Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kanta. Da 'kyar na iya janye Fatima na juya ina yi mata fad'a, kawai sai saukar wu'ka na ji a baya na, Zinaru ta soke ni da ita, lokaci guda jini ya jika riga ta yana d'iga a gurin. da gudu ta shiga dak'i ta kulle 'kofa! Hankali a tashe suka rirrik'e ni suna kuka, ni kam ni kad'ai na san azabar na da nake ji, sosai wu'kar ta hud'a jikina. Asibiti muka nufa. Emagency su ka bani taimakon gaggawa, sai dana na kwana tukkuna na dawo gida da tarin magunguna, bayana nannad'e da bandaji. Ban iya fad'awa Alhaji Harazimi komai ba, kawai dai na ce dashi tsautsayi ne ya ritsa ni wani mai babur ya buge ni lokacin dana fito daga mota ta. Bayan tafiyarsa abokina Alhaji Faruk! Ya ce" Gaskiya ka bani mamaki Alhaji Saddiku mai zai sanya ka rufa mata asiri, wallahi bari na fada maka da yarinyar nan da ta samu nasara a kanka kashe ka za tayi, to mai yasa za ka cigaba da zama da ita, tunda ta zama annoba, kamata yayi ka shedawa d'an uwanta halin da ake ciki, cewa; tunda akayi auran nan baka samu kwanciyar hankali ba. Girgiza kaina nayi na ce" Ba zan iya fad'awa Alhaji Harazimi wannan al'amari ba, domin ni nayi masa al'kawari cewa; zan jure zanyi hakuri da halayen 'yar uwarsa, kuma idan ka duba akwai shekaru a tare dashi, wanda ya kamata a ce yana samun nutsuwa da kwanciyar hankali a irin wannan lokacin, wallahi da bakinsa ya sheda min cewa, a duniya bashi da damuwar kowa sai ta Zinaru, ita kad'ai ce matsalarsa, to mai zai sanya na fad'a masa abinda zai d'aga masa hankali, wallahi ko yarinyar nan, zata kashe ni ba zan fad'a masa abunda zai d'aga masa hankali ba, zan cigaba da bashi amsa d'aya a duk lokacin da ya tambaye ni zan ce masa muna zaune lafiya. Shuru yayi yana jinjina kai! na san yana mamakin karfin hali na, wanda ba kowa ne zai iya jurar wannan al'amari ba. To har na 'karaci jinyyata Zinaru ba ta ce min sannu ba, sai dai duk san da ta ji muryar Fatima a gidan, za ta fito daga d'akinta ta nemi fitina, ni nake tsawatarwa da Fatima, a lokacin zata ci mutuncinta sosai tare da fad'in sai dai gani daga nesa amma Saddiku ya fi 'karfinta, wani lokacin Fatima har kuka take saboda takaici da 'bacin rai! Tsayin sati hud'u bana kula ta, don gabad'aya na ajiye ta a gefe guda, sabgogin gabana kawai nake, sai ta same ni a daki bayan na dawo daga ofis, ta nemi guri ta zauna tana kallona. Na ce" Kina bukatar wani abu ne?" "Eh ina da magana da kai" tafada tare da tsira min ido, lokacin na karanci abinda yake damunta. Babu walwala a tare dani na ce" Ina sauraranki. "Ka san dai ba dutse ka ajiye a gidanka ba ko?" Shuru nayi tare da tsira mata ido! ta cigaba da cewa" Tsayin sati hudu da kwanaki baka kula ni ballantana ka bani hakkina na aure, to gaskiya ni dai wallahi na gaji, idan ba zaka iya ba ka sake ni na fita na samu wanda zai d'ebi min kewa" Zama nayi ina fuskantarta na ce" Zinaru lafiya ta ki ke bu'kata ko?" "Ban gane ba?" tafad'a tana ta'be baki. Na ce" Kwanana nawa a kwance ina jinyya wanda kece sanadi amma baki duba ni ba, ballanatana kiyi min sannu, yanzu Allah ya bani lafiya kin zo kina min wata maganar banza. Shuru tayi tare da sunkuyar da kanta. Na ce" Kin yi min abubuwa masu muni! amma na ajiye su a gefe ba don komai ba, sai don ina duba wani abu, kada ki dauka kin fi k'arfi na, ko kuma tsoro ya hana ni, d'aukar mataki a kanki, ko d'aya, ina da yanda zanyi dake wallahi ina duba wani abu ne amma da ba don haka ba, zaki san asalin waye Saddi'ku" "Ka ga nifa ban nemi wata magana ba, ni fa dole akayi min na aureka amma wallahi na fi jin dad'in zama a haka, idan namiji nake bu'kata akwai su kala-kala sai wanda nayi ra'ayi. Cike da takaici nake kallonta kafin na ce" Ki ji tsoron Allah wallahi, kuma ki bi duniya a sannu idan ba haka ba zaki yi nadama a rayuwarki, menene abin tunk'aho gurin aikata zina? menene abin burgewa? da har ki ke tutiya da aikata alfasha! kina ta 'kama da kyau! da surar jiki ko? to ki sa ni lokaci guda ubangiji na iya juya hallitarki, ki zama abar tsoro abar 'kyama, a gurin mazan dake bibiyarki, su guje ki, babu abun burgewa a gurin aikata abinda Allah ya haramta don haka wallahi kiyi hattara" Lokacin jikinta yayi sanyi, da alama nasiha ta, ta ratsa mata jiki. Na cigaba da cewa" Kada ki sake kiran Shukura da shegiya domin yin hakan, zai sa ni dake mu sa kafar wando d'aya domin ita kad'ai gare ni, kuma ni ne ubanta. Ta ce" To ai nima 'kawata ce ta fad'a min cewa; sun zauna d'aki d'aya da Fatiman a saudia kuma ta tabbatar min da cewa Fatiman 'yar iska ce tana bin maza." Takaici ya cika min zuciyata, na ce" To 'karya take miki, lokacin dana rabu da Fatima tana tare da ciki na, idan kin duba sosai za ki ga kama a tsakanina da Shukura don haka kada na sake jin wannan maganar ta fito daga bakin ki." Ta ce" To na ji ni dai gaskiya idan kana so mu samu zaman lafiya ka cigaba da bani hakkina, domin shine dalilin da yasa zuciyata take zafi wani lokacin. Na ce"Babu damuwa in dai wannan ne, zanyi kokarin sauke hakkinki da yake kaina." lokaci 'kan'kani ta saki fuskarta har tana bani labarai, ni dai jin ta kawai nake cikin zuciyata nake mamakin halayenta, wani sa'in ina gazgata maganar d'an uwanta, lallai tana da matsalar mutanan 'boye! [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 82&83 Haka na cigaba da zama da Zinaru da dad'i ba dad'i nake ha'kuri da halayen ta ina kawar da kaina gudun 'bacin rai da rikice domin duk ranar dana dau'ki mataki akan rashin arzi'kin da take a gidan, iskokai! take tayarwa ta yini ta nayi wani sa'in har kwana take tana buge-buge da birgima! duk abinda ya zo hannunta d'auka take ta kai min duka dashi!Zinaru ta yi min rauni a jikina wanda ba zai lissafu ba, damuwa da fargaba gami da tashin hankali yasa ciwona ya ke tashi akai-aikai, wanda kusan duk sati sai na ga likita ya duba ni tare da bani shawarwari! wasu al'amuran nawa duk sun tsaya sakamakon masifar da nake ciki, gashi a lokacin Allah ya bud'e min 'kofafin samu ta ko'ina, bayan kamfanin shinkafa da Alhaji Harazimi ya bani kyautarsa, cikin hukuncin Allah na bud'e wani kamfanin amma na sumunti, sai gonaki uku da na saya nake noma wake da alkama da kuma gero, harkoki na sun bud'e sosai! kuma ina samun alheri fiye da tunaninki, a lokacin abokina Alhaji Faruk yake tsokana ta da fad'in "Zinaru ita ce matar arziki na taurarinmu sun zo d'aya, wai tunda na aure ta nake samun d'aukaka da cigaba, murmushi kawai nayi a lokacin

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});