Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wata irin girgiza irin ta rashin mutunci take maganar. Kaina ya d'aure mutu'ka! na kalli Hajiya dake zaune idanuwanta sun ciko da ruwan hawaye sakamakon cin mutuncin da Zinaru ke mata, zuciyata ta cika da tausayinta, na kalle ta har yanzu tana tsaye a kan mu babu alamun risina a tare da ita, raina a 'bace na tashi tare da tsinka mata mari a fuskarta, cikin takaici da bak'in cikin abinda ta aikata na ce" Hajiyar tawa ki ke kira da magulmaciya saboda baki da mutunci." "To idan ba magulmaciya ba mai zai sanya ta zaunar da kai tana shirya maka magana wallahi duk abinda ta fad'a sharri tayi min" Ta karasa maganar cikin k'okarin kare kanta. Na ce" Wallahi ki iya bakin ki, muddun kina bukatar zama da ni to dole ne sai kin daraja Hajiyata mutu'kar kuwa ba haka ba, to zamu sa kafar wando daya dake. "To sai me ? tafad'a tana buga cinya kafin ta cigaba da cewa; kai bari ka ji wallahi ba zan zauna kana taka ni ba, al halin na san da dukiyar d'an uwana kake fankama, akan me? wannan tsohuwar zata sanya min ido a gida har tana fada maka cewa; ina fita yawo to 'karya take munafuka ce" Jikina na tsuma! na sake kai mata wani marin, ta kauce ban same ta ba, Hajiya ta tashi ta rirri'ke ni tana hana ni dukanta, ganin haka yasa tayi mana kallon banza tare da jan dogon tsaki! ta shiga daki ta bugo kofar da karfin gaske! Zubewa nayi kan kujera tare da dafe kaina zuciyata in ban da zafi babu abinda take, Hajiya ita ta dinga tausar zuciyata har na samu sukunin tafiya ofis, amma duk da haka da 'bacin rai na yini, har sai da abokina Alhaji Faruk ya fahimci ina da damuwa. ya matsanta min sai na sanar dashi halin da ake ciki. Ya ce" Ban yi mamakin faruwar wannan abu ba, domin dama can yarinyar bata da mutunci, sai dai shawarar da zan baka shine ka kula sosai, kuma ka sanya matakan tsaro a cikin gidanka, gudun kada ta je ta dauko wani ciwo ta kawo maka gida, ko kuma ta d'auko cikin wani ta kawo maka. Na ce" Aboki na wallahi ni duk a tunanina yarinyar nan, ta shiryu ta daina duk wasu halaye marasa kyau! wannan dalilin ne ma ya sanya na saki jikina da ita har nake mu'amular aure da ita, ashe yaudarata take, tana ha'inta ta. "Kayi hakuri abokina kaddara kowa da irin tasa amma ni kaina ina jajanta maka auran Zinaru, sai dai nayi maka alkawari insha Allahu, zan sanya ka cikin addu'ata, Allah ya kawo maka mafita. Jikina a sanyaye na amsa da "ameen suma ameen abokina. Gabad'aya daina shiga sabgar ta nayi, sannan kuma na saka matakan tsaro sosai a gidan, duk a k'okarin na ganin na kare martabar aurena. Hakan da nayi sai ya sanya ta cikin damuwa mai tsanani, ashe kullum idan na fita zuwa take har d'akin Hajiya ta ci mata mutunci iya son ranta, watarana dai Shukura ta kasa daurewa ta mayar mata da martani, tunda a lokacin yarinyar tana da shekara goma sha biyu, ta fara sanin ciwon kanta. Aikuwa kamar jira take, sai ta zari wayar redio ta kama yarinyar ta dinga dukanta kamar wacce Allah ya aiko, Hajiya tayi-tayi ta 'kwace yarinyar daga hannunta ta kasa, k'arshe ma ta dinga had'awa da ita tana duka. Sosai ta farfasawa yarinyar jiki, da wayar redio, amma abin mamaki! ina dawowa gidan ta same ni tana kuka tare da fadin" Shukura tayi mata rashin kunya har da zagi, na tambayeta dalili sai ta fara kame-kame, ganin haka yasa na ce ta je zan d'auki mataki akan hakan. Lokacin da Hajiya take yi min bayanin abinda ya faru. sai ta fito ta zauna duk abinda Hajiyar ta fad'a sai tace 'karya ne ba haka bane, na kalle ta da tsananin b'acin rai a tare dani na ce" Zinaru idan na sake jin maganarki sai ranki ya 'baci." shuru tayi tana zabgawa Hajiyar Harara. Hajiya ta gama yi min bayanin duk abinda ya faru, raina ya 'baci sosai tunda na fahimci cewa babu laifin tsaye bare na zaune ta kama yarinyar da duka har sai da shatin waya ya fito a jikinta, na ce" Wallahi Zinaru, duk sanda ki ka sake dukan yarinyar nan sai na rama mata, domin ita d'in ba jakarki ba ce, da zaki kama duka sai kace an aiko ki, ina so wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe. 'Budar bakinta sai ta ce" A wai! to ai 'yar taka ba cikakkiya bace, domin ita da shegiya ba su da maraba, duk ina da labarin komai, tsohuwar matarka ta je yawo can saudia ta d'auko cikin shege, ta haife ta kawo maka, saboda kai shakatafe ne kazo kana murna, wannan yarinyar duk ina da labarin komai a kanta" Hajiya ta fashe da kuka tana fadin" Ki ji tsoron Allah Zinaru, ki bi duniya a sannu." Tsaki ta ja mana kafin ta tashi ta shige daki ta bar mu cikin damuwa da tashin hankali. Hajiya da Shukura kuka suke, ni kam! gabad'aya ma na rasa tunanin me nake, Shukura na tabbata jinina ce amma a gaban idona ana sheganta min ita, a lokacin idanuwana suka ciko da 'kwallah, babu shakka Fatima tayi mana gi'bi a rayuwarmu. Gabad'aya gidan haka muka kwana da b'acin rai! in ka cire ita wacce ta haddasa mana damuwar kwana tayi tana shaye-shaye! na tabbatar da hakan ne, lokacin dana shiga d'akinta domin na nuna mata kuskuran da ta aikata. Wallahi numfashi kasa sha'ka nayi sakamakon mugun warin da ya cika dakin, kwayoyi ne da kwala'ben kayan maye har da guntayen sigari wanda ta sha, tana kwance a kasan kafet tana ta sharar bacci. Hankali a tashe na je ofis na kasa katabus! tunani da damuwa sunyi min katutu! ashe ba iyakar bin maza Zinaru keyi ba har da shaye-shaye? wannan abu ya tsaya min a rai sosai da sosai. Bala'i ne ya faru bayan fita ta, domin Fatima ce ta je gidan, bayan dawowarta daga dubai! da yake kasuwanci take sosai, to duk sanda ta samu sukuni tana zuwa ta gaishe da Hajiya sannan ta duba Shukura, sai ta same su cikin damuwa! domin ita bata san ma nayi aure ba a lokacin, 'bacin rai da kishi suka rufe mata ido, lokacin da Hajiya take kuka tana fad'a mata abubuwan dake faruwa. Ta duba jikin Shukura ta ga shatin duka a ko'ina, mayafi ta cire kawai ta nufi dakin Zinaru domin d'aukar fansa. Fad'a da zage-zage su kayi sosai a d'akin, kafin su fito falo, nan ma suka cigaba da cin mutuncin junansu, tare da jifan kansu da munanan kalmomi. Zinaru ita ta fara d'auko makami (wu'ka) wai sai ta kashe Fatima sai ta ga wanda ya tsaya mata. Hajiya Hankalinta ya tashi sosai, gudun kada suyi aika-aika, yasa ta umarci Shukura ta kira ni da wayar mamanta, tana kuka take sheda min abinda yake faruwa. Taimakon Allah ne kawai ya kawo ni gidan, lokacin dana shiga na samu Fatima a ruwan cikin Zinaru! sai dukanta take, don Allah ne ya bata sa'a ta 'kwace wukar, ta samu galaba a

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});