Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai Allah ya saka min sharrin da kake min ni 'ban ta'ba kwanciya da wani namiji ba sai kai, amma kullum cikin zargi na kake. Na ce" 'Karya ki ke yawon ta zubar ki ke zuwa bayan na fita dame na gaza miki? na d'auka ko bana son kwanciya dake sai kinyi min dole kuma haka nake 'kure miki gudu! amma shine zaki je ki kwaso mana cuta" Ta tsuguna 'kasan 'kafafuna tana kuka da fadin "Ni dai don Allah ka daina jifa na da irin wannan munanan kalaman, wallahi bana zina, shima lesbian din tunda nayi aure ban sake yi ba, kuma zan gaya maka gaskiyar gurin da nake zuwa. Na zuba mata ido ina kallonta ta ce" Gidan Jamila nake zuwa muna sana'ar dillanci, shine nake samun 'yan kud'i domin nima ina sha'awar na tsaya da k'afafuna, tunda dai kai baka da wata gwagwgwa'bar sana'a." Raina ya 'baci mutu'ka na ce"Yanzu Fatima da 'kananun shekarunki ki ke wannan sana'ar? masifa kike so ki janyo mana ko me?" girgiza kanta tayi. Na ce" Kin ce bani da gwagwagwa'bar sana'a! shin na ta'ba barin ki, da yunwa?" kai ta girgiza. na cigaba da cewa; na gaza miki ta fannin ci dasha da suttura da lafiya da gurin kwanciya? " Ta ce" A'a." na ce" To mai zai sanya ki zubar min da mutunci?" Hakuri ta dinga bani, Na ce" Wannan ya zama na farko da 'karshe kada ki sake fita bada izini na ba, sannan kuma na rabaki da Jamila har abada babu ke babu ita, zan je har gidanta na sameta da wannan maganar." Kamar gaske ta ce" Shikkenan ba zan sake ba nayi alkawari, kuma na rabu da jamila har abada'' jin haka yasa hankalina ya dan kwanta na sassauta mata. To ashe tsugune! bata 'kare ba, domin dai Fatima ha'inata take ta kowanni, idan na siyo kayan abinci na wata guda sai ta kwashe rabi ta siyar, abin ya dinga bani mamaki! ganin cewa mu biyu ne kacal! amma 'karamin buhun shinkafa baya wata d'aya haka nan kwalin taliya ma, mangyada da manja jarka-jarka nake saya da ledar maggi, amma basa kwana goma zuwa sati biyu sun 'kare, sosai na sanya mata ido, anan na gane cewa kwashewa take ta siyarwa da wani mai kanti, dake bayan layinmu, duk na samu wannan hujjojin ne daga gurin al'majirin da yake mana aike-aike! tunda na gane haka sai na daina siyan komai ina aje wa, sai dai kullum idan zan fita zan bata dubu daya ko dari bakwai, tayi awo da cefane! Sai ta shiga damuwa! kullum cikin 'korafi! cewa; kudin da nake bata basa isa komai yayi tsada! shareta kawai nake na kan ce ta cigaba da yi min addu'a idan na samu kudi zan cigaba da siyo mata komai da yawa. Wata da'bi'a da ta tsira kuma shine, duk sanda na dawo gida na cire rigata na shiga wanka sai tayi min binkice ta dauki dubu daya ko biyu a cikin abinda na samu, da yake bana lissafi a can sai na dawo gida shiyasa ban gane ba, sai watarana dana shiga wanka sai naga babu sabulu, na fito kawai sai naga tana zazzage min kudin cikin aljihu tana lissafawa, nan naga ta dauki dubu uku ta daure a bakin zaninta, tashi tayi da sauri zata mayar da rigar sai kawai muka had'a ido! duk sai ta gigice! ta fara wuri-wuri! na daga mata hannu da fadin" Bani kudi na" babu kunya ba tsoron Allah ta kwanto kudin ta bani. Na ce" Tun yaushe ki ke min sata?" "Wallahi yau ne kawai" Tafada muryarta na rawa" Na juya na rufe dakin da sakata na ce" Zaki fada min gaskiya ko sai naci ubanki" Ganin ina kokarin dukanta yasa ta fara kuka da fadin" Ka tsaya don Allah kada ka doke ni zan fad'a maka wallahi wannan shine karo na bakwai ." "Iya adadin nawa ki ka dauka?" na fad'a zuciyata a 'kuntacce! "Dubu goma sha shida kenan" Tafad'a tana yin nesa dani. Na ce" Me za kiyi da kudin?" "Ankon bikin Abulle zan saya dubu talatin da biyar ne, na san idan na fad'a maka ba iya saya min za kayi ba." Wani kuttun bakin ciki ya tokare min wuya.Na ce" Ya akayi ki ka yanke min hukunci bayan baki fad'a min kin ji ta bakina ba" "Dubu talatin fa duka-duka jarin naka guda nawa yake wallahi ba zaka iya say......." Wani bahagon mari na kwada mata, jikina na rawa na ce" Don ubanki da kudin wa za ki saya yanzu?" tayi shuru tana kallona hannunta dafe a kumatu. Na cigaba da cewa; ina jin yanzu har kin had'a dubu goma sha biyar da kudina wanda duk sanda ki ka tashi magana zaki ce bani da jari, ko kuma gwagwgwabar sana'a wannan din kudin ubanki?" Kuka take sosai! na ce" Fito min da kud'ina ko na lahira ya fi ki jin dadi yanzu. Tana kuka ta ce" Ai na riga na bayar dasu na ce zan ciko sauran, don Allah kayi hakuri ka saya min" Na ce"Ai baki biyo hanya ba, wallahi da kin fad'a min cikin mutunci ni mai iya saya miki ne, amma tunda ta wannan hanyar ki ka biyo shikkenan, gobe da wurwuri ki je ki kar'bo min kud'ina idan ba haka ba, ni dake ke ne" Zubewa tayi a kasan dakin tana kuka, ni kuma nasa rigata na fita domin sayo sabulun wanka. Sai da ta kar'bo min kud'ina sannan na 'kyaleta ta sha'ki iska. Kwana biyar da faruwar al'amarin, na dawo gida naga babu kujeru a falo. na tambayeta suna ina? kai tsaye tace ta sayar dasu, domin ta sharewa kanta hawaye! tunda dai nata ne. na ce to shikkenan, mutukar kuwa ta fita zuwa gurin bikin nan, a bakin auranta. Ko a jikinta, biki na zuwa ta dinga zurga-zurga duk ina kallonta ban ce mata komai ba, sai da suka gama bikin tukkuna, da safe ta kwaso wanki za tayi, da zan fita na bata takarda saki, nace" wannan ita ce shedar sakin da nayi mata idan ta manta to na tuna cewa muddun ta fita da niyyar zuwa gidan biki 'kawarta a bakin auranta. Kuka sosai ta dinga yi tana bani hakuri, ban ko saurareta ba nasa 'kafata na fita daga gidan. Wannan abun dana aikata sai da nayi nadama! domin shine silar kwanciyar mamana 'bacin rai da tashin hankali ya janyo mata mutuwar 'barin jiki! kuka sosai nayi da idanuwana ganin mahaifiyata magashiyan rai a hannun Allah, nayi tur! da auran Fatima da kuma 'bakar zuciyata, duk da nasan duk abinda nake yi akan gaskiyata nake domin na kare darajar aure na. Har Mamana ta gama zama a asibiti babu wanda ya taka kafa ya je domin dubata, gabad'aya 'yan uwan mahaifina da ita kanta Hajiyar sun dauki laifi sun d'ora mata cewa; da umarninta nake aikata komai, saboda haka babu su babu ita. Nayi nadama sosai! kuma na zubar da hawayena ganin yanda 'bacin rai da damuwa suka haifarwa da Ummana matsala, 'bari guda na jikinta ya daina aiki, sai an taimaka mata! haka Sadiya take kula da ita, ni kuma ina yi da jikina da aljihuna, kuma nayi mata alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba, sosai

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});