Chapter 5
Chapter 5
kuwa talaka ne wanda bai ajiye ba, kuma bai bawa kowa ajiya ba, amma dai ko da kowa bai zauna ba, 'yan uwansa sa zauna domin kar'bar gaisuwa, duk da cewa zaman ba dole bane a shari'ar musulunci, amma ai an mayar dashi al'ada, a lokacin zan ji dad'i mutukar da wani a kusa dani, sai ya kasance ni kad'ai nake kar'bar gaisuwa domin babu wanda yake zaune gefe da gefe na, sai dai ina farin ciki sosai idan na tuna cewa mahaifina yayi mutuwar shahada, ya kuma shiga ranar juma'a, bayan kyakykyawar sheda ta mutane. Ranar sadakar uku ni da k'anwata Sadiya muka yi masa saukar al'kurani maigirma, bayan haka kuwa babu wani abu da 'yan uwasa suka yi masa na sadaka, a tsaitsaye suka tafi mussaman Baba Auta don shi ko zama beyi ba yace yana da uzuri, gwara Baba Audu ya d'an zauna na 'yan mintina kafin ya tashi ya tafi. Hakan bai dameni ba, domin ni babban buri na da fata na, ace mahaifina ya dace da rahamar ubangiji. Sosai na tashi hai'kan! da neman kud'i, duk abinda za'ayi da jiki k'arfi ina zuwa na yi mutukar zan samu abinda asiri na zai rufu, ni ne wanki da guga! gyaran takalma, aikin gini, dako cikin kasuwanni, gefe guda kuma ina yin gyaran babura da siyar da fetur a bakin titi, asiri na kuwa ya rufu, domin na d'aukewa mahaifiyata da k'anwata nauyin komai, don ba naso suyi kukan maraici! shiyasa nake fita nema ba dare ba rana. Ganin haka yasa Hajiya dawowa gidan, a cewarta ai suma suna da hakki a kaina, duk neman da nake uwata nake wahaltawa, sai ta dawo gidan ta share d'aki ta zauna, tsirfar yau daban ta gobe daban, gashi ita kuma mamana bata da hayaniya! kuma bata son tashin hankali, shiyasa duk abinda Hajiyan tayi mata sai ta kawar da kanta, amma abin yana damunta mutu'ka, ni ma abin yana yi min ciwo, ranar da na samu zama a gidan, zan shiga har dakinta na zauna domin na nusar da ita cewa abinda take ba daidai bane, sai kawai ta fashe min da kuka ta lauya zancen da cewa; don naga 'kasa ta rufe idon mahaifina shiyasa nake nuna mata cewa mamana tafi ta girma a guri na, ganin haka yasa kawai na rabu da ita sai dai na daina sakar mata fuska, ko wasa take min bana saurararta nake shigewa na tafi harkokina, sai ta rarrafo ta fito tsakar gida ta zauna ta dinga habaici! wanda yake damun zuciyar mamana! bata kaunar tashin hankali da damuwa, haka za suyi ta kuka ita da Sadiya a daki abin na damun ransu. Cikin ikon Allah da wannan buge-buge da nake na samu na sayi fili, sai dai tunda Hajiya ta ji labari, ta dame ni kan lallai sai na fito da matar aure tunda ina samun kudi, nayi kokarin nusar da ita cewa; kudin da nake samu na rufin asiri ne, zanyi aure amma ba yanzu ba. Ta 'ki yarda da maganata, kawai ta kira Baba Auta ta fara sheda masa halin da ake ciki, 'kiri-'kiri na ga hassada a cikin idonsa, jin cewa na sayi fili har na soma gini, ya dinga fad'a mara dalili wai akan me duk abunda zanyi ba zan nemi shawararsa ba, ni dai shuru kawai nayi ina kallonsa. Ya ce." Shikkenan Allah ya sanya alheri, maganar aure kuwa dole mu yi maka ka fito da mata, idan kuma baka da ita to na baka Fatima." Gabana ya fadi! na kalle shi da mamaki a tare da ni na ce." Wace Fatima?" Ya ce"Ta waje na mana ko kana ganin kafi karfin ka aureta ne?" Na ce." Gaskiya bana ra'ayinta Baba auta babu maganar rufa-rufa a tsakaninmu, Fatima 'yarka ce amma kasan bata da kamun kai ko?" Ya ce." Magana zaka fada min a gaban ido na?" Na ce" Ba haka bane na jaddada maka abinda ka sani ne, ni d'in ba mace bane, ballanatana ayi min irin auran da bana ra'ayi, a kyale ni da kaina zan duba matar da ta cancata. Sai kawai ta fashe! da kuka da fadin" Saddiku wannan sharrin na mahaifiyarka ne, domin ita take zama ta kitsa maka komai, amma ina laifin wanda yayi maka kyauta, Fatima dai 'yar uwarka ce duk lalacewarta ba zaka sanja ta ba. Ya ce." Ki rabu dashi Hajiya tunda shi bashi da mutunci, a gaban idona yake cin fuskata, to shikkenan tunda kace baka sonta sai ka fito da wacce ka keso." yana gama maganarsa ya tashi fuuuu! ya fita. Nima tashi nayi na bar gurin raina a 'bace! gaskiya ba zan lamunci wannan kama karyan ba. domin dai yarinyar kowa ya san halinta, sam bata da nutsuwa da tarbiya ga shegen kula maza da sauraran abubuwan da basu dace ba, a wannan zamanin kowane uba yana so ya za'bawa 'ya'yansa uwa ta gari, to akan me yana ganin kashi da rana ya taka, ba zai yuwu ba. Ko da na shedawa mamana halin da ake ciki, sai ta ce tunda abun ya riga ya zama haka to nayi gaggawar fito da matar da nake so na aura, domin a ganinta hakan zai sanya su janye maganar Fatima. Na shiga tsaka mai wuya a lokacin, domin kuwa tunda na girma na kai munzali na samartaka ban ta'ba kula wata budurwa ba, ba don bani da bukata ba, a'a asali ma ni mutum ne mai yawan sha'awa, shiyasa sa'i da lokaci nake azimi domin tseratar da kaina. Ina son aure sosai, to amma ina cizawa! domin na riga na san aura a yanzu dole sai ka shirya, nauyi biyu ne zai hau kaina dana iyalina da na mahaifiyata da 'yar uwata. Amma tilas tasa na yankewa kaina shawara domin gujewa auran Fatima wacce babu ita a cikin tsarin rayuwata Na je na samu mahaifiyata da maganar Na'ima 'yar 'kaninta ce Baba Salihu, yarinyar tana da tarbiya sosai da kunya, wannan shine abinda ya ja ra'ayi na akanta har na ji ina sha'awar auranta. Tayi shuru tana nazarin al'amarin kafin ta ce." *D'an gaske* da yake sunan da take kira na dashi kenan, sakamakon sunan mahaifinta ne, ta cigaba da cewa" ina gudun abinda zai biyo bayan al'amarin, domin bana son tashin hankali, kuma ban mance da wasiyyar mahaifinka ba, kan cewa lallai na kula da mahaifiyarsa ka da tayi kuka damu, muyi kokarin ganin mun rabu da ita lafiya, wannan dalilin yasa duk abinda Hajiya take min a gidan nan, bana d'aga kai na kalleta, domin zama na amana da mutunta juna nayi da mijina, duk da mahaifiyata bata yare, ya zama dole na girmama tasa, saboda haka ban hana ka nemi auran Na'ima ba, amma ka je ka shedawa 'yan uwan mahaifinka domin mu ji hukuncin da za su yanke. Hajiya tayi tsalle ta dire tace bata amince ba, wato naje na had'a baki da uwata ta dauki 'yar kaninta ta bani, na guji 'yar uwata Fatima, to bada yawunsu ba, muddun nace dole sai na auri Na'ima sai dai na sanja iyaye, gabad'aya suka had'e bakinsu, Kawu Audu dashi Baba Auta din, babu wanda ya fahimce ni. Mamana ta umarce ni cewa na janye maganar auran Na'ima na amince da auran Fatima domin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28