Chapter 20
Chapter 20
tilas taka auranta duk da na san da cewa; ba ta dace da kamilin mutum irinka ba, wallahi don ka saki Zinaru hakan ba zai yi min ciwo ba." Cike da tausayinsa cikin raina, na ce" Alhaji kayi hakuri don Allah kada kasa damuwa a cikin ranka har wani ciwo ya kama ka, hakika ina tausaya maka wannan jarabawa da Allah ya dora mana, sannan kuma ka daina cewa; ka gaji, ka cigaba da yi mata addu'a babu abinda ya gagari Ubangiji." Fashewa! yayi da kuka a lokacin tsabar bakin ciki ya kasa cewa komai! kawai sai ya kashe wayar ya bar ni cikin tsananin damuwa! Wannan shine abinda ya faru tsakanina da Zinaru, har Alhaji Harazimi ya rasu ban iya furta kalmar saki ga Zinaru ba, har hazar yau, saboda ina ganin idan na aikata hakan, kamar na so kaina kuma nayi rashin adalci, sosai nake k'aunar mutumin, nake kuma tausaya masa da irin jarrabawar da Allah ya d'ora masa, tunda Zinaru ta bar gari, har yau ba ta dawo ba, sai dai ina samun labari a gurin iyalin Alhaji Harazimi cewa; tana can Swaziland din tayi aure akan aure har da 'ya'ya biyu. Bayan rabuwar mu, hankali na ya kwanta na cigaba da bun'kasa harkokin kasuwanci na, cikin ikon Allah nayi suna a 'kasata da duniya, yanzu haka ina da gidajen mai biyar, tare da kamfanoni da dama, sannan ina harkar sufari ina da jirage uku tare da manyan motoci na daukar kaya, alhamdulillhi, Ubangiji ya azurta ni, da dukiyar da ni kaina ban san adadinta ba, kuma daidai gwargwado ina 'kokarin ganin na sauke hakkin Allah dake kaina, domi duk wanda Ubangiji ya bashi dukiya kamar ya d'ora masa babban nauyi ne, wanda dole sai yayi takatsantsan! ina kokarin ganin na taimaki 'yan uwa da abokanan arziki tare da jama'ar gari da duk wani ma'bukaci. Wannan shine abinda ya faru, shine kuma dalilin da yasa na shirya shiga cikin unguwanni domin neman matar aure, na kuma sauya kammani na zuwa mahaukaci, don kin san a wannan zamanin ba kowace mace ce zata yarda ta auri garma-garma! (mai ta'bin hankali) irina ba, tun lokacin da na fara ganinki na ji kin kwanta min a raina, sai a ka ci sa'a kema kina tausaya min, tun daga lokacin na sanya ki, a raina nake addu'a akan Allah ya tabbatar min dake a matsayin matata, domin ni lalurar ki, sam bata dame ni ba, abubuwa da yawa suka ja hankali na a kan ki, saboda haka ki kwantar da hankali, insha Allah zan nuna miki soyayya fiye da wacce ki ke tunanin mahaukacin nan zai yi miki.'' Ya 'kare maganar da lallausan murmushi a kwance a fuskarsa. Kallon sa kawai nake ina mamakin yanda ya sha gwagwarmaya, zahirin gaskiya ba shi da laifi don ya aikata hakan, domin neman matar aure, na farko wata macen za ta aure shi ne saboda dukiyarsa, mafi akasari abinda yake faruwa kenan, auran kud'i! amma yanzu da yayi hakan ya tabbatar da son gaskiya, kuma yayi abinda duk 'kwa'kwar mutum ba zai gane ba. Hannuwa na ya ri'ke tare da sassauta murya ya ce." Kin yi shiru ba ki ce komai ba. Murmushin ya'ke nayi na ce." Ni kam ba ni da abinda cewa domin har yanzu ina kokwanto akan ka." Shiru yayi na minti uku kafin ya kalle ni da fad'in"Ta shi mu je na nuna miki wani abu wanda zai sake tabbatar miki da gaskiya ta." Ban yi jayayya da shi ba, na tashi kamar yanda ya umarce ni, sai ya ri'ke hannuna muka fita harabar gidan... [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 84&85 Ni dai bin sa nake duk in da ya ajiye 'kafarsa nan nake ajiye tawa, har muka isa wata 'kofa dake wani d'an korido, tsoro na ji ganin gurin yayi duhu da yawa! na ja na tsaya ina 'kokarin cire hannuna dake cikin nasa. a nutse ya kalle ni da fad'in" Menene?" na ce" Wannan d'akin fa?" murmushi yayi kafin ya ce." 'Dakina ne, da nake ajiye muhimman abubuwa, kada ki ji komai ba zan cutar dake ba." Nayi shuru ina kallonsa tare da tunanin wani abu a cikin raina. na ji mutane na fad'in yawanci masu kud'in da sukayi shura a duniya suna da wani 'boyayyan sirri wanda suke aikatawa na sa'bon Allah! haka kawai zuciya bata amince da shi ba, duba da yanayin gurin da ya kawo ni, wani irin d'aki a cikin ciyayi! da wata doguwar 'kofa zururu! gabana na fad'uwa! na ce" Ni dai ba zan shiga ba." Kallona yayi da mamaki a tare da shi ya ce." Saboda me? ko har yanzu ba ki amince da ni ba?" Baki na ta'be da fad'in" A'a kawai ina zargin d'akin ne watak'ila ba abin arzi'ki ne a ciki ba" Yanayinsa ne ya sauya don na fad'in wannan maganar, jikinsa duk yayi sanyi kawai sai ya tsira min ido! ya d'an ban tausayi, amma ban nuna a zahiri ba, sai kawai ma na tafi na bar shi a tsaye a gurin. Sosai ransa ya 'baci da abinda yarinyar take masa, gabad'aya ya rasa gane abinda take nufi, yanayin kallon da take masa shi kad'ai ke damunsa, ya riga ya gama sanya ta a cikin ransa, domin wani irin so yake mata wanda ba zai fasaltu ba, amma yana ganin sai ya sha wahala kafin ya samu kanta, don ganin irin kallon da take masa kamar wanda yayi mata gagarimun laifi. Bai sake tunkarar inda take ba sai wajejan goma da rabi na dare ya shiga gurun da take cikin kayan bacci masu taushi, yana 'kamshin azababben turaransa. Salamarsa kawai na amsa na sunkuyar da kaina don ban yi tsammanin zai shigo ba shiyasa na zauna da vest tare da siket wanda ya tsaya iya gwiwa! da sauri na d'auki dankwalina na yafa a jikina na d'an ture plate din da na ci abinci gefe na had'e jikina guri guda. Zama yayi yana fuskanta ta, yayin da 'kamshin turaransa ya addabeni yana neman ya kashe min jiki. ganin yanda ya tsura min ido yasa duk na tsargu! sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce." Haka ki ke zaune a cikin duhu?" shima ya fad'i maganar ne kawai saboda ya ji dad'in bakinsa, waye ya ajiye ta a duhun idan bashi ba. Shuru kawai nayi masa saboda raina ne ma ya 'baci da maganar tasa, wacce tayi kama da ta rainin hankali. Shirun nawa shi ya bashi amsa da kuma yanayin fuskata don 'kiris ya rage na fashe da kuka! "Babu gaisuwa ko?" Ya fad'a yana haske ni da fitilar wayarsa. Hannu nasa na kare fuskata, babu fara'a na ce" Ina wuni?" Ya amsa babu yabo babu fallasa kafin ya d'ora da fad'in." Kin ci abinci?" Kaina na d'aga masa. Falon yayi shuru na 'yan mintina kafin ya sake wata maganar da ta sanya nayi saurin kallonsa. Ya ce." 'Kwarai kuwa ina da bu'katar matata a wannan daran, ai nayi ma 'kokari kusan watanni uku ina kallonki ban yi komai ba, kada ki manta a cikin labarina na sheda miki cewa; ina da yawan bu'kata! saboda haka sai ki shirya domin ina so ki zama jaruma! mai d'aukar d'awainiyata." Kuka ne ya 'kwace! min da sauri na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28