Chapter 8
Chapter 8
ita da mahaifinta wato Baba Auta fuskarsa a murtuke! ina mika masa hannu domin mu gaisa amma bai ko kalle ni ba. Na samu gefe na tsuguna ina sauraran abinda zai biyo baya. Ta fashe! da kuka! fuskarta kaca-kaca da hawaye! take fadin" Saddiku cin mutuncin da za kayi mana kenan? saboda 'kasa ta rufe idon ubanka, shiyasa kake nuna min iyakata, babu damar na yanke hukunci a gidan nan, sai kasa kafa ka tsallake, amma kara wannan, idan mahaifiyarka ta ajiye baka iya tsallakewa saboda kana gudin 'bacin ranta, amma ni dana haifi ubanka ka raina ni, Sadiya ta shirya maka karya da gaskiya ka hau kai ka zauna, shin yaushe Fatima ta zagi uwarka da har zaka sake ta, akan wannan dalilin da bashi da tushe ballanatana maka ma." Zanyi magana ya daga min hannu da fad'in" Dakata" sai nayi shuru ina kallonsa. yayi 'kwafa! yana girgiza kansa da fadin" Aure duka wata hud'u da 'yan kwanaki har ka soma wulakanta min yarinyata! menene abin jin haushi anan, saboda kawai ta nemi hakkinta na aure shine zaka sake ta, idan baka da lafiya ba sai ka fada mana ba, a nema maka magani." Murmushin takaici nayi na ce" Lafiyata lau, kawai ban yarda da nayi kwanan aure da ita kai tsaye ba, sai mun je asibiti likita ya aunta, domin gabad'ayanku kun san abinda yake faruwa. Sai ya fusata! ya rufe ni da fad'a zagi ta uwa ta uba! duk ina kallonsa ina kuma 'kara jin haushin 'yarsa a cikin zuciyata, an aura min ita ba don ina sonta ba, amma ana bina da cin mutunci. Ta sassauta murya da fad'in" Saddiku kada ka bani kunya mana kayi wa Allah da annabi ka dau aniya a zuciyarka ka mayar da matarka dakinta, kada ka manta fa 'yar uwarka ce, duk abubuwan da suka faru a baya ka daina tunawa, ka fuskanci abinda abinda yake gabanka. Ganin ta sassauta yasa na ce"To shikkenan zanyi shawara akan al'amarin... ya katse ni ta hanyar fadin." Kada ma Allah yasa ka mayar da ita mana, ko ka d'auka kai kad'ai ne namiji a duniya shashasha mara mutunci kawai" Na ce" Baba auta idan an ciza a hura! kai babba ne kuma kanin mahaifina, ka dinga sanin irin maganar da zaka fada a kaina, domin ina tsoron watarana ka fusatani na mayar maka da martani" Da kumfar baki ya ce" Ka mayar mana, ai babu lefi tunda kana ganin ka isa" Ta ce" Ya isa haka Auta abi komai a sannu a hankali, domin shima duk abinda yake yana da hujja akai saboda haka rarrashinsa za ayi" Shuru yayi yana cin magani. ita kuma Fatiman sai ta hau kuka! tana fadin" Sai Allah ya saka mata a kan zargin da ake mata, tunda ita dai bata ta'ba sanin wani d'a namiji ba. Ni dai tashi nayi na bar su a gurin suna mayar da magana, na shiga dakin Mamana na same su a zaune jigum! Inna Samira na kwantar mata da hankali, itama zuwanta gidan kenan, sai ta riski irin cin zarafin da akewa 'yar uwarta, wannan dalilin yasa ta shiga ciki fad'an, domin kare mutuncin yar uwarta. Ta kalle ni kafin ta ce" 'Dan gaske, wannan ya zama na farko kuma ya zama na 'karshe! kada ka kuskura wani sa'bani ya sake had'aka da matarka ka sake ta, ko bayan raina ban amince da hakan ba. Na ce" Umma ba zan iya zama da matar da zata zage ki ba, wallahi duk son da nake mata zan rabu da ita, muddun ba zata martabaki ba, to ballantana wannan da kin san ba sonta nake ba, akan me zata ci mutuncinki ba." Ta ce" Wannan ba hujja bace, ba kuma dalili ne da zai sanya ka saki matarka a kai ba." Na ce" Wallahi Umma kin fi karfin komai a guri na, kamar yanda na fada miki da farko ba zan zauna da matar da zata ci zarafinki ba." Ta ce" A gaban idonka Fatima ta zage ni?" na girgiza kai da fadin" A'a amma Sadiya ta tabbatar min, kuma na san ba za tayi k'arya ba." Ta 'bata rai da fadin" To na gargad'e ka, ka daina yanke hukunci sai ka tabbatar da gaskiyar lamari, domin sakin Fatima na nufin abubuwa da yawa a gidan nan, ciki kuwa har da rashin kwanciyar hankalina, bayan haka kuma ina mai baka umarni yanzu-yanzu ka mayar da matarka, wannan shine farin ciki na" Cikin 'bacin rai ta kai k'arshen maganar . Na ce" Shikkenan Umma na mayar da ita kamar yanda ki ka bukata. Ta ce" Allah yayi maka albarka, ka je ka d'auke ta ku tafi gida, kuma ka tabbatar da cewa ka bata hakkinta na aure, kada ta sake zuwa gidan nan, da wata matsala." Na ce" Insha Allahu komai ya wuce zanyi k'ok'arin bin umarninki. Addua sosai tayi min kafin na tashi daga gurin. To wannan shine abinda ya faru, hakan yasa na kwanta da Fatima kwanciya irin ta sunnah, amma kash! ban same ta cikakkiyar mace ba, wanda dama na san hakan zata iya faruwa. Koda na tsira ta a d'aki domin ta fad'a min iyakacin mazan da take mu'amula dasu, sai ta rushe! da kuka ta dinga ranste-rantse! kan cewa; babu wani namiji da ta kwanta dashi, na ce to ya akayi ban same ta cikakkiya ba, nan ta sheda min abinda suke yi da 'kawayenta (Madigo) hankalina ya tashi sosai! a lokacin, amma ban yi 'kasa a gwiwa ba, nayi mata nasiha mai ratsa jiki, ta ce min insha Allahu ba zata sake ba. Saboda yanayin magungunan matan da take sha yasa kullum sai na neme ta, kuma bana iya ha'kura nayi sau d'aya sai nayi sau biyu zuwa uku sannan nake jin daidai, babu lefi ina jin dadin auratayya da ita sosai, saboda ta gama fahimtar abinda nake so. Rayuwa tana tafiya da dad'i babu, haka muke zaune, amma duk wani hakki nata ina kokarin saukewa, to sai da tabbatar da cewa na saki jikina da ita sannan ta 'bullo da wata manufa, kullum bata yarda da na kwanta da ita sai na bata kud'i! Ni kuma bani da hakuri ko kadan ta wannan 'bangaran, gashi na riga ba saba da ita bana iya kwanciya bacci sai nayi tara da ita, wannan dalilin yasa hankalina yake tashi a duk lokacin da bani da kudin da zan bata, domin sai an kai ruwa rana, take amincewa da b'ukata ta. Cikin wannan halin ta samu ciki, sai ta tsiri nu'kufurci! 'bacin rai iri-iri! idan na tambayeta abinda ke damunta, sai ta ce min babu komai, ashe cikin ne bata so, ni kuma a lokacin farin ciki yasa na kasa hakuri na shedawa Mamana da Hajiyata, sunyi murna sosai! mussaman mahaifiyata da kullum idan naje gidan sai ta bani tsaraba irin ta masu ciki ta ce na kai mata. Yanda na kai mata sak'on haka za ta bari su lalace! suyi funfuna, sai dai a zubar a shara, ga k'azanta domin ta daina komai a gidan, sai dai da safe kafin na fita aiki na gyara. Ranar litinin 'Kawarta Jamila ta zo da sassafe! sam! bana 'kaunar yarinyar, dalili bata da kamun kai ko kad'an, shiyasa bana sakar mata fuska. Ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28