Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

samun kwanciyar hankali, amma zata tsananta da yi min addua insha Allahu ba zan lalace ba. Jin haka yasa na amince ba don raina yaso ba, sai don samun zaman lafiyarmu bakid'aya. amma sam Fatima bata daga cikin tsarin matan da nake so na aura. 'Bangaran wacce ake dambawar don ita, ko da ta samu labarin abinda yake faruwa, sam bata nuna damuwa ba, domin ta jima da sona a cikin zuciyarta, duk da bata furta min ba, amma duk alamomi sun bayyana, idan zamu had'u a ko'ina ne sai tayi min magana irin ta rashin kamun kai, "Wallahi kana burgeni, ina son namiji dogo giant (ingarma) wanda na san ya cika cif, zai gamsar da ni a shimfida, ire-iren wannan maganganun banzan take min a duk sanda za mu had'u, sai nayi mata jan ido sannan! na nuna mata cewa; ni nafi k'arfinta, amma hakan baya hana ta sake zuwar min da maganganun banza makamanta wannan. a duk sanda zamu had'u a wani guri Tunda ake maganar auran ban taka k'afa na je gurin yarinyar ba, komai suke ina kallonsu ne kawai, nayi iyakar abunda zan iya na lefe da sauran abubuwan bukata na aure. Sai ga ta tazo ta same ni a gurin aiki na tare da 'kawarta, kallo daya nayi musu na kawar da kaina domin raina ya 'baci da ganin sutturar dake jikinsu, komai a bayyane. ''Magana na zo nayi da kai" tafada a lokacin da take tsaye a kaina. Na kalleta tare da fadin."Me yake tafe dake?" kai tsaye ta ce."Kudin 'kunshi da kitso nake bukata. Dubu uku na bata amma na gargade ta kan cewa; kada ta kuskura ta zo min gida da gashin doki, domin gwanar 'karin gashi ce da tara farce, ga uban bilicin da take, duk ta lalata fatarta! Ta'be bakinta tayi ta ja hannun 'kawarta suka tafi, tana maganganu kasa-kasa wanda na san dani take. 'Daki da rumfa kawai na samu na kammala, na dan kwaskware! dai-dai gwargwado. amma kicin da band'aki da sauran aiki, dan babu fulasta ballanatana rufi, haka nan na hakura, saboda yanda wahala tayi yawa, ga bikin ya matso komai ya kacame! babu mataimaki sai Allah. To tunda aka d'aura auran, ban wani saki jikina da ita ba, na dai sanya mata ido ne kawai ina nazari a kanta. Duk wani hakkinta da ya rataya a wuya na, ina kokarin ganin na sauke shi, amma kuma ban ta'ba had'a shimfida da ita ba, a falo nake kwanciyata ita kuma a cikin uwar daki, haka nan, za tayi shigar fitar da tsaraici a gabana tayi ta juyawa, amma cikin ikon Allah ba ta iya jan ra'ayi na zuwa gare ta. Sai kawai ta je ta fad'awa Hajiya cewa; bani da lafiya domin tunda akayi auranmu wata hud'u ban ta'ba kwanciya da ita ba. Hajiya ta samu abin yi ta je har d'akin mamana ta rufe ta da fad'a, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cin mutumci iri-iri abin mamaki! Fatima har tana sanya baki, anan ne Sadiya ta gaza hakuri ta fara mayar da martani, Hajiya ta gaura mata mari tana fadin" Wato za ta goyi da bayan uwarta kenan! to shikkenan zata sanya kafar wando daya dasu gabad'aya! Sai da nazo gidan Sadiya ke sheda min abinda ya faru, sosai raina ya 'baci! idan Hajiya ta ci zarafin mamana na rabu da ita to babu shakka Fatima ba zata wanye lafiya ba, domin bani da hakuri a kan mahaifiyata da nake jinta a cikin ko'kon raina! Sosai ta ga 'bacin raina akan abinda tayi, na ce kuma lallai in tana bukatar zama dani to ta je ta bata hakuri, idan ta'ki wallahi sai na sake ta. wannan shine hukuncin dana yanke mata. 'Kwana d'aya biyu shuru ba tabi umarnina ba, a cikin kwana na ukun, na rubuta mata saki daya a takarda na ce lallai kafin na dawo ta fice min daga gida. Yanda na fahimta al'amarin ya bata tsoro sosai, domin ba tayi tunanin zan iya sakinta ba, haka na fita na barta cikin damuwa mai tsanani, wanda ni hakan bai dameni ba, mutukar zata ta'ba martabar mahaifiyata to wallahi na gama zama da ita. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 67&68 ASALIN LABARI. "Ni mutumin jahar katsina ne, a cikin karamar hukumar jibia a ka haife ni, tare da 'yan uwa na biyu wanda suka kasance mata, sai dai Allah yayi wa babbar cikinmu rasuwa a lokacin da ta zo haihuwar fari, tayi mutuwar shahada, ina rokon Allah ya jikan Amina yasa aljanna makomarta, mahaifinmu Malam Sani kafinta ne ma'ana mai sarrafawa katako ta kowace siga, daidai gwargwado yana samun rufin asiri da wannan sana'ar duk ya d'auki d'awainiyarmu, ci da sha suttura da harkokin karatunmu. Ya kasance mutum mai sha'awar karatun boko tun yana yaro, amma Allah bai sa yayi ba, dalili mahaifinsa bashi da wannan ra'ayi a cewarsa duk wani karatu ya bi bayan na addinin musulunci, wannan dalili yasa ya daukeshi ya kai shi can jamhuriyar nijar karatun allo, anan ya sauke al'kur'ani mai girma ya kuma haddace shi, sannan ya dawo gida domin taimakawa mahaifinsa akan sana'arsa ta gado, wacce shima ya gada a gurinsa, yake kuma cin abincinta da ita tare da biyan buk'atar yau da gobe. Sosai ya tsaya min da 'karfinsa dana aljihunsa har sai da ya ga na samu gurbin karatu, a jami'ar bayaro university dake jahar kano, hankalinsa ya kwanta, burinsa kawai nayi karatu sosai wanda zan samu aiki na d'auki nauyin kaina, na kuma yi aure domin rike iyali. A lokacin mahaifiyarsa tayi ta k'orafi da k'ananun maganganu, kan cewa; da Mahaifinsa yana raye wannan d'anyan aikin ba za'ayi ba, domin itama akwai 'karancin rashin fahimta a tare da ita, a ganinta duk wani karatu da za ayi a yanzu mutukar bana al'kurani bane to bashi da amfani, kuma a lokaci fa nayi saukar al'kur'ani, nasan hadisai da sauran littaffan addinin musulunci, kawai dai ita bata son karatun bokon ne, ganin haka yasa mahaifiyata yin shuru da bakinta, domin tana iya magana laifin ya dawo da kanta, sai tayi shuru kawai, amma cikin zuciyarta addua. take min. Tun ina yaro 'karami nake jangwale-jangwale, duk lalacewar abu idan nasa masa hannu sai ya tashi, musamman irinsu tv keken d'inki babur, mota da sauransu, wannan dalilin yasa mahaifina ya bani shawarar karantar Engineering, cikin ikon Allah kuwa cos din beyi min wahala ba, ni nake zuwa na d'aya duk jarrabawar da za muyi bana fad'uwa, sosai nake taimakawa wasu daga cikin abokan karatuna. Na kammala karatuna cikin narasa takarduna sun yi kyau sosai! irin yanda ake bukata, sai dai fafur! aiki ya'ki samuwa, tunda na dawo gida nake yawon neman aikin abin ya fassakara a cikin jahata babu local goment din da ban je neman aiki ba, amma Allah bai sa na samu ba, A lokacin Hajiya ta samu bakin magana, fad'i take dama ai na fad'a! wannan karatun bashi da wani amfani, gashin tsayin shekara hud'u kana fagauniya duk ka lalace! ka yi rama, shi kuma da yake daure maka gindi yayi asarar kudinsa a banza, sai a zo a rungumi sana'ar gado tunda abinda ake nema bai samu ba. Mahaifina dai shuru kawai yayi mata ba wai don bashi da

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});