Chapter 3
Chapter 3
wanda Allah ya haramta. A cikin al'kur'ani mai girma Ubangiji subahanahu-wata'ala ya umarce ku da ku aura daga d'aya zuwa biyu da abinda yayi sama, mutukar kuna da iko kuma za kuyi adalci." Ta d'an sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa; Allah yayi maka komai na daga jin dadin duniya ya wadataka da arziki da rai da lafiya da ji da gani bai tauye ka ba, to mai zai sanya ka butulce masa? kana da dukiyar da zaka auri mata hud'u ka ajiye a gidanka domin raya sunnar ma'aiki salallahu alaiyi wassalam, amma kana zubar da 'kima da mutuncinka, ka sani cewa duk abinda ka yi a kan dan wani sai anyi da naka, saboda haka ka ji tsoron Allah ka daina bibiyar rayuwata." A maimakon jikinsa ya mutu da nasihar ta, sai kawai ta ga yana murmushi tare da wasa da gemunsa kamar wacce tayi abin dariya sai kallonta yake yana murmushi, tsayin mintina uku kafin ya ce" Na gode da nasiha malama, amma ina sheda miki cewe; ina nan akan bakana, ba zan janye kudiri na ba, dole zaki bani kanki ko kina so ko ba kya so, ki je kiyi shawara na baki kwana uku kamar yanda na fad'a miki da farko." Ya na gama maganarsa ya tashi ya haye sama ya bar ta zaune a gurin cikin tsantsar damuwa da tashin hankali. A tsakanin kwanakin sosai ta mayar da hankalinta gurin karatun al'kurani mai girma tare da shedawa Allah damuwarta, a yanzu dai ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko, dalili babu wanda za ta je ta fada masa damuwarta saboda wayar da take hannunta ma tun ranar da su kayi magana da Saliha ya 'kwace! har ya tafi bai bata ba. Tana dai zaune a gidan tare da mi'ka lamuranta ga Allah. Yau ne cikar kwanakin da ya gindaya mata. Tayi ta k'o'karin danne damuwarta amma hakan bai samu ba, sai da Hajiya Saude ta fahimci damuwa a tattare da ita a lokacin da ta shiga domin gaishe ta. Ta kalle ta, kafin ta ce." Shahida cikin kwana biyun nan ina ganin damuwa a tare dake ko da akwai wani abu da mu ke miki?" Ta ji kamar ta fad'a mata abubuwan da suke faruwa, sai kuma wata zuciyar ta tsawatar mata saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, watakila idan ta tona maganar ita ce zata kwana a ciki, domin babu wanda zai yarda da ita. Ta girgiza kai da fadin." Hajiya babu komai kawai dai bana jin dadin jiki na ne." Tayi murmurshi kafin ta ce" Wai cikin naki wata nawa ne?" Da sauri ta ce." Hajiya bani da ciki fa." "Ke haba dai 'yar nan, to wannan laulaye-laulayen da ki ke na menene?" Shuru tayi ba tace komai ba. Shukura ta fito daga d'akinta ta shirya tsaf sai kamshin turare take, ta nemi kujera ta zauna hankalinta a kan wayarta ciki bada Umarni ta ce." Ke Shahida ki shiga dakina ki gyara min sannan kuma ki wanke toilet." Hajiya Ta ce." Ai yau sai dai kiyi da kan ki ba ta da lafiya" Wani irin kallo tayi wa Shahidan tana ta'be baki da fad'in." Hajiya gaskiya ba zan iya wani abu ba yanzu na riga nayi wanka ai d'akin nawa babu wani datti sosai! kawai ta tashi ta je tayi dama aikin ta ne" Ta ce." A'a ki sa Marka mai aiki tayi miki mana ita wannan d'in ki kyale ta rana daya dai da huta." Tana k'okarin magana ya k'araso gurin, duk sai su kayi shuru, suna kallonsa amma banda Shahida kanta yana 'kasa domin tunda taji 'kamshin turaransa ya cika gurin, hankalinta ya tashi, gabanta in banda fad'uwa babu abinda yake. Ya ce." Hajiya maganar me ku ke ne? zuwa na gurin kun yi shuru sai kace wani mala'ika" Murmushi ta yi kafin ta sheda masa maganar da suke. Ya harari Shukuran kafin ya ce." Ke aikin me ki ke da ba zaki gyara abinda ki ka 'bata ba." Tayi shuru ba tace komai ba. Ya ce." Kada ki kuskura ki sake sanya ta aiki, ke kika 'bata kuma ke zaki gyara abinki." A sanyaye ta ce."To Daddy." Jin haka yasa ta tashi da niyyar tafiya gurinta ta d'an risina da fadin." Hajiya a tashi lafiya zan ni koma guri na." Ta ce." To sannu, ubangiji Allah ya baki lafiya amma yana da kyau! kuje asibiti likita ya dubaki sosai laulayin yayi yawa gashi kin ce baki da ciki.'' Murmushi kawai tayi ta juya tare da kallon gefen da yake zaune, bata yarda ta kalle shi ba ta ce."Alhaji a tashi lafiya." Shima ba tare da ya kalle ta ba ya amsa hankalinshi a kan wayarsa. A gaggauce ta fita tana cigaba da neman tsarin Ubangiji akan mummunan al'amarin da yake bibiyar rayuwarta. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 65&66 Lamarin dai babu dad'i domin wani lokacin idan tsanani yayi yawa sai mutum ya gwammace mutuwarsa akan rayuwar da yake, sai dai kuma hausawa suka ce idan aski yazo gaban goshi to ya fi zafi! hakane kowane bawa akwai irin tasa kaddarar wanda babu wanda ya isa ya goge ta, to ita kam tana tunanin wannan ce kaddararta wanda ta tazo da kafafunta ta sameta har inda take, babu shakka wannan mutumin ya zame mata jaraba da kuma kaddara, ba kowa ne sila ba sai Mijinta wato wanda ta kwallafa rai a kansa take ganin shi din mai kaunarta ne, ashe kallon kitse takewa rogo, mutum ne shi azzalimi mayaudari, ta amince masa ya cutar da ita. Har ta gaji da zubar da hawaye, watakila rashin kukan ne ya janyo mata toshewar mak'ogwaro domin wani k'atoton abu ne ya zo ya tsaya mata a wuya! sai kuma damuwa da fargabar da tayi mata katutu! Da 'kyar ta iya tsakurar abinci cokali biyar kacal ta ci gabad'aya cikinta ya cushe! tasha ruwa ta kwanta lamo a tsakanin kujeru! wannan duhun ma babbar masifa ce, domin tuntuni batiran fitilar suka mutu! sunyi ruwa basa bada haske, gashi kwana biyu bata ga Sule ba ballantana ta fad'a masa. Sosai kanta yake mata ciwo domin ba wani cikakken bacci take samu ba saboda tunani yayi mata yawa shiyasa bacci ya kauracewa idonta sai dai ta yi shi a tsin-tsinke. Lumshe idonta tayi tare da kiran sunan Allah da ya kawo mata d'auki! a rayuwarta. Motsi ta ji a kanta bayan masifaffen kamshin turaransa da ya bakunci hancinta, sai tayi gaggwar bud'e ido ta tashi a razane! shine ya shigo, to ta wace hanya? bayan duk ta rurrufe k'ofofi! Innalillahi-wa'ina ilahi raji'un! abinda ta fada kenan kafin ta ja jikinta ta matsa can gefe tare da takurewa a jikin kujera. Gurin yayi shuru bayan zamansa da minti biyar ya bud'e muryarsa sosai kafin ya ce." A ina maganarmu ta kwana ina fata baki mance cewa yau ne cikar kwanakin dana baki ba. Shuru tayi tana kallonsa amma ba sosai ba, saboda babu hasken a dakin sai na wayarsa da ya kunna. Ya ce"Shurun da ki kayi ya tabbatar min da cewa kin amince kenan?" Uffan ba tace masa ba, wata mummunar shawara ta yanke a zuciyarta. kawai sai ta tashi ta nufi kicin cikin zafin nama! Ya bi ta da kallo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28