Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Maganar shekaru, gaskiya ya kwana biyu a duniya domin ya wuce shekaru ar'ba'in da biyar don a 'kalla zai yi shakara hamsin, amma saboda yanda yake kula da kansa shekarun basu nuna ba, bayan haka kuma yana da kyawun jiki, dogo ne amma bashi da ki'ba mai muni! sai dai kowace ga'ba a jikinsa a bud'e take, wannan ya samo asali ne, sakamakon atisayen da yake a duk ranakun karshen ma'ko, yana da kyau! daidai gwargwado don bashi da muni! ya fi ni kyau! nesa ba kusa ba, gashi da gayu da tsafta! kowace mace ta same shi a matsayin miji ta more! amma ni har yanzu zuciyata ta kasa aminta da shi, domin na zauna nayi rayuwar aure dashi, kuma na rasa a wane matsayi zan ajiye shi a cikin raina. Da wannan tunanin na yini, don sai bayan magariba ma na shiga kicin na dafa taliya fara tunda na kan yi miya ta kwana biyu zuwa uku, don na kori yunwa na zauna na tuttura abincin ba don baki na yana so ba. Wanka nayi na sanya doguwar rigar bacci ma dan taushi, saboda yanayin garin ana zafi, falo na fito, kafin na zauna sai dana zuge labule domin haske ya shigo, tunda harabar gidan, da fitilu ko ina, gurina ne, kawai babu fitila, to idan na bud'e labule haske yana shigowa, don tun ina jin tsoro har na saba. Zama nayi ina sa'ka wasik'ar jaki, har lokacin da na ji agogo ya buga goma daidai na dare, na sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da gyara kwanciyata kan dugowar kujera, ina tunanin Baba Asabe da sauran 'yan uwa da mahaifi na, hawaye ne suka zubo min nasa hannu na goge wasu na na sake zubowa, cikin wannan yanayin ya shigo ya same ni, nayi saurin juya fuskata baya ina rintse idona. Sallama yayi bata amsa ba, kuma ya ga sanda ta juya baya a lokacin da ya shigo. Bai ajiye abin a ransa ba, ballananta ya dame shi, kawai abinda yake nazari shine, yarinyar ta samu dama a kansa ne, tunda ta fahimci irin azababben son da yake mata, dama kuma ta'kidin mata ne hakan, mutu'kar sun fahimci namiji na k'aunarsu shikkenan iskanci iri-iri zai biyo baya. Ya zauna a gefan ta tare da riko hannunta kafin ya 'bud'e muryarsa yanda za ta ji ya ce" Na zama dodo abin gudu ko Shahida?" Shiru ba tayi magana ba, sai ya d'ora da fad'in." Ki tashi mu tafi can cikin gidan, na gaji da zaman ki anan gurin, tunda wasan kwaikwayon ya 'kare." Ta shi nayi ina kallonsa shima ya tsira min nasa idon, wanda nake hango tsantsar gajiya a ciki. Na ce" A'a ka bar ni anan tunda dai kai ka ajiye ni kuma nan d'in kaga ya fi cancanta da ni.'' Ya ce." Ba zai yuwu ba dole zaki koma cikin gidanki da zama kiyi rayuwa mai kyau kamar yanda ko wace mace take a gidan auranta." Cikin rauni! na ce" Ka da ka manta fa, da bakinka ka ke fad'in kud'i ka bayar aka baka ni, to mai zai sanya ka ajiye ni a guri mai kyau?" Shiru yayi yana kallona, na goge hawayen dake zubo min na ce, idan ka manta ni ban manta ba, babu irin cin mutuncin da ba kayi wa mahaifina ba duk da na san halinsa ne ya janyo masa cin zarafi, saboda haka ni me zanyi a cikin gidanka domin ni wannan auran har yanzu wasan kwaikwayo na d'aukashi'' Ransa a 'bace ya ce." Kada ki sake kiran auranmu da wasan kwaikwayo kin ji ko." Kaina na d'auke tare da fad'in" Ai kai ka shirya kuma kai ka bada umarnin sunan shirin film din naka wasan kwaikwayo." Na sake maimaitawa duk da ya nuna baya so ban ji shakka ba. Shiru falon yayi ni da shi kowa da nazarin da yake, ganin kawai ya tisa ni a gaba yana kallo yasa na yun'kura zan tashi, sai ya ri'ke min hannu, still idonsa yana kaina, gabadaya jikina ya mutu! domin bana iya jurar wannan kallon nasa. Ya ce" Na je jibia ban fad'a miki ba, duk suna gaishe ki, za kiyi 'bakuwa cikin satin Sadiya za ta zo ku gaisa." Shiru nayi masa. ya sake rintse hannuna dake cikin nasa, kafin ya ce." Ina ganin dai har yanzu wahalata ba ta 'kare ba, zan cigaba da addu'a tare da fara dubawa daga cikin masu rubibi na." Kallonsa nayi tare da jin fad'uwar gaba, duk da cikin zaurance yayi maganar na fahimci abinda yake nufi, duk sai na ji rashin dadin furucinsa, amma ban nuna a fuskata ba, nayi saurin d'auke kaina. Ya mi'ke tsaye tare da zuba hannuwansa cikin aljihu, ya ce" Na tafi ko na zauna na taya ki kwana?" Da sauri na ce" Ka je kawai." Yayi tsayiwar minti biyu kafin ya kama hanyar fita, na bishi da kallo! zuciyata na wani irin tunani akan kalamansa. Washe gari na tashi sukuku! babu kuzari ko kad'an a jikina, dalilin mafarkin da nayi, haka dai na gudanar da komai cikin rashin nutsuwa! na gama uzurirrika na sannan na zauna karya kummalo kana na sa hijabi a jikina, kamar dai ko da yaushe na nufi cikin gidan. Lokacin dana shiga falon shiru babu kowa, jikina a sanyaye na sake wata sallamar a karo na uku, babu wanda ya amsa, sai jikina ya 'kara mutuwa! cikin zuciyata nake addu'ar cewa; Allah yasa lafiya. Motsi na ji can saman bene in da ya kasance turakar mai-gidan, da sauri na d'aga kaina ina kallon gurin, Hajiya ce take saukowa daga benan idanuwanta jawur! da alama kuka tayi. gabana ya yanke ya fad'i! cikin rawar baki na gaishe ta amsa a sanyaye kafin ta ce" Ki hau sama mai-gidan naki bashi da lafiya jiya da daddare ciwonsa ya tashi ba mu rintsa ba" 'Kafafuna suka shiga rawa! na kasa gaba na kasa baya kawai na zuba mata ido, k'walla duk ta cika kwarmin idona. Ta ce" Kiyi wa Allah da Annabi ki kwantar da hankalinki a gidan nan, ki bawa mijinki kulawa, wallahi ba mu da mummunan nufi! a kanki, bana raba d'aya biyu 'bacin ran ki ne, ya haddasa ciwonsa ya tashi. Da sauri na ce" Wallahi ba haka bane Hajiya, ni kuma me nayi masa da har ciwonsa zai tashi a kaina, kada fa ki manta manya irinsu, dole ba zaki raba su da cututtuka ba, bayan haka kuma abubuwa sunyi masa yawa, na harkokin yau, da gobe, amma kada ki ala'kanta ciwonsa da damuwata." Murmushi takaici tayi kafin ta ce." Duk abubuwan dake faruwa a tsakaninku ina da labari, domin Saddiku baya b'oye min komai, ki sani cewa; a gurinki ne kad'ai muke sanya rai za mu samu nutsuwa, gashi ke kuma kina yi mana wani irin kallo na rashin yarda, wannan ce babbar damuwarsa, gashi ya sanya ki a ransa sosai, ki duba irin 'kaunar da yake miki don Allah ki zauna dashi." Duk yanda na so dana daure abun ya gagara, hawayen da nake 'boyewa suka su'bce! na ce" Hajia wallahi bani da laifi zuciyata ce, amma insha Allahu zanyi 'ko'karin ganin na kawar da komai na zauna tare da ku kamar yanda kuke bu'kata." Ta saki fuskarta tare da fad'in"

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});