Chapter 14
Chapter 14
shigo dakin, ido na tsira masa har ya 'karaso gurin da nake zaune, cikin taushin murya ya ce" Tashi ga abincin na samo miki gurin Hajiya." Shuru nayi ban ce komai ba, kuma bani da niyyar tashi. Ya ajiye fulas din kan dirowa, ya hayo gadon yana k'okarin janyo ni, Na cire hannunsa da fad'in" Don Allah ka daina ta'ba ni." A sakarce ya kalle ni, kafin ya girgiza kansa, yanayinsa ya nuna kamar ya fara gajiya da abinda nake masa, ni kuwa duk abinda nake yi, baya damuna, domin har yanzu ban yi na'am dashi a cikin zuciyata ba, amma kuma ina mamakin yanda yake min rawar jiki, kuma ina kallon tsagwaron sona a cikin 'kwayoyin idanuwansa. Kansa ya sunkyar k'asa yayi shuru tare da tsirawa k'asa ido! wannan ya sake tabbatar min da cewa; ransa a 'bace yake da abubuwan da nake masa. Jiki a sanyaye na sauko daga gadon, na shiga band'akin dake cikin dakin, na wanko hannuna na fito, na same shi a yanda yake, kusa da kafafunsa na zauna tare da janyo abincin na bud'e, abinci ne mai rai da lafiya, sai 'kamshi yake, lokaci 'kank'ani yunwar da nake ji ta dawo sabuwa, hannu nasa da bissimillah a bakina na fara cin abincin. Tashi yayi ya fita, minti uku ya shigo da ruwa da lemo ya ajiye a gabana, kunya duk ta rufe ni ganin irin hidimar da yake min, ni kaina na san abinda nake masa bana kyautawa. a hankali na ce" Sannu" bai amsa ba, kawai ya nemi gefen gado ya zauna tare da kunna wayarsa yana dubawa. Har na kammala cin abincin, hankalinsa yana kan wayarsa, na je na wanke hannuna, na zaune can 'karshen gado. A nutse ya kalle ni tare da fad'in" Kin 'koshi?" shuru nayi ina kallonsa don ban ji abinda ya fad'a ba. Murya ya bud'e kafin ya sake maimaita maganarsa. kai na d'aga masa alamar "Eh na ko'shi. Ya ce" Kin shirya saurarata yanzu?" Cikin jin nauyi na ce"Eh" sai ya ajiye wayar hannunsa a kusa dashi, wannan karon beyi yun'kurin rungume ni ba, sai dai ya mayar da hankalinsa kaina sosai kafin ya cigaba da bani labarin rayuwarsa. "Zinaru, 'kanwar maigida na ce, ina nufin mutumin da nake aiki a 'kar'kashinsa, ni dai da bakina da nasa ban ta'ba fad'a masa cewar bani da aure ba, sai kawai ya same ni da wata magana wacce na kasa yin jayyaya dashi. "Saddiku na yaba da hankali da nutsuwarka, wananan dalilin yasa nake neman wata alfarma a gurinka, ina fatan zan samu. Na ce" Alhaji wace irin alfarma ce wannan?" domin ni a gani na mai nake dashi da har zai nemi alfarma a guri na. Ya ce" 'Kanwata nake so ka aura" gabana ne ya fad'i! na kalle shi tare da fad'in" Alhaji ai ina da aure" Murmushi yayi kafin ya ce" Allah ta'alah hud'u ya ce mu aura mutukar muna da iko! to ballanatana kuma na san da cewa; baka da aure, na samu labari a bakin abokinka Faruk, wannan dalilin yasa na nemi wannan alfarmar a gurinka. Wato Faruk ne ya fad'a masa cewa; bani da aure, amma gaskiya ban ji dad'in abinda yayi min ba domin kwata-kwata babu maganar aure a tare dani, amma tunda al'amarin ya kasance haka, dole nayi hakuri, domin ba zan iya jayayya da wanda ya rufa min asiri ba. Na ce" Alhaji Na gode da wannan kyauta da kayi min, tabbas hakane, bani da aure a yanzu, amma shekarun baya na auri 'yar uwata har da rabo a tsakaninmu." Ya ce" Ma sha Allah. ai duk Faruk ya fad'a min komai. amma idan kana ganin da akwai matsala sai na janye. Na ce" Haba Alhaji ai kafi 'karfin komai a guri na wallahi, zan auri 'kanwarka kamar yanda ka bu'kata" Ya ce" Na gode sosai Saddiku da wannan rufin asirin da kayi min, sai dai kuma hanzari ba gudu ba" Shuru yayi fuskarsa da alamun damuwa. Na ce" Alhaji da akwai matsala kenan?" Ya gyad'a kansa da fad'in" 'Kwarai kuwa Saddiku ba zan munafurce ka ba, yarinyar nan ta d'an yi yawo gaskiyar magana kenan, bana tsammanin za a samu budurci a tare da ita, bayan haka kuma tana da aljanu, wanda muke tunanin sune suke sanyata aikata munanan ayyuka" Gabad'aya jikina ya mutu! cikin zuciyata nake tasbihi ga Ubangiji duba da irin kaddarar da take wanzuwa a tattare dani, ba zan ta'ba bijirewa umarnin Alhaji Harazimi ba, domin yayi min abinda ba zan manta ba. Na ce" Alhaji kada ka damu. auran Zinaru a gare ni, kamar jahadi ne, mutukar tayi istibura'i zan aureta na kuma zauna da ita da zuciya d'aya, maganar aljanu kuma, ba su fi k'arfin Allah ba, insha Allahu zanyi iyakar bakin kokarina akan hakan. Nan da nan, ya saki fuskarsa cikin jin dadin lafazi na, ya ce" Na gode sosai Saddiku Allah ya saka maka da alheri, hakika ka rufa min asiri a lokacin da nake bukatar hakan, a duniya bani da matsalar komai, sai ta Zinaru, 'kanwata ce, mu biyu iyayenmu suka haifa, asali mutumin Nijar ne, cikin zinder aka haife ni, neman kudi ya kawo ni Najeria, har nayi aure na tara iyali na, bayan rasuwar iyayenmu, Zinaru ta dawo hannuna, wallahi tunda ta zama cikakkiyar budurwa ta gagare ni, babu irin dukan da ban yi mata ba, amma k'arshe sai ta tattara kayanta ta gudu, sai tayi wata uku hud'u sannan zata dawo gida, wannan dalilin yasa na daina dukanta, sai na tsananta da addu'a tare da sanya matakan tsaro a gidana, amma duk da hakan, sai ta fita yawo, maza na d'aukarta a mota su tafi uwa duniya, wannan shine dalilin da yasa na yanke shawarar yi mata aure, ko Allah zai sanya ta shiryu. Cikin damuwa na ce" Ranka ya dad'e ka kwantar da hankalinka, duk abinda yayi farko, yana da 'karshe! ni nayi maka al'kawarin ri'ke yarinyar nan amana, zanyi iyakar bakin 'kok'ari na insha Allahu. Sosai ya dinga yi min godiya har sai da ya bani tausayi. Wallahi Shahida idan kin ga Zinaru, sai ki dauka ita tayi kanta saboda tsananin kyau! domin ta ko'ina tayi, cikakkiyar mace kyakykyawa, tana da duk abinda namiji yake bukata, dama na fad'a miki asalinsu, 'yan nijar ne, buzaye ne gashinta har baya gata da kyau! sai dai rashin kyawun hali. Amma kin san wani abu, wallahi kwata-kwata ni ba ta kwanta min a raina ba, kawai dai na aureta ne saboda d'an uwanta, dama can a tsari na bana son auran kyakykyawar mace, saboda wasu dalilai nawa. Zuwa na gurinta sau d'aya aka d'aura aure ta tare a gidana, washe garin ranar d'aurin auran Alhaji Harazimi yayi min kyautar d'aya daga cikin kamfaninsa na shinkafa! sosai al'amarin ya bani tsoro mutu'ka! na kalle shi a lokacin da yake bani takardun kamfanin, na ce"Alhaji kada muyi haka da kai, don Allah ka janye wannan kyautar, wallahi ban auri yarinyar nan don abun hannunka ba, na aureta ne tsakani da Allah, da kuma darajarka, amma ban aureta don ka bani wani abu ba. Murmushi yayi tare da cewa" Saddiku ba ka ji bahaushe yana fad'in" Yaba kyauta tukwici ba, wallahi zan iya mallaka maka duk kadarorina, saboda rufamin asiri da kayi,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28