Chapter 1
Chapter 1
61&62 Wani irin kallo take masa. bakinta na rawa magana ta take so tayi amma tsabar tashin hankali! da mamakin al'amarin ya sa bakinta yin nauyi, ta gagara furta komai sai kallonshi take tana ayyana abubuwa da yawa a kansa, gaskiyar magana yau ne ta tabbatar da cewa yana da matsalar kwakwalwa, kamar yanda jama'a suke zarginsa, idan ba mara hankali da tunani ba waye zai d'auki matar auransa ta sunnah ya mi'ka ga wani 'kato, tabbas basu da hankali! gabadaya har maigidan nasa dukkaninsu suna bukatar ganin likitan k'wak'walwa! ita kam ba zata yarda da wannan yahudancin ba, tana ganin duk abinda zai faru sai da ya faru, ba zata amince da wannan manufar ba. To bayan tafiyarsa sai ta kasance cikin damuwa da tunanin hanyar da zata bi gurin ganin ta warware matsalarta, gaskiyar lamari barin gidan shine samun nutsuwarta, ashe dama wannan matsalar Baba Asabe ke hango mata, gashi kuwa tun ba a je ko'ina ba al'amura sun jagwalgwale. Ita kanta Hajiya Saude kwana biyu ta kasa gane me yake damunta, domin ko ta je gurinta ba ta iya sakin jikinta, suna gaisawa take tafiya domin ba ta yarda ta zauna maigidan ya same ta, gabad'aya ta sanja taku a gidan, da wurwuri take kukkule ko'ina na sashenta, sai ta shige can uwar daki ta kulle kanta, duk a kokarinta na tsaretar da rayuwarta. Sai dai duk yunkurin da za tayi masu tsaron gidan idonsu a kanta, domin zuwa yanzu sun santa a gidan, amma ba su san matsayinta ba. Sai ta sanja shawara da kuma shirya yanda za tayi ta gudu daga gidan. Ranar Juma'a ita ce ranar da gidan ke cika da jama'a maza da mata domin a ranar ne maigidan ke raba kud'i ga mabukata. To tana ganin za tayi basaja ne kawai ta shiga cikin jama'ar a matsayin mai neman taimako. Gidan ya cika sosai da jama'a gabad'aya masu tsaron gidan suna can suna shirya mutane domin su daidaita layi kafin ya fito, wannan ya bata damar shiga jerin matan da suke ja dogon layin da ba zai 'kirgu ba. Sule ya fito ya sanar musu da cewa; saboda yamma tayi kuma dab ake da a kira sallar magariba su yi hakuri sai anyi sallah tukkuna maigidan zai fito. Babu wanda ya nuna damuwarsa da hakan, kowa dai burinsa ya samu abinda zai sa a aljihunsa. Fitowarsa ta hango sai tayi saurin sunkuyar da kanta. tana addua Allah yasa kada ya gane ta. Jama'a su ka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa, ya amsa daidai gwargwado kafin ya wuce zuwa massalacinsa dake jikin gidan, wasu suka bi bayansa wasu kuma suka gabatar da sallarsu a cikin gidan mussaman mata tunda akwai manya manyan rumfuna dake shimfide da kafet da tabarmi. Kan wata kujera ya zaune a nutse ya fara gudanar da abinda ya tarasu a gurin. Duk wanda aka bawa zai yi godiya ya kama hanya ya fita cikin farin ciki da annashuwa. Layi yana ta tafiya har aka zo kanta, kallo daya yayi mata ya gane ko wacece a gabansa, mamaki sosai ya kamashi, sai ya tsira mata idonsa kamar koda yaushe, ita kuma sai jikinta ta daburce! da sauri ta dauke kanta tana sake gyara zaman hijab din da ya rufe mata fuska sai 'kwayar idonta kawai ake gani. Sannu take mik'a masa tana risinawa wai ya bata kudin. bai yi 'kasa a gwiwa ba ya bata domin ganin abinda take shirin aikatawa domin ya tabbatar da zarginsa. aikuwa tana kar'ba hanyar fita ta nufa da saurin gaske. Da azama ya juya in da escort d'inshi biyu ke tsaye a kansa. Duka suka sunkuyo domin jin umarninsa. Da sauri wanda yake hannun damarsa ya nufi bakin gate wanda a lokacin har tasa kafarta a waje za ta fita, aka dakatar da ita. Gabanta ya buga da karfin gaske! shikkenan ta faru ta kare. Jami'in tsaron ya nuna mata bindiga kafin ya bata umarnin komawa ciki da hannunsa. Da sauri ta bi umarninsa ta koma ciki domin ba ta so hankalin jama'a ya dawo kansu, dama yanayin kallon yayi mata tasha jinin jikinta cewa ya sheda ta. Ganin masu tsaro gidan da masu gadin hankalin su ya karkata wani guri da sauri ta kama hanyar sashenta tana ta addua a cikinta. Rurrufe ko'ina tayi ta zube kan kujera! sai kawai kuka ya 'kwace mata, wannan masifa dame ta yi kama? shikkenan haka za tayi ta zama cikin fargaba da damuwa, wai shin ya za tayi ne da rayuwarta. Abokiyar shawararta wato zuciyarta ita ce ta tunasar da ita cewa dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma Allah yana nan saboda haka ta nemi sauki a gurinsa. Don haka sai ta ji k'warin gwiwa! lallai wannan shawarar ita ce abin yi. Alwala tayi ta gabatar da nafila raka'a biyu sannan ta daga hannunta tana zubar da hawaye take rokon Allah ya kawo mata sassauci a rayuwarta, Allah ya zaba mata abinda ya fi alheri. Da safe ta tashi sakayau! lallai ta yarda al'kur'ani yana maganin kowace irin masifa, kuma dukkan wanda ya shiga damuwa ya mika lamuransa ga Allah zai isar masa. Kwana d'aya biyu babu wani lamari na tashin hankali da ya biyo baya duk da cewa sun had'u amma bai yi mata komai ba ballantana ya tuhume ta akan matakin guduwa da ta d'auka! Ranar litinin da sassafe Hajiya ta je asibiti domin a duba lafiyarta, tare da Shukura su ka tafi domin daga Asibitin za su wuce wata unguwa. Da k'warin gwiwarta ta shiga da sallama a bakinta. Sai dai ganinsa a hakimce! a kan kujera ya tsoratar da ita, da sauri ta juya da nufin fita. Ya dakatar da ita babu yabo babu fallasa ya ce." Ya zaki juya kuma ko ba gaida Hajiya ki ka zo ba?" Kanta kawai ta iya daga masa alamun "Eh hakane" Ya bata umarnin zama da fadin." Zo ki zauna yanzu za ta fito.'' kallonsa tayi amma bata yarda da maganarsa ba domin a irin wannan lokacin take samun hajiyan a zaune a falo a duk sanda ta zo gaishe ta. Ya ce." Matsalata dake gardama zo ki zauna na ce." Yafada yana nuna mata saman kujera. A jiyar zuciya ta sauke a tsarge ta je ta zauna kasan k'afafunsa domin babu yanda za a yi ta zauna kan kujera bayan yana kai. K'amshinsa ne duk ya cika mata hanci! jikinta yayi la'asar, a duk sanda za ta ji 'kamshin jikinsa sai ta rasa gane abinda yake damunta, ita dai 'kamshin yana mata dad'i Tsaye ya mi'ke tayi saurin kallonsa sai ta ga ya nufi hanyar fita, ta sauke sanyayyar azuciyar zuciya domin duk a zaton ta fita zai yi ga mamakinta kawai sai ta ga yana kulle kofar da key (mukulli) "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! wannan kalmar ta kira kafin ta tashi tsaye suka hada ido a lokacin da ya juyo. ta tsorata da ganin yanayin fuskarsa don babu fara'a ko kad'an. Daf da ita ya tsaya saura kadan jikinsu ya had'u. Ta ja da baya, ya sake matsowa ta sake ja da baya! Still ya sake kusantarta! sai ta daga hannu da niyyar tayi masa gargad'i! ya bar abinda yake, ya r'ike hannun ya had'a da nasa yatsun suka had'u guri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28