Chapter 21
Chapter 21
ce" Ni wallahi ban shirya wannan al'amari da kai ba, domin dai ni ba kai nake so ba, saboda haka ka ajiye wannan maganar ni kawai ka dauke ni ka mayar wa da iyayena" Murmushi yayi mai ciwo kafin ya ce." Ai kin shigo hannun Saddiku dattijon nan mai furfura! babu rabuwa a tsakanina dake yarinya sai dai mutuwa." Tashi nayi da gudu na shige d'aki na kwanta a kan gado ina kuka! ni gaskiya ba zan iya bashi kaina ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma ban shirya zaman aure dashi ba. Gadon ya hayo ya janyo ni jikinsa yana so ya rungume ni ina turjewa tare da fizge-fizge! sai kawai yasa min 'karfi ya matse ni tsam! a jikinsa yana ta jijjigani tare da shafa gashin kaina! rarrashina yake tamkar 'yar goye yana ta fad'a min kalaman soyayya a cikin kunnena har ya samu nasarar kashe min jiki ta hanyar fad'in" Da wasa yake babu abunda zai yi min. jin haka yasa nayi shuru, tare da gyara kwanciyata a jikinsa. Cikin wata murya na ji maganarsa a kunne na. ya ce. "Me yasa ki ke tunani mara kyau a kaina?" Shiru nayi ban bashi amsa ba. Ya cigaba da cewa; ba zan gaji da fad'a miki cewa ni ba zan cutar dake ba, kuma duk abinda ya faru, akwai dalili wanda na sheda miki, amma ban yi tunanin haka daga gare ki ba don Allah kiyi hakuri mu zauna domin mu raya sunnar ma'aiki tare." Jin yanda yake had'a ni da Allah yasa jikina ya mutu! na ce" Ni fa muddin kana so na zauna da kai domin yin rayuwar aure sai ka kasance yanda na sanka a farko, domin ni fi bukatarka a haka." Ya ce." Hakan ba zai yuwu ba, ki so zahiri na, shine abinda na fi buk'ata, amma wancan da ki ke so duk gaibu ne, shiri ne, nayi domin cimma wata manufa kuma Alhamdulillhi na samu nasara, amma ba zan zauna cikin yagaggun kaya da 'kazanta ba, wannan zai janyo min wani abu daban." Na ce" Ni kam na fi bu'katar ka a haka, tunda kana ganin hakan ba zai yuwu ba shikkenan." Murmushi kawai yayi bai sake magana ba. ganin haka yasa na tashi daga jikinsa na matsa can 'karshen gado! na ja bargo na rufe jikina. Bacci ne mai nauyi ya d'auke ni, ko da na tashi da asubah! baya d'akin, ban damu ba, kawai na tashi na shiga band'aki da tunani mai yawa a cikin raina. Sai da na shirya tsaf sannan na nufi cikin gidan don gaishe da Hajiya. Da sallama a bakina na shiga falon, Hajiya da Shukura suna zaune a gurin cin abinci. na 'karasa a nutse na tsuguna har kasa na gaishe ta, ta amsa da fara'a mai yawa a fuskarta. Cikin wani irin yanayi mara dad'i Shukura ta gaishe ni kamar anyi mata dole. nima na amsa babu yabo babu fallasa. Hajiya ta ce" Ki zauna ki karya kummalo mana. Na ce" Hajiya na ci abinci a guri na kafin na fito. "Allah sarki." Ta fad'a kafin ta d'ora da fad'in." Mijin naki ai tun asubah ya tafi can garin mu jibia da yake duk 'karshen wata yana zuwa, ina fatan kunyi sallama da juna?" Da sauri na ce" Eh Hajiya ya fad'a min, Allah ya dawo dashi lafiya" Ta amsa da "Ameen ya Allah." Tsaye na mi'ke tare da fad'in" Hajiya zan koma guri na sai an jima. Ta ce"To shikkenan mu jima da yawa." Tana fita Shukura ta kalli Hajiya da fad'in "Wai Daddy ya rasa wacce zai aura sai kurma! wallahi Hajiya abin yayi min ciwo sosai! tuntuni Mommyna take so ya dawo da ita ya'ki ya je ya kwaso wannan k'azamar." Hajiya ta ce" Ke dai ki iya bakin ki Shukura bana son tashin hankali don Allah. domin abin farin ciki ne a guri na da Allah yasa yayi auran ina raye, maganar babarki kuma ki ajiye ta, a gefe domin da zai dawo da ita da tuntuni anyi an gama, saboda haka ki d'auki matar babanki a matsayin uwarki, kin fi kowa sanin halin mahaifinki, don haka kada ki ga kuna sa'anni da yarinyar nan, ki raina ta, duk 'kan'kantar ta uwarki ce, tunda tana auran mahaifinki." Kawai sai ta buga tevur d'in cin abinci tare da fad'in" ba zai yuwu ba wallahi." hanyar d'akinta ta shiga tana surutai! Hajiya tabi ta da kallon mamaki! "Mommy kina da labarin Daddyna yayi aure kuwa?" ta fad'a cikin ba'kin ciki da takaici! Daga d'aya 'bangaran Hajiya Fatima ta ce" Aure? yaushe yayi babu labari?" Nan duk ta kwashe komai ta sheda mata. Ta ce" Amma gaskiya 'Dan-gaske ya ba ni kunya, duk diddigin nasa anan ya tsaya? auran kurma wacce take da nakasu, mtsww! kada ki damu idan na dawo zan zo gidan, ai ko yana so ko baya so sai ya mayar dani d'aki na, ko kuma na hana shi kwanciyar hankali da matar tasa. Ta ce."Mommy ni na rasa wace irin zuciya ce da Daddy, ke fa 'yar uwarsa ce, yana kallon yanda ki ke katangala! kiyi nan kiyi can, duk saboda shi amma ya 'ki ya saurareki, gaskiya Momy kiyi wani abu akai, domin ba zan iya bud'e idona na kalli kucakar yarinyar can a matsayin matar mahaifina ba, wai har Hajiya tana fad'in" Dole sai nayi mata biyayya" Hajiya Fatima ta ja tsaki tare da cewa; ki rabu da Hajiya Saude tuntuni na fahimci cewa; ba ta son lefinsa, saboda yana da kud'i! babu yanda ban yi da ita ba, akan tasa baki ya mayar dani, amma ta'ki, saboda haka idan na dawo daga dubai, a gidan zan sauka duk sai na rikirkita musu lissafi tunda abin ya kasance haka." Ta ce." Yawwa Mommy Allah ya dawo dake lafiya." Ta amsa da "Ameen kafin ta kashe wayar zuciyarta a 'kuntacce! [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 86&87 Ranar na yini cikin zullumi da tunanin hanyar da zan bi gurin ganin na yi zaman aure da shi kamar yanda yake bu'kata, gaskiyar magana ba shi da wata makusa ta kowane fanni yana da kyawun hali, uwa uba kyawun zuciya tare da nagartar da ba kowa ne mai arzi'ki ne yake da ita ba, yanda na fahimce shi, bai d'auki kansa wata tsiya ba, irin yanda masu kud'i da mulki sukeyi, ya ajiye kansa dai-dai yake da kowa, kuma arzikinsa bai rufe masa ido ba, yana alheri sosai, tunda ni ganau ce, domin duk sati ranar juma'a kenan, gidan cika yake yi da bil-adam yara da manya dattijai da matasa har da mata masu buk'ata, kuma da kansa yake fitowa ya gaisa da kowane sashi kafin ya zauna ya fara robon kayan abinci da kud'i! shiyasa a kullum bakin gate d'in gidansa baka raba shi da al'majirai kala-kala, daga wata uwa duniya ma zuwa suke kuma duk yawansu sai ya faranta mu su rai, mutuk'ar kaga sawun 'kafa ya d'auke a gidansa, to ka tabbata cewa; baya gari yayi tafiya, amma duk da haka dai ba'a fasa aikin alherin ba, al'majirai irin na tsangayu suna zuwa kar'bar sadakar abinci mai rai da lafiya, wanda ya bada umarin cewa; ko baya gari kada a sauke tukunyar abincin sadaka.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28