi miki na kulawa da soyayya, to ni zan yi miki wanda ya fi shi, buri na kawai ki amince da ni cewar ba zan cuce ki ba, kuma nayi miki al'kawarin ba zan gaza miki ta kowane fanni ba. Kalamansa su suka sanyyayar min da jiki cikin zuciyata na ji ina sha'awar zaman aure da shi, sa'banin tunanin da na keyi , ganin kamar ya fi 'karfina, tabbas
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28