Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

To shikkenan Allah ya baki iko." na amsa da "ameen" kafin na fara hawa 'kafar benan cikin sassarfa. Zaune a kusa dashi na samu Shukura tana kuka tare da rungume hannunsa a 'kirjinta fuskarta ji'ke da hawaye! sai duk suka bani tausayi ita da shi, mafarkin da nayi yana nema ya tabbata. A sanyaye na 'karasa bakin gadon, wanda tun da na shiga d'akin yake kallona, kuma bai daina ba har na zauna a kusa da shi. Ta kalle ni a banza ce kafin ta ja tsaki! mai tsayi wanda duk rashin ji na, sai da kunnuwa suka amsa sautin tsakin! kaina kawai na sunkuyar, ita kuma ta tashi ta fita daga dakin tare da bugo 'kofar da k'arfin gaske. Tun da na sunkuyar da kaina bai d'ago ba, domin na ji ciwon kallon banzan da tayi min tare da tsakin da ta ja min. Sautin maganarsa na ji, na d'ago kaina ina kallonsa, ya sake maimaita maganarsa wacce yake da tabbacin cewa; ban ji ba, wannan karon da sauti mai 'karfi yayi maganar. "Kiyi hakuri." Ya fad'a tare da kamo hannuna yana 'kokarin tashi zaune. sai kawai na tsinci kaina da taimaka masa ya tashi na jingina masa fillo a bayansa kafin na koma na zauna. A nutse na ce."Ai ku za a bawa hakuri." Ya ce." Saboda me?" murmushin takaici nayi kafin na ce" Na ga gabad'aya kun d'auki lefi kun d'ora min, domin na shigo na ga Hajiya tana kuka tana sheda min cewa; damuwata ce ta haddasa ciwonka ya tashi, bayan haka kuma, a gabanka Shukura ta ja min tsaki tana min kallon banza! idan da matsala kawai ka rabu da ni, domin ni bana so shiga cikin zargi, bayan da bakinka kafad'i ga wacce ta haddasa maka ciwon tun fil-azal, amma ana neman d'ora min jakar tsaba." "Kiyi hakuri." Wannan kalmar ya furta kafin ya rintse idonsa, alamun sun nuna baya bu'katar doguwar magana. Na ce" Ya jikin naka?" da sauk'i ya fad'a ba tare da ya bud'e idonsa ba. Shiru d'akin yayi na 'yan mintina kafin na ce" Yanzu me kake bu'kata?" Bud'e idonsa yayi yana bi na da kallon mamaki! Fuskata na saki amma ban ce komai ba. Ya girgiza kansa tare da fad'in" Ba abinda nake bukata a gare ki, sai alfarmar ki zauna tare da ni, ki kuma cire shakku a kaina, bayan haka kuma ki ri'ke ni amana." Jim nayi na minti biyu kafin na ce" Shikkenan zanyi 'kokarin ganin nayi hakan muddin zan fita daga zargi don bana so wani abu ya same ka mutane su ce ni ce sanadi. Murmushi yayi, yana min wani irin kallo kafin ya ce'' Babu wanda zai zarge ki don kin taka sawun 'barawo, kin 'karasa gawar da ba taki ba, dama can bani da cikakkiyar lafiya, ko da Hajiya tayi wannan maganar, ba da wata manufa ba, tayi ne domin ki gyara kuskuranki, ma'ana ki zama mai kula da mijinki domin ki samu rabauta ranar gobe 'kiyama." Sunkuyar da kaina nayi tare da wasa da yatsun hannuna, ya tashi a hankali ya nufi band'aki cikin 'kwarin jiki, sai kawai na tsinci kaina da bin sa da kallo da tausayinsa 'kadan a cikin raina. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 88&89 Gadon na shiga bi da kallo kamar me neman wani abu. wayoyinsa ne akai sai farin gilashinsa da kuma littafin husunul muslim a ajiye a gefe, sai kuma 'kamshin turaransa da ya mamaye d'akin, komai nasa a tsanake babu harigido a ciki, dattijo ne mai kamala da hallin dattako. Ajiyar zuciya na sauke tare da tsirawa k'ofar 'bandakin ido! fitowarsa daga band'akin yasa nayi gaggawar d'auke kaina, kai tsaye 'katuwar wardrobe din da ta cinye bango guda ya nufa yana neman kayan sawa. A nutse na je na tsaya a kusa dashi tare da fad'in" Ka je ka zauna na duba maka kayan. Kallo na yayi da mamakin magana ta. Sai na d'an saki fuskata tare dasa hannuna kan kayan nasa ina dubawa. Ban an kara ba kawai na ji shi a jikina, ya zagaye k'ugu na da hannuwansa tare da d'ora ha'barsa a kafad'ata. Cikin fad'uwar gaba na juyo rigar dake hannuna ta fad'i a gurin. 'Kokarin k'wace jikina nake yana sake matse ni a jikinsa dake wani irin karkarwa! 'Kafafuna suka shiga kyarma! jin yanda yake yawo da hannuwansa a sassan jikina. Kuka nasa tare da ture shi da 'karfi na matsa gefe ina gyara zif d'in rigata da ya zuge min. Da azama! na kama hanyar fita, sai yayi saurin tarar gabana, ya sanya mukulli a jikin 'kofar d'akin, ba tare da ya ce komai ba ya ja jikinsa da babu 'kwari ya hau gado ya kwanta har da jan bargo. A sanyaye na ce" Ka bud'e min 'kofar na fita. Shiru yayi be ce min komai ba. Ganin haka yasa na zauna kan kujera tare da zabga tagumi! abinda yayi min yanzu ya tsorata ni, mutumin da bashi da lafiya. Motsin ta'ba 'kofa na ji sai nayi sauri na kalle shi har yanzu yana cikin bargo a lullu'be. Na ce" Za'a shigo fa." Shiru babu amsa. Gurinsa na nufa domin neman mukkulin, ya bud'e fuskarsa da alamun bacci ya bani mukullin da fad'in."Amma don Allah kada ki ce zaki koma wannan gurin ina bukatar ki zauna tare dani, ina neman wannan alfarmar." Jikina ne yayi sanyi jin yana had'a ni da Allah kamar ya san kud'iri na kenan. Ni kaina ina jin wani iri a duk lokacin da yake 'kas'kantar min da kai. A sanyaye na je na bud'e 'kofar. Shukura ce ta shigo hannunta ri'ke da kwandon abincin. wani irin wula'kantaccan kallo tayi min kafin ta wuce cikin d'akin. Sosai raina ya 'baci da iskancin da yarinyar take min, idan tayi min wulakanci a can baya nayi ha'kuri, to yanzu zahirin gaskiya ba zan iya jura ba, domin kuwa a matsayin uwa nake a gurinta ko tana so ko ba ta so dole ta girmama ni kamar yanda zata girmama mahaifinta. idan ma ba zata gaishe ni ba to ba zan jure kallon banza da zagi ba. K'ofar na rufe na je na zauna ina kallonta tana fad'in" Daddy ka tashi ka ci abinci ka sha magani." Na kalle ta babu walwala a fuskata na ce" Ki rabu da shi mana ko ba kya ganin bacci yake?" Ta juyo a fusace! tare da cewa" Kin ga malama kada kiyi min shishshigi" Kafin nayi magana har ya 'bud'e fuskarsa. rai a 'bace! ya kalle ta da fad'in" Tun da kin kawo min abincin, tashi ki je kawai." A sanyaye ta tashi ta fita kamar ta fashe da kuka. Na kalle shi yana 'ko'karin sake rufe fuskarsa na ce" Yana da kyau! ka tashi ka ci abincin sai ka sha magani ko." Minti biyu da magana ta ya ta shi tare da cire bargon dake jikinsa ya sauko da 'kafafunsa 'kasa! sai kuma na ga ya dafe kansa da duk hannuwansa. Ganin haka sai jikina yayi sanyi na tashi na je kusa dashi na zauna. Cikin zuciyata nake jin d'an tausayinsa, da alama yana jin jiki daurewa kawai yake. kafad'arsa na dafa a hankali na ce"Sannu kan ka ne yake ciwo ne?" Girgiza kansa yayi ba tare da ya

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});