Chapter 15
Chapter 15
ka auri 'yar uwata ba tare da ka 'kyamace ta ba, a wannan zamanin da kowane uba yake kokarin samawa 'ya'yansa uwa ta gari, sannan ba kowa ne zai yarda ya auri mace irin Zinaru ba, ai ni ka gama yi min komai, saboda haka kyauta nayi maka, kuma babu mai canza ta, ina bukatar ka tsaya da k'afafunka saboda nauyin iyali, tunda akwai yaran da su kayi iya aiki ta dalilinka, to za su cigaba da zama a 'kar'kashina, amma kai na 'yantaka insha Allahu. Gabadaya sai jikina yayi sanyi da kalamansa, hannu biyu nasa na 'karbi takardun ina godiya. Ya ce" Zaka cigaba da gudanar da komai na kamfanin, domin ya riga ya bar hannuna, kuma na tara duk ma'aikatan dake karkashin kamfanin na sheda mu su komai, saboda haka kanka tsaye, zaka cigaba da gabatar da komai." Na ce" Na gode sosai Alhaji Ubangiji Allah ya 'kara suttura duniya da lahira, Allah ya amfani zuria" ya amsa da "amen ya Allah tare da mi'ko min hannu mu kayi sallama. Abota ta da Alhaji Faruk babu ganin 'kyashi, ya taya ni murna sosai, kuma ya taimaka min ta hanyoyi da dama, har kawowa yanzu muna tare muna gudanar da harkokinmu. Hajiya tayi farin cikin alherin da ya same ni tare da duk wani mai k'aunata, amma a zahiri ina ganin masu yi min hassada! sai dai tsakani na dasu addu'a ce. Zama na da Zinaru da farkon fari, yayi dad'i sosai, don har na dinga k'ok'arin sanyata cikin zuciyata domin a lokacin ina ganin kamar tayi hankali ta nutsu ta shiryu kamar yanda muke bu'kata, don tun da na fahimci cewa; tana cikin jerin jarababbun mata nake kokarin ganin na kawar mata da sha'awarta a duk lokacin da ta bukaci hakan daga gare ni, sai dai ashe duka aikin banza nake, domin duk kokarin da nake akanta fita take yi tabi abokan shashancinta da aurena a kanta. Hajiya ce ta tare ni da maganar ranar litinin da sassafe na fito da shirin fita ta ce" Saddiku ina son magana da kai." Yanayin fuskarta kawai na kalla na fahimci cewa maganar da za tayi tana da muhimmanci, duk da sauri nake a lokacin, sai na nemi guri na zauna tare da fadin" To Hajiya ina sauraranki. Ta ce" Duk dai shiga tsakanin ma'aurata babu kyau, amma ni gaskiya abinda ake a gidan nan, ya fara damuna. Na ce" Hajiya wani abu yana faruwa ne?" Shuru tayi tana girgiza kai kafin ta ce" Matarka bata da gaskiya Saddiku, domin tana aikata abubuwa marasa kyau! Gabana ya fadi jin abinda tace, da saurin na ce" Me take aikatawa?" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Kullum bata zama a gida, ka na fita take ficewa, kuma bata dawowa sai dare, sannan duk san da take gida wani mutum kullum sai ya zo gurinta su shiga daki, na ta'ba tambayarta shin wanane shi? sai tace ai d'an uwanta ne, ban yarda ba domin kwata-kwata basa kama da juna, wannan dalilin yasa nake zarginta." [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 77&78 Saukar ajiyar zuciyarta yake ji tare da sheshshekar kukanta, wanda yake masa tsananin zafi a cikin ransa, shima kukan zucci yake, sakamakon tuna abunda ya wuce na daga rayuwarsa, hannu yasa ya dinga goge mata hawaye yana rarrashinta da kalamai masu sanyi, har ya samu tayi shiru ta daina kukan, ya matse ta tsam! a kirjinsa yana jijjigata kamar 'yar goye. Kiran sallar asubahi ne ya raba tsakaninsu, a hankali ya cire ta daga jikinsa ya tashi ya shiga toilet domin d'aura alwala. Sai da yayi wanka tukkuna sannan ya d'aura alwala a gurguje ya fito daga band'akin, nan ya sameta a zaune gefen gado. kallon juna sukayi, yayi mata murmushi na mussaman kafin ya bud'e k'ofa ya fita, sai ta bishi da kallo tana mamakin al'amarin, gabad'aya jikinta ne ya mutu sakamakon jin labarinsa, ta rasa wane tunani za tayi domin gani take kamar ita d'in ba ta dace dashi ba, duba da matsayi da mu'kamin sa, ya kere mata nesa ba kusa ba, ya za'ayi ta saki jiki dashi ta kwantar da hankali har tayi rayuwar aure dashi. *** Tunanin da na jima a cikinsa shine rayuwar aure da talaka dai-dai da ni, don wallahi ban ta'ba sanyawa raina auran mai kudi ba, duba da lalura ta, bayan haka kuma bani da wani kyau na kuzo a gani, sai kuma gani a matsayin matar babban mutum! wanda jama'a suke alfahari dashi, wannan kad'ai ya isa na godewa Allah a bisa ni'imar da yayi min. to amma a raina nake jin kamar auran namu akwai matsala ta kowane 'bangare. Wanka nayi na shirya jikina cikin riga da siket na atamfa, mai kawai na shafa a jikina na gyara gashin kaina, ban d'aura dankwalin ba, sai kawai na yafa a kaina na fito falo na zauna, tunani yayi min katutu! domin kwata-kwata na kasa shiga kicin ballantana nayi tunanin abinda zan ci, da damuwa gami da fargaba sun taru sun cushe min ciki bana sha'awar komai . Haka ya shigo ya same ni cikin wannan halin. kallo d'aya nayi masa nayi saurin kawar da kaina, yayi bala'in kyau cikin 'kananun kayan da yake sanye a jikinsa, mutum ne shi mai wani irin kwarjini da haiba wanda da yawa mutane basa iya had'a ido dashi, sosai k:ananun kayan su kayi masa kyau, ya dawo matashin saurayi, farin gilashin da yake tu'ammali dashi a koda yaushe, yana 'kara masa kyau mutu'ka! Kusa dani ya zauna jikinmu har yana had'uwa 'kamshin turaransa duk ya dabaibaye gurin. Gefe na d'an matsa ina wasa da yatsun hannuna. Ya kama hannun da fad'in." Yaushe za a yi min lalle ('kunshi) irin na amare ina bukata" yana maganar ne lokacin da ya had'a yatsunmu guri daya. Jikina ya d'an mutu sakamakon jinsa a kusa dani, namijin 'kokari nayi gurin gaishe shi. Ya amsa tare da sa bakinsa daidai kunne na ya ce." Ya gajiyar kuka?" Murmushi nayi na ce" Labarinka ya bani tausayi sosai! amma kayi hakuri jarrabawa kowa da irin tashi, sannan ka godewa Allah da ni'imar da yayi maka." Ya ce" Kullum a cikin godiyar Allah nake, gashi yanzu ya amsa min addu'a ta, ya azurtani da mar'atussaliha" "Nayi mamakin sosai da wannan al'amarin, amma ya akai kake sauya hallitarka? don wallahi ban ta'ba tsammanin kaine kake kasancewa mutum biyu. Dariya yayi ya ce" Zan baki labari anan gaba, ni dai burina ki saki jiki da ni, ki ri'ke ni amana, domin nasha wahala a hannunku, shiyasa nake tsoronku, amma dai ina da tabbacin ke ba zaki wahalar dani ba ko?" Yanda ya fad'i maganar ne ya bani dariya da tausayi. Na ce" Auranka nawa?" "Wannan shine na uku kuma ina rokon Allah yasa nayi dace." Ya fada tare da rintse hannuna da nasa. Shuru kawai nayi ban ce komai ba. "Kinyi shuru ko baki amince dani a matsayin miji ba" Na ce" Ni dai gaskiya sai nayi tunani tukkuna, domin naga kamar kana da dabi'ar auri saki, ita mace tana da rauni me yasa ba za kayi hakuri da hallayar mata ba. "Bangane abinda ki ke nufi ba" yafada da alamun rashin dadi a tare dashi. Na ce" Ni ina tunanin wani abu ne" Hannuna ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28