Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

to a rabu kawai domin ya gaji da sasanci." Hajiya ranta ya 'baci sosai! a take gurin ta umarce ni dana sake ta, ban jira komai ba na furta cewa na sake ta, na kuma rubuta a rubuce, na bashi sheda! bai damu ba, ya kar'ba tare da buge rigarsa ya ta tashi ya tafi ya bar mu a zaune a gurin cikin tsananin mamaki. A tsakankanin lokacin sai da na kwanta a asibiti domin tsananin ciwon kai da ya addabe ni, jina ne ya hau sosai! sai da likitoci suka rufu a kaina da kuma taimakon Allah na samu lafiya, na dawo gida da tarin magunguna tare da kokarin cire damuwa daga cikin raina, kamar yanda likitana ya bu'kata. Wata uku da rasuwar Mamana wani abokina da mu kayi karatu tare dashi a kano, ya kira ni a waya ce maza na zo ya samar min aiki a wani kamfani, amma nazo da takarduna. Banyi 'kasa a gwiwa ba, na shedawa Hajiya halin da ake ciki, tayi min addu'a sosai kafin na kama hanya na tafi. Faruk ya dafa kafad'a ta da fadin Abokina insha Allah wahalarmu ta 'kare domin "Babban kamfanin sarrafa shinkafa ne dake unguwar harad'a suke neman injiniyoyi irinmu, wannan dalilin yasa na kira ka nace maza kazo ko Allah zai sa a dace, domin ni har na fara zuwa aiki cikin satin da ya gabata" Na ce" Na gode sosai Faruk Allah ya 'kara zumunci" ya ce."Babu komai abokina duk yiwa kai ne. To shi dama lamarin ubangiji ne yana faruwa ne a lokacin da ba kayi tsammani ba, kuma wani lokacin baka samun farin ciki kai tsaye sai an jarabce ka. Kasancewar takarduna sunyi kyau sosai! yasa aka daukeni aiki, akan matsayi mai girma! da albashi mai tsoka, kuma da yake shugaban company yana da tarihin rayuwata, wallahi gida ya dauka ya bani tare da abun hawa mota sabuwa mai kyau da 'kwari! Nayi masa addua sosai da sosai! kuma na d'auki alkawarin yin aiki cikin gaskiya da amana. Wannan shine mafarin dawowata garin Kano da zama, tare da Hajiya na tare a sabon gidana domin tun bayan rasuwar mahaifiyata take tausaya min, wannan dalilin yasa ta ce " Duk inda nake tana gurin" Baba Auta ya dinga kishi! ya kuma kasa 'boye hassadarsa akan abun alherin dana samu. 'Bangaran Baba Audu kuwa addua yayi min sosai, wannan yasa na dauki kudi masu yawa na bashi. Sadiya ma har gidanta na je na kwantar mata da hankali, na ce duk abinda take bukata ta kira ni, a waya insha Allah zan share mata hawaye! cikin damuwa muka rabu da juna. *** Bayan shekara biyu da fara aiki na, rayuwa ta sauya min sosai! hankalina ya kwanta domin bani da wata matsala gagarima, kullum cikin nasara nake fita aiki na kuma dawo cikin fatahi! Rana tsaka Fatima ta kira ni a waya, nayi mamaki sosai! na d'aga wayar muka gaisa, na ce "Ina fatan lafiya? Sai cewa tayi " Kayi hakuri da abinda ya faru" Na ce"Shine dalilin kiran?" Ta ce"A'a" na ce" To ina sauraranki" Ta ce" Na samu labarin abun alherin da ya sameka Allah ya sanya alheri ya kara d'aukaka" Na amsa da "ameen ya Allah" Ta ce"Ka bani address din gidanka zan zo maka da wani albishir wanda zai sanya ka farin ciki." Tsaki na ja da fadin" Baki da hankali har yanzu Fatima" sai kawai na kashe waya ta na rabu da ita, tayi ta kira ban daga ba har ta gaji ta hakura Ina tsammanin number wayata ta bibiya har ta samu gidana.karfe takwas na dare sai ganinta mu kayi tare da wata 'karamar yarinya da bata fi shekara daya da rabi ba. Duka muka zuba mata ido da kallon mamaki a fuskokinmu, kawai sai ta zube kasan kafet tana kuka! tare da rungume yarinyar a jikinta! Hajiya ta je ta kama yarinyar tana duddubata, sai ta kalleni bakinta na rawa, nima yarinyar kawai na zubawa ido ganin fuskarta irin tawa sak! sai dai bata da haske sosai! gabana ya dinga fad'uwa ina kiran sunan Allah a zuciyata cikin raina naji cewa wannan yarinyar 'yata ce domin kama take da Sadiya 'kanwata. Hajiya ta ce"Fatima wannan kukan da ki ke bashi da wani amfani, kiyi mana bayanin matsayin wannan yarinyar." Ta share hawaye murya a dashe ta ce" 'Yarsa ce" gabad'aya muka zuba mata ido. Ta cigaba da cewa" Bayan naje likita yayi min allurar zubar da ciki, ashe tagwaye ne (twins) kuma d'aya ne ya fita. shima likitan be gane ba, saboda Allah ya 'boye al'amarinsa, sai bayan na je saudia domin fara gudanar da harkokina, kawai ciki ya bayyana, koda na je asibiti domin a zubar, likitan ya tabbatar min da cewa ba zai fita ba, domin kuwa ya riga ya girma, idan kuma na tsananta to zan iya rasa rayuwata, wannan dalilin yasa na hak'ura har na haifeta, amma na shiga damuwa sosai, saboda ina fargaba kada na kawo maka yarinyar kace ba kai ne ubanta ba, sai dai nayi farin ciki sosai da Allah yasa yarinyar tayi kama da kai, don Allah Hajiya ku yafe min." Hajiya ta dinga kuka tana fadin" Fatima kinga ikon Allah ko? yanzu kin tabbatar da cewa, ba a yiwa Allah wayo tunda ya saukar da ishara a kanki, ya kamata kiyi hankali kuma" Ta ce"Wallahi Hajiya nayi nadama sosai, na san kuma abinda na aikata ba dai-dai bane don Allah ki bashi hakuri ya mayar dani d'akina" Na kalleta zuciyata cike da b'akin ciki abinda ta aikata Na ce"Har abada aure ya haramta a tsakaninmu, idan kin manta to bari na tuna miki, saki d'aya sau uku nayi miki, ba kuma a lokaci guda ba, ballanatana ki kawo min wani k'auli da ba'adi! saki uku ya halarta a kanki, ni dake har abada mun gama zaman aure, wannan yarinya kuma na 'karba Allah yayi mata albarka" Sosai take kuka tana bani hakuri wai idan aka tambayi malamai za su iya gyara lamarin, kallon mahaukaciya kawai nake mata, ina ji Hajiya na tambayarta sunan yarinyar ta ce" Sunan mahaifiyarsa nasa mata wato Aisha, amma sai nake kiranta da Shukura" Ta ce"Aikuwa kin kyauta da ki ka sanya mata sunan Aisha, Allah yasa ta gaji halinta. Tashi nayi na basu guri domin zamana a gurin ina kallon fuskarta yana tuna min da munanan abubuwan da suka faru a baya. Wannan shine mafarin dawowar Shukura hannuna, domin hana ta tafiya nayi da ita, Hajiya ta cigaba da rainonta, ita kuma tunda ta tabbatar da cewa ba zan mayar da ita ba, sai ta fara biye-biyen malamai, daga 'karshe dai ta je tayi auran kisan wuta wanda ko wata uku ba tayi ba ta fito, ta zo ta matsanta min cewa lallai sai na mayar da ita gidana, sai da nayi mata jan ido sosai! ta saurara min, na nuna mata cewa ko babu mata a duniya sai ita wallahi ba zan 'kara zaman aure da ita ba. "Wannan shine tarihin rayuwata da Fatima matata ta farko, kuma Uwar Shukura, kasancewar asubah ta gabato zan tsaya miki a nan kafin na cigaba da baki labarin abinda ya wuce.. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 78&79 Hannunsa ri'ke da fulas mai d'an girma ya

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});